Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 7/1 pp. 7-12
  • Kada Ku Zama Masu Manta Abin Da Ku Ka Ji

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ku Zama Masu Manta Abin Da Ku Ka Ji
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene Zai Iya Sa Mu Yi Mantuwa?
  • Ka Ƙi Sha’awoyi na Duniya
  • Biyayya ta Ƙwarai ga Jehovah
  • “Ku Guje ma Fasikanci”
  • Ka Nuna Godiya Ko Yaushe ga Tanadin Jehovah
  • ‘Wane ne Na Jehobah?’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Kada Ka Mance da Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Yadda Za Ka San Hanyoyin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • “Ku Guje Wa Halin Lalata!”
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 7/1 pp. 7-12

Kada Ku Zama Masu Manta Abin Da Ku Ka Ji

“Ku zama masu-aika magana, ba masu-ji kaɗai ba, watau yaudara kanku ke nan.”—YAƘUB 1:22.

1. Waɗanne mu’ujizoji mutanen Isra’ila ta dā suka sami gatar gani?

“ABIN da ba za a manta ba” furci ke nan da ya dace a kwatanta mu’ujizoji da Jehovah ya yi a ƙasar Masar ta dā. Kowacce cikin Annoba Goman babu shakka aba ce ta mamaki. Ceton mutanen Isra’ila a hanya mai ban mamaki a ruwan Jar Teku da ta rabu ta biyo bayan waɗannan farmakin ne. (Kubawar Shari’a 34:10-12) Da ka shaidi waɗannan aukuwa da idanunka, babu shakka ba za ka taɓa manta Wanda ya yi su ba. Duk da haka, mai Zabura ya rera: “[Isra’ilawa] suka manta da Allah mai-cetonsu, Wanda ya aika al’ajibai cikin Masar; ayyuka na ban mamaki cikin ƙasar Ham, al’amura na ban tsoro a bakin Jan Teku.”—Zabura 106:21, 22.

2. Menene ya nuna cewa godiyar Isra’ila don ayyuka masu girma na Allah bai daɗe ba?

2 Bayan sun ƙetare Jar Teku, Isra’ilawa suka “ji tsoron Ubangiji: suka bada gaskiya ga Ubangiji.” (Fitowa 14:31) Mutanen Isra’ila suka bi Musa a rera waƙar nasara ga Jehovah, Maryamu da sauran matan suka bi suna kada tambari da rawa. (Fitowa 15:1, 20) Hakika, ayyuka masu girma na Jehovah sun burge mutanen Allah. Amma godiyarsu ga Wanda ya yi waɗannan ayyuka ba ta daɗe ba. Ba da daɗewa ba da yawa cikinsu suka aikata abubuwa kamar suna da ciwon mantuwa. Suka zama masu gunaguni masu ƙunƙuni ga Jehovah. Wasu sun sa hannu cikin bautar gumaka da lalata.—Litafin Lissafi 14:27; 25:1-9.

Menene Zai Iya Sa Mu Yi Mantuwa?

3. Domin ajizancinmu, me za mu iya mantawa?

3 Rashin godiya ta Isra’ila abin mamaki ne. Amma, irin wannan abin zai iya faruwa da mu. Hakika, ba mu taɓa ganin irin wannan mu’ujizoji na Allah ba. Amma, a dangantakarmu da Allah, babu shakka akwai lokatai da ba za mu manta ba. Wasu cikinmu za mu iya tuna lokacin da muka samu gaskiya daga Littafi Mai Tsarki. Wasu lokatan farin ciki za su iya haɗawa da addu’a ta keɓe kanmu ga Jehovah da kuma baftismarmu cikin ruwa mu Kiristoci na gaskiya. Da yawa cikinmu mun samu taimakon Jehovah wasu lokatai a rayuwarmu. (Zabura 118:15) Musamman kuma, ta mutuwar hadaya na Ɗan Allah, Yesu Kristi, mun samu begen ceto. (Yohanna 3:16) Duk da haka, domin ajizancinmu, lokacin da muke fuskantar mummunar sha’awoyi da alhini na rayuwa, mu ma da wuri za mu iya manta abubuwa masu kyau da Jehovah ya yi dominmu.

4, 5. (a) Ta yaya Yaƙub ya yi kashedi game da haɗarin zama masu manta abin da muka ji? (b) Yaya za mu yi amfani da kwatancin Yaƙub na mutumin da kuma madubi?

4 A cikin wasiƙarsa zuwa ga ’yan’uwa Kiristoci, ɗan uban Yesu Yaƙub ya yi kashedi game da haɗarin zama masu manta abin da suka ji. Ya rubuta: “Ku zama masu-aika magana, ba masu-ji kaɗai ba, watau yaudarar kanku ke nan. Gama idan kowa mai-jin magana ne, ba mai-aikawa ba, yana kama da mutum wanda yana duban halittaciyar fuskarsa a cikin madubi: gama ya duba kansa, kāna ya tafi, nan da nan kuwa ya manta irin mutum da ya ke.” (Yaƙub 1:22-24) Menene Yaƙub yake nufi da waɗannan kalmomin?

5 Idan muka tashi da safe, mukan duba madubi mu ga gyara da ya kamata mu yi a yadda muke. Yayin da muka yi ayyuka dabam dabam, zuciyarmu na kan wasu abubuwa, sai mu daina tunanin abin da muka gani a madubi. Wannan zai iya faruwa a fanni na ruhaniya. Yayin da mun duba Kalmar Allah, za mu iya gwada abin da muke da abin da Jehovah yake zata mu zama. Saboda haka, muna ganin kasawarmu kai tsaye. Wannan sani ya kamata ya motsa mu mu yi gyara a halayenmu. Amma yayin da muke tafiyar da ayyukanmu na kullum da kuma fama da matsalolinmu, za mu iya daina tunani game da al’amura na ruhaniya da sauƙi. (Matta 5:3; Luka 21:34) Yana kama ne da manta da ayyuka masu kyau da Allah ya yi dominmu. Idan wannan ya faru, sha’awar yin zunubi za ta zama da sauƙi.

6. Wane bincike na Nassi zai taimaka mana kada mu manta da kalmar Jehovah?

6 A hurariyar wasiƙarsa ta farko zuwa ga Korinthiyawa, manzo Bulus ya yi nuni ga Isra’ilawa da suka yi mantuwa cikin daji. Yadda Kiristoci na ƙarni na farko suka amfana daga kalmomin Bulus, sake duba abin da ya rubuta zai taimaka mana kada mu manta da kalmar Jehovah. Saboda haka, bari mu bincika 1 Korinthiyawa 10:1-12.

Ka Ƙi Sha’awoyi na Duniya

7. Wane tabbaci na ƙaunar Jehovah da ba za a iya ƙaryatawa ba Isra’ilawa suka samu?

7 Abin da Bulus ya ce game da Isra’ilawa gargaɗi ne ga Kiristoci. Kaɗan ciki, Bulus ya rubuta: “ ’Yan’uwa, ba ni so ku rasa sani, ubaninmu duka ƙarƙashin girgije ne, dukansu kuwa suka ratsa teku; dukansu kuwa aka yi masu baftisma zuwa cikin Musa cikin girgije da teku kuma.” (1 Korinthiyawa 10:1-4) Mutanen Isra’ila a zamanin Musa sun ga bayyanuwar ikon Allah mai girma, haɗe da umudi na girgije ta mu’ujiza ta Allah da ke tafe da su da rana da kuma ke taimaka musu suka tsira ta Jar Teku. (Fitowa 13:21; 14:21, 22) I, waɗannan Isra’ilawa sun samu tabbaci da ba za a iya ƙaryatawa ba na ƙaunar Jehovah dominsu.

8. Menene sakamakon mantuwa na ruhaniya da Isra’ila suka yi?

8 Bulus ya ci gaba “amma yawancinsu Allah ba ya ji daɗinsu ƙwarai ba; gama aka jirkice su cikin jeji.” (1 Korinthiyawa 10:5) Abin baƙin ciki! Yawancin Isra’ilawa da suka bar ƙasar Masar sun hana kansu shiga Ƙasar Alkawari. Da Allah ya ƙi su don rashin bangaskiyarsu, sun halaka a daji. (Ibraniyawa 3:16-19) Menene za mu iya koya daga wannan? Bulus ya ce: “Waɗannan al’amura fa sun zama misalai a garemu, domin kada mu yi kwaɗayin miyagun abu, kamar yadda suka yi kwaɗayi.”—1 Korinthiyawa 10:6.

9. Yaya Jehovah ya yi wa mutanensa tanadi, kuma me Isra’ila suka aikata?

9 Isra’ilawa suna da abubuwa da yawa da zai sa su kasance da ruhaniya yayin da suke cikin daji. Sun yi alkawari da Jehovah kuma suka zama al’umma da suka keɓe kansu gare shi. Ban da haka ma, an ba su tsarin firistanci, mazauni cibiyar sujjada, da tsarin miƙa wa Jehovah hadayu. Amma, maimako su yi farin ciki don waɗannan kyauta na ruhaniya, sun yarda wa kansu kada su gamsu da tanadi da Allah ya yi musu.—Litafin Lissafi 11:4-6.

10. Me ya sa ya kamata koyaushe mu tuna da Allah?

10 Ba kamar Isra’ilawa cikin daji ba, mutanen Jehovah a yau suna more amincewar Allah. Yana da muhimmanci mu tuna da Allah, kowannenmu. Yin haka zai taimake mu mu ƙi sha’awoyi na son kai da zai iya mallakar ra’ayinmu na ruhaniya. Dole ne mu ƙuduri aniyya “mu rayu da hankali da adalci da ibada cikin wannan zamani na yanzu, yayin da muna ƙin rashin ibada da sha’awoyi na duniya.” (Titus 2:12) Mu waɗanda tun muna jarirai muke tarayya da ikilisiyar Kirista kada mu taɓa tunanin cewa ana hana mu abu mai kyau. Idan irin wannan tunani ya zo zuciyarmu, zai yi kyau mu tuna da Jehovah da kuma albarka na ban al’ajabi da ya shirya dominmu.—Ibraniyawa 12:2, 3.

Biyayya ta Ƙwarai ga Jehovah

11, 12. Yaya mutum zai zama da laifin bautar gumaka ba tare da bauta wa siffofi ba?

11 Bulus ya ba mu wani gargaɗi yayin da ya rubuta: “Kada ku zama masu-bautan gumaka kuma, kamar yadda waɗansu daga cikinsu su ke; kamar yadda an rubuta, Jama’a suka zauna garin su ci su sha, suka tashi kuma garin su yi wasa.” (1 Korinthiyawa 10:7) Bulus yana magana ne game da lokacin da Isra’ilawa suka nace wa Haruna ya yi musu ɗan maraƙi na zinariya. (Fitowa 32:1-4) Ko da yake da kyar ne mu juya ga bautar gunki, za mu iya zama masu bautar gumaka ta barin sha’awoyi na son kai su janye mu daga bauta wa Jehovah da dukan zuciyarmu.—Kolossiyawa 3:5.

12 A wani lokaci kuma, Bulus ya rubuta game da wasu da suke damuwa don abin duniya kawai maimakon al’amura na ruhaniya. Game da waɗanda suke tafiya “maƙiyan [gungumen azabtar da] Kristi ne,” ya rubuta “waɗannan ƙarshensu halaka ne, allahnsu ciki ne.” (Filibbiyawa 3:18, 19) Abin da suke bauta wa ba sifoffi ba ne. Muradinsu ne na abin duniya. Gaskiya, ba dukan muradi ba ne munana. Jehovah ya halicce mu da bukatu da kuma iyawa na more nishaɗi dabam dabam. Amma waɗanda suka saka yin nishaɗi fiye da dangantakarsu da Allah, hakika sun zama masu bautar gumaka.—2 Timothawus 3:1-5.

13. Menene za mu iya koya daga labarin ɗan maraƙi na zinariya?

13 Bayan sun bar ƙasar Masar, Isra’ilawa suka yi maraƙin zinariya su bauta wa. Ƙari ga gargaɗi game da bautar gumaka, akwai wani darasi mai kyau cikin wannan labarin. Isra’ilawan sun ƙi ja-gora da ke daga Jehovah. (Fitowa 20:4-6) Duk da haka, ba su nufa su ƙi Jehovah Allahnsu ba. Sun yi hadayu ga maraƙin zinariya kuma sun ƙira bikin “idi ga Ubangiji.” Sun ruɗi kansu da tunani cewa Allah zai ƙyale rashin biyayyarsu. Wannan zagin Jehovah ne, kuma ya sa shi fushi sosai.—Fitowa 32:5, 7-10; Zabura 106:19, 20.

14, 15. (a) Me ya sa Isra’ilawa ba su da hujja na zama masu manta abin da suka ji? (b) Idan mun ƙuduri aniyya kada mu zama masu manta abin da muka ji, menene za mu yi game da umurnan Jehovah?

14 Da kyar ne Mashaidin Jehovah ya shiga wani addinin ƙarya. Amma ko da muna cikin ikilisiya, wasu za su iya ƙin ja-gorar Jehovah a wasu hanyoyi. Mutanen Isra’ila ba su da dalilin zama masu manta abin da suka ji. Sun ji Dokoki Goma kuma suna wurin lokacin da Musa ya ba su umurnin Allah: “Ba za ku yi waɗansu alloli game da ni ba; na azurfa, ko na zinariya, ba za ku yi wa kanku su ba.” (Fitowa 20:18, 19, 22, 23) Har ila, Isra’ilawa suka bauta wa maraƙin zinariya.

15 Mu ma ba mu da ƙarfafar hujja idan za mu zama masu manta abin da muka ji. A cikin Nassosi, muna da ja-gora daga Allah game da fasalolin rayuwa da yawa. Alal misali, Kalmar Jehovah musamman ta haramta cin bashi ba tare da biya ba. (Zabura 37:21) An umurci yara su yi biyayya ga iyayensu, an zaci ubanni su yi renon yaransu cikin “horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afisawa 6:1-4) An umurci Kiristoci da ba su yi aure ba su yi haka “sai dai cikin Ubangiji,” kuma an gaya wa bayin Allah da suka yi aure: “Aure shi zama abin darajantuwa a wajen dukan mutane, gado kuma shi kasance mara-ƙazanta: gama da fasikai da mazinata Allah za shi shar’anta.” (1 Korinthiyawa 7:39; Ibraniyawa 13:4) Idan mun ƙuduri aniyyar ba za mu zama masu manta abin da muka ji ba, za mu ɗauki waɗannan da wasu ja-gora daga Allah da muhimmanci kuma mu bi su.

16. Menene sakamakon bauta wa maraƙin zinariya?

16 Jehovah bai amince da ƙoƙarin Isra’ilawa su bauta masa yadda suke so ba. Maimako, an halaka 3,000 wataƙila don sun yi ja-gora a ayyukan tawaye na bauta wa maraƙin zinariya. Sauran masu laifin sun sha annoba daga Jehovah. (Fitowa 32:28, 35) Darasi ne ga kowane da ke karanta Kalmar Allah amma sun zaɓa wa kansu abin da suke so su yi wa biyayya!

“Ku Guje ma Fasikanci”

17. Wace aukuwa ce 1 Korinthiyawa 10:8 ke magana a kanta?

17 Bulus ya ambata wuri ɗaya da sha’awoyi na jiki za su iya jawo mantuwa ta ruhaniya yayin da ya ce: “Kada mu yi fasikanci kuma, kamar yadda waɗansu daga cikinsu suka yi, rana ɗaya kuwa suka faɗi, mutum zambar ashirin da uku.” (1 Korinthiyawa 10:8) A nan Bulus na nuni ne ga abin da ya faru a Filayen Mowab a ƙarshen tafiya ta shekara 40 na Isra’ilawa cikin daji. Ba da daɗewa ba Isra’ilawa sun sami taimakon Jehovah a cin ƙasashe na gabashin Urdun, amma da yawa sun zama masu mantuwa da butulci. A iyakar Ƙasar Alkawari, an jarabe su da lalata da bauta mara tsabta na Baal na Peor. An halaka 24,000, cikinsu 1,000 sune ke ja-gorar wasu zuwa munanan ayyuka.—Litafin Lissafi 25:9.

18. Wane irin hali ne zai iya kai ga lalatar jima’i?

18 An san mutanen Jehovah a yau sosai domin mizanan ɗabi’arsu masu girma. Amma yayin da an jarabe su da lalata, wasu Kiristoci sun daina tunani game da Allah da ƙa’idodinsa. Sun zama masu manta abin da suka ji. Da farko, jarabar ƙila ba za ta ƙunshi fasikanci ba. Zai iya zama son kallon hotunan tsirarun mutane, saka kai cikin yin batsa ko rawan ido da bai dace ba, ko kuma yin tarayya ta kurkusa da mutane marasa ɗabi’a. Duk waɗannan abubuwa sun kai Kiristoci cikin halayen zunubi.—1 Korinthiyawa 15:33; Yaƙub 4:4.

19. Wane gargaɗi na Nassi ne ke taimaka mana mu “guje ma fasikanci”?

19 Idan an jarabe mu da lalata, kada mu daina tunani game da Jehovah. Maimako, dole ne mu kiyaye tunasarwar cikin Kalmarsa. (Zabura 119:1, 2) Da yake mu Kiristoci ne, yawancinmu muna iyakacin ƙoƙarinmu mu kasance da tsabta ta ɗabi’a, amma yin abin da yake daidai a gaban Allah na bukatar ƙoƙari sosai. (1 Korinthiyawa 9:27) Bulus ya rubuta, zuwa ga Kiristoci a Roma: “Biyayyarku ya yaɗu zuwa dukan mutane. Ina fa murna da ku: amma ina so ku zama masu-hikima zuwa abin da ke nagari, salihai zuwa abin da ke mugu.” (Romawa 16:19) Yadda aka kashe Isra’ilawa 24,000 don zunubansu, masu fasikanci da masu laifi jim kaɗan za su sha hukunci mai tsanani na Jehovah. (Afisawa 5:3-6) Maimakon mu zama masu manta abin da muka ji, dole ne mu ci gaba da “guje ma fasikanci.”—1 Korinthiyawa 6:18.

Ka Nuna Godiya Ko Yaushe ga Tanadin Jehovah

20. Ta yaya Isra’ilawa suka gwada Jehovah, menene sakamakon haka?

20 Yawancin Kiristoci ba su taɓa faɗa wa lalata ba. Duk da haka muna bukatar mu mai da hankali kada mu ƙyale kanmu mu biɗi tafarki da ke kaiwa ga yin gunaguni da zai jawo rashin amincewar Allah. Bulus ya gargaɗe mu: “Kada mu gwada Ubangiji kuma, kamar yadda waɗansu daga cikinsu suka gwada, suka halaka a bakin macizai. Kada ku yi gunaguni kuma, kamar yadda waɗansu daga cikinsu suka yi, suka lalace a hannun mai-halakarwa.” (1 Korinthiyawa 10:9, 10) Isra’ilawan sun yi gunaguni game da Musa da Haruna—E, sun yi gāba da Allah kansa—suna ƙunƙuni game da manna da ya yi musu tanadinsa ta mu’ujiza. (Litafin Lissafi 16:41; 21:5) Shin Jehovah ya yi fushi ne game da fasikancinsu fiye da gunaguninsu? Labarin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa macizai sun kashe masu gunaguni da yawa. (Litafin Lissafi 21:6) Da farko, an halaka masu gunaguni fiye da 14,700 da suka yi tawaye. (Litafin Lissafi 16:49) Saboda haka, kada mu gwada haƙurin Jehovah ta bi da tanadinsa da rashin hankali.

21. (a) Wane gargaɗi aka hure Bulus ya rubuta? (b) In ji Yaƙub 1:25, yaya za mu kasance da farin ciki na gaske?

21 Da rubuta wa ’yan’uwa Kiristoci, Bulus ya kammala jerin kashedinsa da gargaɗin nan: “Waɗannan al’amura dai suka same su watau misali ne; kuma aka rubuta su domin gargaɗi garemu, mu waɗanda matuƙan zamanu sun zo a kanmu. Domin wannan fa, wanda ya ke maida kansa yana tsaye, shi yi lura kada ya fāɗi.” (1 Korinthiyawa 10:11, 12) Kamar Isra’ilawa, mun samu albarka da yawa daga Jehovah. Amma, ba kamar su ba, kada mu taɓa mantuwa kuma mu kasa godiya ga abubuwa masu kyau da Allah yake mana. Lokacin da ɗawainiya ta rayuwa ke damunmu, bari mu yi tunani a kan alkawura masu ban al’ajabi da ke cikin Kalmarsa. Bari mu tuna da dangantakarmu mai tamani da Jehovah kuma mu ci gaba da aikin wa’azi na Mulki da aka ɗanka mana. (Matta 24:14; 28:19, 20) Irin wannan tafarki babu shakka zai kawo mana farin ciki na gaske, domin Nassosi sun yi alkawari: “Wanda ya duba cikin cikakkiyar shari’a, shari’a ta ’yanci, ya lizima, shi kuwa ba mai-ji wanda ke mantawa ba ne, amma mai-yi ne wanda ke aikatawa, wannan za ya zama mai-albarka a cikin aikinsa.”—Yaƙub 1:25.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene zai iya sa mu zama masu manta abin da muka ji?

• Me ya sa biyayya ta ƙwarai ga Allah ke da muhimmanci?

• Yaya za mu iya “guje ma fasikanci”?

• Menene ya kamata ya zama halinmu game da tanadi na Jehovah?

[Hoto a shafi na 9]

Isra’ilawa sun manta da ayyukan Jehovah masu girma dominsu

[Hoto a shafi na 10]

Mutanen Jehovah sun ƙuduri aniyyar su riƙe mizanan ɗabi’a mai girma

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba