Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 3/1 p. 19
  • Samun Gaskiya a Inda Ba Za a Yi Tsammani Ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Samun Gaskiya a Inda Ba Za a Yi Tsammani Ba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Makamantan Littattafai
  • An Dauka Cewa Ni Ne Faston
    Labarai
  • Har Yanzu Gaskiya Tana da Muhimmanci Kuwa?
    Karin Batutuwa
  • Ku Ci Gaba da “Bin Gaskiya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Kiristoci Suna Bauta Cikin Ruhu Da Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 3/1 p. 19

Rahoto Daga Masu Shelar Mulki

Samun Gaskiya a Inda Ba Za a Yi Tsammani Ba

NUFIN Allah ne cewa ‘ire-iren mutane su tsira, kuma su kai ga cikakken sanin gaskiya.’ (1 Timothawus 2:3, 4) Domin su cim ma wannan makasudi, Shaidun Jehovah sun buga kuma sun rarraba miliyoyin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai na nazarinsa. A wasu lokatai, waɗannan littattafai sun taimaki masu zuciyar kirki su koyi gaskiya a hanyar da ba a yi tsammani ba. Game da wannan, masu shelar Mulki a Freetown a Saliyo, suka ba da wannan labari na gaba.

Osman shi ne ɗa na biyu cikin ’ya’ya tara na babansa. Domin iyalinsa tana da son addini, kullum yana zuwan bauta tare da babansa. Amma, Osman ya damu ƙwarai da abin da addininsa ke koyarwa game da jahannama. Ya kasa fahimtar yadda Allah mai jinƙai zai gana wa masu mugunta azaba a cikin wuta. Dukan bayani da ake yi wa Osman don ya taimake shi ya fahimci koyarwa game da wutar jahannama bai ƙayatar da shi ba.

Wata rana, da Osman ya kai shekara 20, ya ga wani littafi, shuɗi, shara ta kusan ta rufe shi cikin kwandon shara. Domin yana son karatu, ya ɗauka, ya share, ya lura da jigon—Gaskiya mai bishe zuwa Rai Madauwami.a

‘Wace gaskiya ke nan wannan?’ Osman ya yi kakabi. Da ya cika da son ya sani, Osman ya kai littafin gida ya karance shi nan da nan. Ya yi murna ƙwarai da ya koyi cewa Allah yana da suna—Jehovah! (Zabura 83:18) Osman ya kuma koyi cewa hali na Allah na musamman ƙauna ce, saboda haka tunanin ya gana wa mutane azaba cikin wuta abin ƙyama ne a gare Shi. (Irmiya 32:35; 1 Yohanna 4:8) A ƙarshe, Osman ya karanta cewa ba da daɗewa ba Jehovah zai mai da duniya ta zama aljanna da mutane za su iya rayuwa har abada. (Zabura 37:29; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Hakika gaskiya ce ta ban mamaki daga Allah mai jinƙai, mai ƙauna! Cike da godiya a zuciyarsa, Osman ya gode wa Jehovah da ya yarda masa ya sami gaskiya a inda bai yi tsammanin ta ba.

Bayan ’yan kwanaki, da taimakon wasu abokai, Osman ya sami inda Majami’ar Mulki ta Shaidun Jehovah take kuma ya halarci taronsa na farko. Da ya je wurin, ya ce wani Mashaidi ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Duk da hamayya ƙwarai daga iyalinsa, Osman ya ci gaba da ci gaba a ruhaniya kuma ya yi baftisma. (Matta 10:36) A yau, yana hidimar dattijo a ikilisiya. Abin godiya ne cewa dukan wannan ya faru ne saboda ya sami littafi na Littafi Mai Tsarki cikin kwandon shara!

[Hasiya]

a Shaidun Jehovah ne suka buga a shekara ta 1971.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba