Ta Yaya Salamar Kristi Za Ta Yi Mulki A Cikin Zukatanmu?
“Bari salama ta Kristi ta yi mulki a cikin zukatanku; zuwa wannan salama aka yi kiranku cikin jiki ɗaya.”—KOLOSSIYAWA 3:15.
1, 2. A wace hanya ce “salama ta Kristi” take mulki a cikin zuciyar Kirista?
MULKI kalma ce da mutane da yawa suke ƙyama, tun da tana sa a yi tunanin tilastawa ko kuma mallaka. Gargaɗin Bulus ga ’yan’uwa masu bi a Kolosi, “Bari salama ta Kristi ta yi mulki a cikin zukatanku,” zai sa wasu su ji cewa wannan ba azanci ciki. (Kolossiyawa 3:15) Mu ba mutane ba ne da aka ba mu ’yancin mu yi abin da muke so? Me ya sa za mu ƙyale wani abu ko wani ya yi mulki cikin zukatanmu?
2 Bulus ba gaya wa Kolossiyawan yake su yasar da ’yancinsu ba. Kalmar Helenanci da aka fassara “mulki” a Kolossiyawa 3:15 tana da alaƙa da kalmar rafali wanda yake ba da kyauta a wasannin gasa na wancan zamanin. Masu wasa suna da ɗan ’yanci cikin dokokin wasan, amma a ƙarshe, rafalin ne zai nuna wanda ya bi dokokin kuma saboda haka ya yi nasara a gasar. Hakanan, muna da ’yanci mu tsai da shawarwari da yawa a rayuwa, amma sa’ad da muke haka, salama ta Kristi ta kasance ko da yaushe “rafali”—ko kuma, kamar yadda mai fassara Edgar J. Goodspeed ya saka shi, “mizani mai mulki” a cikin zukatanmu.
3. Mecece ce “salama ta Kristi”?
3 Mecece ce “salama ta Kristi”? Kamewa, da kuma kwanciyar rai ne, da muka samu lokacin da muka zama mabiyan Yesu kuma muka san cewa Jehovah Allah da Ɗansa suna ƙaunarmu kuma sun gamsu da mu. Lokacin da Yesu ya kusa ya bar mabiyansa, ya gaya musu: “Salamata ni ke ba ku: . . . Kada zuciyarku ta ɓace, kada ta ji tsoro kuma.” (Yohanna 14:27) Kusan shekaru 2,000 yanzu, shafaffu masu aminci waɗanda suke ɓangaren jikin Kristi suna moran wannan salamar, kuma a yau abokanan tarayyarsu, “waɗansu tumaki,” suna mora. (Yohanna 10:16) Wannan salamar za ta zama rinjaya mai mulki a zukatanmu. Sa’ad da muke fuskantar gwaji mai tsanani, za ta iya taimakonmu mu guji kasala domin tsoro ko kuma mu damu ƙwarai. Bari mu ga yadda wannan ya kasance gaskiya sa’ad da muka fuskanci rashin gaskiya, lokacin da ɗawainiya ta matsa mana, da kuma lokacin da muke jin ba mu cancanta ba.
Lokacin da Muka Fuskanci Rashin Gaskiya
4. (a) Ta yaya Yesu ya san yadda ake yin rashin gaskiya? (b) Yaya Kiristoci suka yi da aka yi musu rashin gaskiya?
4 Sarki Sulemanu ya lura: “Mutum ya sami iko bisa wani, ikon kuwa ya ciwuce shi.” (Mai-Wa’azi 8:9) Yesu ya san gaskiyar waɗannan kalmomin. Lokacin da yake sama, ya ga rashin gaskiya mai yawa da mutane suke yi wa junansu. A duniya, shi kansa ya wahala daga rashin gaskiya, mutum mara zunubi, an zarge shi da saɓo kuma an kashe shi kamar mai laifi. (Matta 26:63-66; Markus 15:27) A yau, har ila rashin gaskiya ya gama duniya, kuma Kiristoci na gaskiya sun wahala ƙwarai da gaske, sun zama “abin ƙi ga dukan al’ummai.” (Matta 24:9) Duk da wahala da suka ɗanɗana a sansanin mutuwa na Nazi, da kuma na Rasha, duk da kasancewa waɗanda taron ’yan banza suka faɗa musu, na zagin ƙarya, da ƙarya wajen farmaki, salama ta Kirista ta sa su sun tsaya da ƙarfi. Sun yi koyi da Yesu, game da wanda muka karanta: “Sa’anda aka zage shi, ba ya mayarda zagi ba; sa’anda ya sha azaba, ba ya yi kashedi ba; amma ya damƙa maganatasa ga wanda ke yin shari’a mai-adalci.”—1 Bitrus 2:23.
5. Idan muka ji game da wani rashin gaskiya a cikin ikilisiya, me ya kamata mu yi la’akari da shi da farko?
5 A ƙaramar hanya, za mu iya gaskata cewa wasu kalilan an yi musu rashin gaskiya a cikin ikilisiyar Kirista ma. A irin wannan yanayi, za mu ji kamar yadda Bulus ya ji, wanda ya ce: “Wanene a ke tuntuɓadda shi, ni ban ƙuna ba?” (2 Korinthiyawa 11:29) Menene za mu yi? Ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Da gaske rashin gaskiya ne?’ Sau da yawa, ba mu san cikakken labarin ba. Wataƙila muna aikata abin da ba shi da kyau bayan mun saurari wani wanda yake da’awar ya san kome. Da kyakkyawan dalili Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mara-wayo yana gaskata kowacce magana.” (Misalai 14:15) Saboda haka muna bukatar mu mai da hankali.
6. Ta yaya za mu aikata idan muna jin kamar an yi rashin gaskiya cikin ikilisiya?
6 A ce, mu kanmu muna jin cewa an yi mana rashin gaskiya. Ta yaya wanda yake da salama ta Kristi a zuciyarsa zai aikata? Muna iya ganin ya kamata mu yi magana da wanda muke jin cewa ya yi mana abin da ba daidai ba. Daga baya, maimakon tattauna batun da dukan wanda zai saurara, me ya sa ba za mu ƙyale batun cikin hannun Jehovah ba cikin addu’a kuma mu dogara a gare shi cewa za a yi gaskiya? (Zabura 9:10; Misalai 3:5) Zai kasance cewa bayan mun yi haka, za mu gamsu mu sulhunta batun a zuciyarmu kuma mu “yi shuru.” (Zabura 4:4) A yawancin yanayi, gargaɗin Bulus zai yi amfani: “Kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowane mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku, hakanan kuma sai ku yi.”—Kolossiyawa 3:13.
7. Menene ya kamata mu riƙa tunawa kullum a sha’aninmu da ’yan’uwanmu?
7 Dukan abin da za mu yi, muna bukatar mu tuna cewa ko da yake ba za mu iya magance abin da ya faru ba, za mu iya kame kanmu. Idan muka aikata abin da bai dace ba domin muna jin an yi rashin gaskiya, wannan zai fi yi wa salamarmu lahani fiye da rashin gaskiyar kansa. (Misalai 18:14) Za mu iya yin tuntuɓe ma mu daina tarayya da ikilisiyar har sai mun gamsu cewa an yi gaskiya. Mai Zabura ya rubuta cewa waɗanda suke ƙaunar dokar Jehovah “ba kuwa wani dalilin tuntuɓe garesu.” (Zabura 119:165) Gaskiyar ita ce, kowanne yana fuskantar rashin gaskiya lokaci lokaci. Kada ka ƙyale irin abin baƙin cikin nan ya shafi bautarka ga Jehovah. Maimakon haka, bari salama ta Kristi ta yi mulki a cikin zuciyarka.
Lokacin da Ɗawainiya ta Matsa Mana
8. Menene ne wasu abubuwa da suke kawo ɗawainiya, kuma menene ɗawainiya za ta iya jawowa?
8 Ɗawainiya ɓangare ne na rayuwa a cikin waɗannan “kwanaki na ƙarshe.” (2 Timothawus 3:1) Hakika, Yesu ya ce: “Kada ku yi alhini saboda ranku, abin da za ku ci; ko kuwa saboda jiki, abin da za ku yafa.” (Luka 12:22) Ba dukan ɗawainiya ba ce take tasowa daga damuwa game da abin duniya. Lutu “ransa ya ɓaci ƙwarai” domin lalata na Saduma. (2 Bitrus 2:7) Bulus ya damu da “tattalin dukan ikilisiya.” (2 Korinthiyawa 11:28) Yesu yana cikin azaba a dare kafin mutuwarsa da “jiɓinsa kuma ya zama kamar manyan ɗararasa na jini, sun[a] fāɗuwa a ƙasa.” (Luka 22:44) A bayyane yake cewa ba dukan ɗawainiya ba ce alamar raunanniyar bangaskiya. Ko menene ya kawo ta, idan ɗawainiya ta yi tsanani kuma ta ɗauki dogon lokaci, za ta iya ɗauke mana salama. Ɗawainiya ta rufe wasu, ta sa suka ji su ba za su iya ci gaba da cika hakkin da bautar Jehovah ta ƙunsa ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Nawaya a zuciyar mutum ta kan sa ta sunkuya.” (Misalai 12:25) Me za mu yi idan ɗawainiya ta matsa mana?
9. Waɗanne matakai za a iya ɗauka a rage ɗawainiya, amma waɗanne tushen ɗawainiya ne ba za a iya kawarwa ba?
9 A wasu yanayi, za mu iya ɗaukan wasu matakai. Idan ciwo ne tushen ɗawainiyarmu, hikima ce idan muka nemi magani, ko da yake wannan batu ne da za mu tsai da shawarar kanmu.a (Matta 9:12) Idan hakkoki da yawa sun taru mana, zai yiwu mu ba wa wasu cikin hakkokin. (Fitowa 18:13-23) To, yaya game da waɗanda—kamar iyaye—waɗanda suke da hakki mai yawa wanda ba za su iya ba wasu ba. Yaya kuma game da Kirista da yake zama tare da wata da ba mai bi ba ce? Yaya kuma game da iyali da suke fuskantar wahalar rashin kuɗi ko kuma suna zama a inda ake yaƙi? Babu shakka, ba za mu iya kawar da dukan tushen ɗawainiya ba a cikin wannan tsarin abubuwa. Duk da haka, za mu iya riƙe salama ta Kristi cikin zukatanmu. Ta yaya?
10. Waɗanne hanyoyi biyu ne Kirista zai iya biɗa ya rage ɗawainiya?
10 Neman ta’aziyya daga Kalmar Allah hanya ce ɗaya. Sarki Dauda ya rubuta: “A cikin yawan wusuwasi da ke cikina ta’aziyyanka suna ji ma raina daɗi.” (Zabura 94:19) Ana samun ‘ta’aziyyar’ Jehovah cikin Littafi Mai Tsarki. Bincika hurarren littafin nan a kai a kai zai taimake mu mu riƙe salama ta Kristi a zukatanmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya agaje ka: Ba za ya yarda a jijjige masu-adalci ba daɗai.” (Zabura 55:22) Hakanan, Bulus ya rubuta: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah. Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku cikin Kristi Yesu.” (Filibbiyawa 4:6, 7) Addu’armu daga zuci da kuma a kai a kai za ta taimaka mana riƙe salamarmu.
11. (a) Ta yaya Yesu ya kasance abin koyi mai kyau a batun addu’a? (b) Yaya za mu ɗauki addu’a?
11 Yesu misali ne kyakkyawa a wannan batu. Wani lokaci, ya yi magana da Ubansa na samaniya cikin addu’a na awoyi a lokaci guda. (Matta 14:23; Luka 6:12) Addu’a ta taimaka masa ya jimre wa gwaji mai tsanani ma. A dare kafin mutuwarsa, damuwarsa ta yi tsanani. Me ya yi? Ya yi “naciyar addu’a.” (Luka 22:44) Hakika, kamilcaccen Ɗan Allah mutum ne mai addu’a. Saboda haka, mu mabiyansa ajizai ya kamata mu koyi halin addu’a! Yesu ya koya wa mabiyansa su “riƙa yin addu’a, kada a suma.” (Luka 18:1) Addu’a magana ta gaske ce kuma mai muhimmanci da Wanda ya san mu fiye da yadda muka san kanmu. (Zabura 103:14) Idan za mu riƙe salama ta Kristi a cikin zukatanmu, za mu yi “addu’a ba fasawa.”—1 Tassalunikawa 5:17.
Nasara Bisa Ajizancinmu
12. Domin waɗanne dalilai ne wasu suna jin cewa hidimarsu ba ta cika ba?
12 Jehovah yana ɗaukan kowannenmu cikin bayinsa abu mai tamani. (Haggai 2:7) Duk da haka, yana yi wa mutane da yawa wuya su gaskata. Wasu za su yi kasala domin tsufa, ƙaruwar hakki a iyali, ko kuma rashin lafiya. Wasu za su ji ba su da ta yi domin abin da suka fuskanta lokacin da suke yara. Har ila wasu kuma za su riƙa tsorata domin kuskure da suka yi a dā, suna shakkar idan Jehovah zai gafarta musu. (Zabura 51:3) Menene za a iya yi game da irin waɗannan?
13. Wace ƙarfafa ce ta Nassi ake da ita ga waɗanda suke jin ba su cancanta ba?
13 Salama ta Kristi za ta tabbatar mana da ƙaunar Jehovah. Za mu iya mai da wannan salama cikin zuciyarmu ta wajen bimbini bisa gaskiyar cewa Yesu bai taɓa cewa tamaninmu ya dangana ne bisa gwada abin da muka yi da abin da wasu suka yi ba. (Matta 25:14, 15; Markus 12:41-44) Abin da ya nanata shi ne aminci. Ya gaya wa almajiransa: “Wanda ya jimre har matuƙa shi ne za ya tsira.” (Matta 24:13) Yesu kansa mutane sun ‘raina shi,’ duk da haka, bai yi shakka cewa Ubansa yana ƙaunarsa ba. (Ishaya 53:3; Yohanna 10:17) Kuma ya gaya wa almajiransa cewa su ma ƙaunatattu ne. (Yohanna 14:21) Domin ya nanata wannan, Yesu ya ce: “Ba a kan sayarda gwarare biyu a bakin [kobo] guda ba? ko ɗaya a cikinsu kuwa ba shi faɗuwa a ƙasa ba sai da sanin Ubanku: amma har da gasussuwan kanku dukansu an ƙididdige su. Kada ku ji tsoro fa; kun fi gwarare masu-yawa daraja.” (Matta 10:30, 31) Tabbaci ne mai daɗaɗawa na ƙaunar Jehovah!
14. Wane tabbaci muke da shi cewa Jehovah yana ɗaukan kowannenmu da tamani?
14 Yesu kuma ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” (Yohanna 6:44) Tun da Jehovah ya jawo mu mu bi Yesu, Yana so mu samu ceto ne. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Ba nufin Ubanku wanda ke cikin sama ba ne, guda ɗaya daga cikin waɗannan ƙanƙanana shi lalace.” (Matta 18:14) Saboda haka, idan kana bauta da zuciya ɗaya, ka yi murna cikin ayyukanka masu kyau. (Galatiyawa 6:4) Idan kana shan azaba domin kuskurenka na dā, ka tabbata cewa Jehovah zai gafarta “a yalwace” ga waɗanda suka tuba da gaske. (Ishaya 43:25; 55:7) Idan domin wani dalili kana jin kasala, ka tuna cewa “Ubangiji yana kusa da masu-karyayyar zuciya, yana ceton irin waɗanda su ke da ruhu mai-tuba.”—Zabura 34:18.
15. (a) Ta yaya Shaiɗan yake so ya hana mu salama? (b) Wace dogara za mu yi ga Jehovah?
15 Shaiɗan ba ya bukatar kome fiye da ya hana ka salama. Shi ke da hakkin zunubi da muka gāda da dukanmu muke kokawa da shi. (Romawa 7:21-24) Babu shakka yana so ka ji cewa ajizancinka ya sa bautarka ba ta karɓuwa ga Allah. Kada ka ƙyale Iblis ya kashe maka gwiwa! Ka mai da hankali ga dabarunsa, kuma bari wannan mai da hankalin ya sa ka ƙuduri aniyyar jimrewa. (2 Korinthiyawa 2:11; Afisawa 6:11-13) Ka tuna cewa, “Allah ya fi zuciyarmu girma, ya kuwa san abu duka.” (1 Yohanna 3:20) Jehovah yana ganin fiye da kasawarmu. Yana ganin abin da yake motsa mu da kuma nufinmu. Ka ƙarfafa daga kalmomin mai Zabura: “Ubangiji ba za ya yarda mutanensa ba: ba kuwa za ya yi ɓari da gadōnsa ba.”—Zabura 94:14.
Haɗa Kai Cikin Salama ta Kristi
16. A wace hanya ce ba mu kaɗai ba ne yayin da muke ƙoƙarin mu jimre?
16 Bulus ya rubuta cewa ya kamata mu bari salama ta Kristi ta yi mulki a cikin zukatanmu domin ana kiranmu “cikin jiki ɗaya.” Shafaffu da Bulus ya rubuta musu wannan an kira su su zama ɓangaren jikin Kristi, tun da su ne raguwar shafaffu a yau. “Waɗansu tumaki” abokanan tarayyarsu sun haɗa kai da su sun zama “garke ɗaya” a ƙarƙashin “makiyayi ɗaya,” Yesu Kristi. (Yohanna 10:16) Tare, a dukan duniya “garke” na miliyoyi suna barin salama ta Kristi ta yi mulki cikin zukatansu. Sanin cewa ba mu kaɗai ba ne yana taimaka mana mu jimre. Bitrus ya rubuta: “Ku tsaya ma [Shaiɗan] fa, kuna tabbatawa cikin bangaskiyarku, kuna kuwa sani ’yan’uwanku da ke cikin duniya suna shan waɗannan azabai da ku ke sha.”—1 Bitrus 5:9.
17. Wane motsuwa muke da shi na barin salama ta Kristi ta yi mulki cikin zukatanmu?
17 Bari duka su ci gaba da koyon salama, ɗiyar nan mai muhimmanci na ruhu mai tsarki na Allah. (Galatiyawa 5:22, 23) Waɗanda Jehovah ya same su marasa aibi, kuma cikin salama a ƙarshe za a albarkace su da rai madawwami a aljanna a duniya, inda adalci yake zaune. (2 Bitrus 3:13, 14) Muna da dalilai da yawa na barin salama ta Kristi ta yi mulki a cikin zukatanmu.
[Hasiya]
a A wasu yanayi, ciwo da ya yi tsanani zai iya kawo ɗawainiya, kamar su baƙin ciki da yake bukatar magani.
Ka Tuna?
• Mecece salama ta Kristi?
• Ta yaya salama ta Kristi za ta yi mulki a cikin zukatanmu sa’ad da muka fuskanci rashin gaskiya?
• Ta yaya salama ta Kristi take taimakonmu mu bi da ɗawainiya?
• Ta yaya salama ta Kristi take yi mana ta’aziyya sa’ad da muke ji ba mu cancanta ba?
[Hoto a shafi na 27]
A gaban masu tuhumarsa, Yesu ya ba da kansa ga Jehovah
[Hoto a shafi na 28]
Kamar rungumar uba mai ƙauna, ta’aziyyar Jehovah za ta rage mana ɗawainiya
[Hoto a shafi na 30]
Jimiri yana da muhimmanci ƙwarai ga Allah