Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 7/1 pp. 3-4
  • Taimako Don Fahimtar Littafi Mai Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Taimako Don Fahimtar Littafi Mai Tsarki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Sani?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Yadda Za Ka Shirya Kanka don Yin Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Za Ka So Ka Ƙara Sanin Littafi Mai Tsarki?
    Za Ka So Ka Ƙara Sanin Littafi Mai Tsarki?
  • Ka Riƙe Kalmar Allah Gam
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 7/1 pp. 3-4

Taimako Don Fahimtar Littafi Mai Tsarki

LITTAFI MAI TSARKI littafi ne na musamman. Marubutan suna da’awar hurewa daga wurin Allah, abin da ke cikinsa kuma ya tabbatar da zancen. (2 Timothawus 3:16) Littafi Mai Tsarki ya nuna abubuwan da ya ƙunsa cikinsa haɗe da, inda muka fito, dalilin kasancewarmu a nan, da kuma inda muka nufa. Lalle littafi ne da ya cancanci mu bincika!

Wataƙila ka yi ƙoƙarin karanta Littafi Mai Tsarki amma ka iske yana da wuyar fahimta. Mai yiwuwa ba ka san inda za ka duba don ka sami amsoshin tambayoyinka ba. Idan haka ne, ai kuna nan da yawa. Yanayinka kama yake da na wani mutum da ya yi zama a ƙarni na farko. Yana kan tafiya cikin karusa daga Urushalima zuwa ƙasarsa, Kush. Ma’aikaci daga ƙasar Kush ya ɗaga murya yana karanta littafin annabci na Ishaya na Littafi Mai Tsarki da aka rubuta shekara ɗari bakwai da suka shige.

Farat ɗaya, sai wani mutum ya gai da shi kusa da karusarsa. Mutumin Filibbus ne, almajirin Yesu, ya tambayi mutumin Kush: “Ka fahimci abin da ka ke karantawa?” Mutumin Kush ɗin ya amsa: “Yaya zan iya, sai ko wani ya bishe ni?” Sai ya gayyaci Filibbus ya hau karusar. Filibbus ya fassara ma’anar inda mutumin yake karantawa kuma ya ci gaba ya yi masa shelar “wa’azin Yesu.”—Ayukan Manzanni 8:30-35.

Kamar yadda Filibbus ya taimaki mutumin Kush ya fahimci Kalmar Allah a can dā, haka ma Shaidun Jehovah suke taimakon mutane su fahimci Littafi Mai Tsarki a yau. Za su yi farin ciki su taimaka maka kai ma. Da ma, ya fi kyau a yi nazarin Littafi Mai Tsarki bi-da-bi, somawa da muhimman koyarwar Nassi. (Ibraniyawa 6:1) Yayin da ka ci gaba, za ka iya cin abin da manzo Bulus ya kira “abinci mai-ƙarfi”—wato, gaskiya masu zurfi. (Ibraniyawa 5:14) Ko da yake Littafi Mai Tsarki ka ke nazarinsa—abubuwan taimako a yin nazarin Littafi Mai Tsarki—suna iya taimaka maka ka san ayoyin Littafi Mai Tsarki game da batutuwa dabam dabam kuma ka fahimce su.

Za a iya shirya yin nazari a lokaci da kuma wuri da ka ke so. Wasu suna nazari ta amfani da tarho ma. Nazarin ba kamar na aji ba ne; tsari ne wanda dominka ne daidai da yanayinka, daidai bisa inda ka fito da kuma iliminka. Ba ka bukatar ka biya kuɗi domin nazarin Littafi Mai Tsarkin. (Matta 10:8) Ba a ba da jarrabawa, kuma ba za a ba ka kunya ba. Za a amsa tambayoyinka, kuma za ka koyi yadda za ka matsa kusa da Allah. Amma, me ya sa ya kamata ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki? Ka yi la’akari da wasu dalilai da ya sa nazarin Littafi Mai Tsarki zai kawo farin ciki ga rayuwarka.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba