Me Ya Sa Za Ka Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki?
BILL matashi ne, mai wasan guje-guje, yana da ilimi kuma yana da arziki. Duk da haka, bai gamsu ba. Rayuwarsa ba ta da ma’ana, wannan ya dame shi ƙwarai. Wajen ƙoƙarin ya samu ma’ana a rayuwa, ya bincika addinai dabam dabam, amma bai samu abin da yake nema ba. A shekara ta 1991 ya sadu da Mashaidin Jehovah, wanda ya ba shi wani littafi da ke zancen abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da ma’anar rayuwa. Aka shirya a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Bill don ya sami amsar nan da kuma wasu.
Bill ya tuna abin da ya faru: “Muka yi nazari na farko, domin sau da yawa muna buɗe Littafi Mai Tsarki, na sani cewa abin da nake nema ke nan. Amsoshi da ke cikin Littafi Mai Tsarki masu kyau ne. Bayan nazarin, na ja motata zuwa cikin duwatsu, na fita daga motar tawa na ɗaga murya na yi kuka domin farin ciki. Na yi murna ƙwarai domin na samu amsoshi ga tambayoyina a ƙarshe.”
Hakika, ba kowa ba ne da ya sami gaskiyar Littafi Mai Tsarki yake kukan farin ciki a zahiri. Duk da haka, samun amsoshi ga muhimman tambayoyin rayuwa abin farin ciki ne ga mutane da yawa. Suna ji daidai da mutumin cikin almarar Yesu wanda ya sami dukiyar da aka ɓoye cikin wata gona. Yesu ya ce: “Don farincikin abin kuma ya tafi ya sayarda dukan abin da yake da shi, ya sayi gonan.”—Matta 13:44.
Mabuɗin Rayuwa Mai Ma’ana
Bill ya yi tunani game da muhimmiyar tambaya, Menene dalilin rai? ’Yan falsafa, ’yan tauhidi, da kuma ’yan kimiyya sun yi ta fama da wannan tambayar na shekaru aru aru. Mutane da suke ƙoƙarin su amsa ta sun rubuta littattafai da yawa a kan wannan. Ƙoƙarce-ƙoƙarcensu sun kasance banza, kuma da yawa sun kammala da cewa ba za a iya amsa tambayarta ba. Amma, da akwai amsar. Amsar kuwa tabbacacciya ce, ba a murɗe take ba. Tana bayyane cikin Littafi Mai Tsarki. Mabuɗin rayuwa na farin ciki, mai ma’ana shi ne: Dole ne mu kasance da dangantaka da ta dace da Jehovah, Mahaliccinmu Ubanmu na sama. Ta yaya za mu samu wannan?
Da akwai fasaloli biyu da kamar suna saɓa da juna a matsowa kusa da Allah. Waɗanda suka yi haka suna tsoronsa kuma suna ƙaunarsa. Bari mu bincika nassosi biyu da suka goyi bayan wannan. Da daɗewa, Sarki Sulemanu mai hikima ya yi nazari a kan ’yan Adam kuma ya rubuta abin da ya gano cikin littafin Mai-Wa’azi na Littafi Mai Tsarki. A kammalawarsa, ya ce: “Wannan shi ne ƙarshen zancen; duk an rigaya an ji: ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama wannan kaɗai ne wajibin mutum.” (Mai-Wa’azi 12:13, tafiyar tsutsa tamu ce.) Ƙarnuka daga baya, aka yi tambaya wannene umurni mafi girma cikin Dokar da aka ba Musa, Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.” (Matta 22:37, tafiyar tsutsa tamu ce.) Baƙon abu ne gare ka cewa mu ji tsoron Allah kuma mu yi ƙaunarsa? Bari mu bincika muhimmancin tsoro da kuma ƙauna mu ga yadda suke aiki tare a samun dangantaka mai gamsarwa da Allah.
Abin da Tsoron Allah Yake Nufi
Muna bukatar mu ji tsoro mai daraja idan Allah zai amince da sujjadarmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tsoron Ubangiji mafarin hikima ne.” (Zabura 111:10) Manzo Bulus ya rubuta: “Bari mu kasance da godiya, da za mu yi ma Allah sujjada abin karɓa gareshi tare da ladabi da saduda.” (Ibraniyawa 12:28) Hakazalika, manzo Yohanna ya ga mala’ika a tsakiyar sama cikin wahayi ya soma shelarsa ta bishara da kalmomin nan: “Ku ji tsoron Allah, ku ba shi daraja.”—Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7.
Wannan tsoron Allah, wanda muhimmi ne don rayuwa mai ma’ana, ba daidai yake da tsoro na firgita ba. Za mu iya jin tsoron wani mugu, azzalumi. Amma tsoron Allah—ko kuma tsoro na ibada—saduda da girma ne ga Mahalicci. Ya kuma ƙunsa tsoro mai kyau na ƙin ɓata wa Allah rai domin shi ne Alƙali Mafi Girma kuma Mai Iko Duka, wanda yake da ƙarfi da iko ya hori waɗanda suka yi rashin biyayya.
Tsoro da Ƙauna Suna Aiki Tare
Duk da haka, Jehovah ba ya son mutane su bauta masa domin suna tsoronsa kawai ba. Jehovah, Allah ne musamman na ƙauna. Manzo Yohanna ya motsa ya rubuta: “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Jehovah Allah ya bi da mutane cikin ƙauna, kuma yana son mutane su mai da masa da ƙauna. Amma, ta yaya irin ƙaunar nan take haɗe da tsoro na ibada? Biyun a haɗe suke. Mai Zabura ya rubuta: “Asirin Ubangiji ga masu-tsoronsa ya ke.”—Zabura 25:14.
Ka yi tunanin ladabi da tsoro da ɗa yake da shi ga uba mai ƙarfi mai hikima. Amma kuma ɗan zai more ƙaunar uban. Ɗan zai yarda da uban kuma ya dogara gare shi don kāriya, da tabbacin cewa kāriyarsa za ta kawo amfani. Hakazalika, idan muka yi ƙauna da tsoron Jehovah, za mu yi biyayya da ja-gorarsa, kuma wannan zai amfane mu. Ka lura da abin da Jehovah ya faɗa game da Isra’ilawa: “Da ma da wannan irin zuciya a cikinsu da za su ji tsorona, su kiyaye dukan dokokina kullum, domin su zauna lafiya, duk da ’ya’yansu har abada!”—Kubawar Shari’a 5:29.
I, tsoro na ibada ba ya kai wa ga rashin sukuni amma ga ’yanci, ba baƙin ciki ba amma ga farin ciki. Ishaya ya annabta game da Yesu: “Jin daɗinsa kuma za ya kasance a cikin tsoron Ubangiji.” (Ishaya 11:3) Mai Zabura kuma ya rubuta: “Mai-albarka ne mutum wanda ya ke tsoron Ubangiji, wanda ya ke faranta ransa cikin dokokinsa ƙwarai.”—Zabura 112:1.
Gaskiya ne cewa ba za mu iya tsoron ko ƙaunar Allah ba, sai mun san shi. Abin da ya sa ke nan nazarin Littafi Mai Tsarki yake da muhimmanci ƙwarai. Nazarin yana taimaka mana mu fahimci halayen Allah kuma mu so hikimar bin ja-gorarsa. Yayin da muka jawo kurkusa ga Allah, za mu so mu yi nufinsa kuma muna motsa mu bi umurnansa, da sanin cewa za su amfane mu.—1 Yohanna 5:3.
Abin farin ciki ne mutum ya san yana kan hanyar da ta dace ta rayuwa. Haka yake game da Bill da muka ambata a farko. A kwanan bayan nan ya ce: “Cikin shekaru tara da suka shige tun nazarina na farko cikin Littafi Mai Tsarki, dangantakata da Jehovah ta yi zurfi. Farin ciki na farko da na samu ya yi girma ya zama tafarkin rayuwa. Na ci gaba da kasancewa da ra’ayi mai kyau game da rayuwa. Rayuwata tana cike da ayyuka masu ma’ana, ba neman annashuwar banza ba. Jehovah ya kasance gaskiya a gare ni, kuma na sani yana so na sosai.”
A cikin talifin nazari na uku, za mu sake bincika yadda sanin Jehovah yake kawo farin ciki da fa’idodi ga waɗanda suke yin amfani da shi cikin rayuwarsu.
[Bayanin da ke shafi na 5]
Matsowa kusa da Allah yana nufin za mu yi ƙaunarsa kuma mu ji tsoronsa
[Hoto a shafi na 6]
Yesu ya yi farin ciki cikin tsoron Jehovah