Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 10/1 pp. 3-4
  • Bangaskiya Ta Gaske—Tana Yiwuwa Har Yanzu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bangaskiya Ta Gaske—Tana Yiwuwa Har Yanzu?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Bangaskiya ta Gaske
  • Rashin Bangaskiya
  • Ka Kasance da Tabbaci a Kan Alkawuran da Jehobah Ya Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • “Ka Kara Mana Bangaskiya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Da Gaske Ka Ba Da Gaskiya Ga Bisharar?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Bangaskiya​—Tana Sa Mu Kasance da Karfin Zuciya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 10/1 pp. 3-4

Bangaskiya Ta Gaske—Tana Yiwuwa Har Yanzu?

“Bangaskiya rayayyiya ce, gaba gaɗi ne cikin alherin Allah, tabbaci da mai bi zai iya ba da ransa a kanta ko sau nawa.”—MARTIN LUTHER, 1522.

“Kusan gaba ɗaya, mun zama jam’iyyar mutane ne da bangaskiya ta Kirista ba ya wanzuwa.”—LUDOVIC KENNEDY, 1999.

RA’AYOYI a kan bangaskiya sun bambanta ƙwarai. A dā, bangaskiya ga Allah aba ce ta yau da kullum. A yau, a cikin duniya da take cike da tantama da wahala, bangaskiya ta gaske ga Allah da kuma Littafi Mai Tsarki na ɓacewa da sauri.

Bangaskiya ta Gaske

Ga mutane da yawa, “bangaskiya” kasancewa ce da imani na addini ko kuma bin fasalin wata bauta. Amma, yadda Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da “bangaskiya” tana nufin dogara gabaki ɗaya—duka duka, gaba gaɗi mara jijjiga ga Allah da kuma alkawuransa. Hali ne da ke nuna almajirin Yesu Kristi.

A wani lokaci, Yesu Kristi ya yi magana game da bukatar yin addu’a ban da ‘yin suwu.’ A yin haka, ya yi tambaya game da ko za a sami bangaskiya ta gaske a zamaninmu. Ya yi tambaya: “Sa’anda Ɗan mutum ya zo, za ya sami [wannan] imani bisa duniya?” Me ya sa ya yi irin wannan tambayar?—Luka 18:1, 8, hasiya ta NW.

Rashin Bangaskiya

Abubuwa da yawa sukan sa mutane su yi rashin bangaskiyar da suke da ita. Wasu cikinsu sune wahala da kuma jarabobbin rayuwar yau da kullum. Alal misali, Farfesa Michael Goulder, firist ne a Manchester, Ingila, a lokacin wani haɗarin jirgin sama a shekara ta 1958 a Jamus da ’yan wasan ƙwallon ƙafa na Manchester United suka mutu. A wani wasan telibijin na BBC, mai wasa labarai Joan Bakewell ta bayyana cewa Goulder “bai ji daɗi ba ƙwarai ganin yadda mutane suke baƙin ciki sosai.” Abu ɗaya da wannan ya jawo shi ne ya “yi rashin bangaskiyarsa ga Allah wanda zai iya sa hannu a harkokin mutane.” Goulder ya furta imaninsa cewa “Littafi Mai Tsarki . . . ba maganar Allah ba ne da ba ta kasawa” maimako “maganar mutum ce da take kasawa, ƙila da wasu hurewa a nan da can.”

Wasu lokatai bangaskiya takan yi yaushi. Abin da ya faru ke nan da marubuci kuma mai wasa labarai, Ludovic Kennedy. Ya ce tun yana yaro “tantamarsa da shakka [game da Allah] ya ci gaba kuma rashin imanin[sa] ya ƙaru.” Kamar dai, babu wanda zai iya ba da amsoshi da suka dace ga tambayoyinsa. Mutuwar ubansa cikin teku ta raunana bangaskiyarsa wadda dama raunanniya ce. Addu’o’i ga Allah da muka yi cewa ya “tsare mu daga haɗarin teku da kuma muguntar magabci” ba a amsa su ba, da yake jirgin yaƙi na Jamus a lokacin Yaƙin Duniya na II ya kai farmaki kuma ya halaka jirgin ruwa na fasinja da ubansa yake ciki.—All in the Mind—A Farewell to God.

Irin labaran nan ba sabon abu ba ne. Manzo Bulus ya ce: ‘Ba duka ke da bangaskiya ba.’ (2 Tassalunikawa 3:2) Yaya ka ke ji game da haka? Zai yiwu ne a kasance da bangaskiya ta gaske ga Allah da kuma Kalmarsa a duniyar da ke cike da tantama? Ka bincika abin da talifi na gaba zai faɗa game da wannan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba