Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 12/1 p. 32
  • Muhimmin Lokaci don Rayuwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Muhimmin Lokaci don Rayuwa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 12/1 p. 32

Muhimmin Lokaci don Rayuwa

IDAN kana fuskantar lokaci mai wuya ƙwarai, kana sha’awar rayuwarka ta dā? Idan haka ne ka yi la’akari da kalmomin Sarki mai hikima Sulemanu: “Kada ka tambaya, Don me kwanakin dā sun fi na yanzu kyau? Gama ba da hikima ka ke binciken wannan ba.”—Mai-Wa’azi 7:10.

Me ya sa Sulemanu ya ba da wannan shawarar? Domin ya sani cewa idan muka bincika da gaske abin da ya faru dā yana da muhimmanci wajen jure wa yanayi mai wuya na yanzu. Waɗanda suke sha’awar “rayuwarsu ta dā” wataƙila sun manta cewa waccan rayuwar tana cike da matsaloli da masifu ba ta kasance yadda ake so ba. Wataƙila wasu abubuwa a dā suna da kyau, amma yawanci ba su da kyau. Kamar yadda Sulemanu ya lura, babu hikima cikin kasancewa da sha’awar abin da ta faru a dā, babu tantama, ba za mu iya mai da hannun agogo baya ba.

Da cikas ne mutum ya dulmaya cikin begen abin da ya shige? Hakika, idan hakan ya sa muka kasa sabawa da yanayinmu na yau ko kuma ya hana mu fahimtar lokaci da muke ciki da kuma bege da za mu iya yi.

Yanzu ne muhimmin lokaci don rayuwa, duk da ƙarin matsaloli na duniya. Me ya sa? Domin mun kusa da cikar nufe-nufen Allah game da duniyarmu da kuma albarkatu na sarautar salama na Mulkinsa. Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari: “Za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙinzuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) A lokacin, da yanayi ya kyawanta ƙwarai, babu dalilin da wani zai yi sha’awar rayuwa ta dā.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba