Dā Mu Karnukan Daji Ne—Yanzu Mu Tumaki Ne!
Lokacin da ni da Sakina muke yara, mu maƙwabta ne. Sakina babba ce kuma tana da ƙiba, amma ni ƙarama ce siririya. Sau da yawa muna cacar baki, amma akwai ranar da muka yi doke doke. Tun daga ranar ba mu sake gaisawa ba balle magana. Daga baya, dukanmu muka ƙaura kuma ba mu sake ganin juna ba.
A shekara ta 1994, na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehovah, a hankali na canja halayena. Shekara huɗu bayan haka sa’ad da muke halartar taro na Ranar Taro na Musamman a Bujumbura, Burundi, na yi mamaki da na sadu da Sakina. Na yi farin cikin ganinta, amma ba mu gaisa sosai ba. Ranar, na yi mamakin ganinta tsakanin waɗanda za su yi baftisma! Ita ma ta canja ƙwarai. Ba mai faɗa ba ce kuma wadda sau da yawa muka yi jayayya. Abin farin ciki ne ganin ta nuna ba da kanta ga Allah a fili ta wurin yin baftisma a ruwa!
Da ta fito daga cikin ruwa, na yi gudu na rungume ta na yi mata raɗa: “Ƙin tuna yadda muka yi faɗa?” Ta ce “E na tuna, amma wannan a dā ke nan. Yanzu ni sabuwar mutuniya ce.”
Dukanmu muna farin ciki da muka samu gaskiyar Littafi Mai Tsarki da ta haɗa kanmu kuma ta canja halayenmu mai kama da na karnukan daji zuwa na tumakin Babban Makiyayi, Jehovah Allah. Hakika, gaskiyar Littafi Mai Tsarki tana canja rayuwa.