Me Ya Sa Ake Wa Masu Iko—Rashin Biyayya?
“Wata rana za a yi ramako a kan raina iko da ake yi, na addini da na jiha, na zaman jama’a da na siyasa, a dukan duniya , zai zama aukuwa na musamman a shekaru na ƙarshe.”
SHEKARU sun wuce tun shekara ta 1960, shekarun da ’yar tarihi kuma ’yar falsafa Hannah Arendt ta yi zancensu a nan. A yau, yanayin rashin biyayya ga masu iko yana ƙara muni fiye da dā.
Alal misali, wani rahoto na baya bayan nan cikin jaridar The Times ta London ya ce: “Wasu iyaye ba sa son malami ya yi iko a kan ’ya’yansu idan kuwa aka yi ƙoƙari a hora musu da ’ya’yansu sai su ƙi.” Sau da yawa, idan aka yi wa yaransu horo a makaranta, sai iyayensu su je makarantar ba domin kawai su yi burga wa malaman ba amma kuma su faɗā musu.
An ɗauko wani abin da mai magana da yawun Ƙungiyar Tarayyar Shugaban Malamai a Britaniya ya ce: “Jama’a suna cewa ‘ina da dama,’ maimakon su ce ‘ina da hakki.’ ” Ban da ƙin koya wa yaransu yin biyayya mai kyau ga masu iko, wasu iyaye ma ba sa yi wa yaransu horo—kuma ba sa son wasu su yi musu horo. Yara da suke bin “ra’ayin” ana ƙyale su su yi banza da ikon iyaye da kuma na malamai, kuma an annabta sakamakon haka—“sabuwar tsara mara biyayya ga masu iko da ba su san abin da ke daidai da wanda ba daidai ba,” yadda Margarette Driscoll ta rubuta ke nan.
Jaridar Time cikin talifinta “Tsara da ta Lalace” ta yi magana game da gaskiyar wasu matasa na Rasha, ta ɗauko abin da wani mawaƙin rap ya faɗa da ya ce: “Ta yaya za a haife wani cikin duniyar nan, inda babu abin da ke daɗewa, babu nagarta, kuma ya yi gaba gaɗi?” Masanin zaman jama’a Mikhail Topalov ya amince da wannan furcin: “Yara ba wawaye ba ne. Sun ga an ruɗe iyayensu, sun ga yadda iyayensu suka yi hasarar ajiyarsu da kuma ayyukansu. Za mu yi tsammanin su yi biyayya ga masu iko ne?”
Ba zai zama daidai ba a kammala cewa rashin aminci ga masu iko daga wajen yara ne kaɗai. A yau, mutane duka ba sa amincewa da masu iko, har raini suke yi. Wannan yana nufin cewa ba za a iya amincewa da ko wane irin iko ba ke nan? Idan aka bi da shi daidai, an ba da ma’anar iko cewa “ƙarfi ko ikon gudanar da, yi shari’a wa, ko kuma na hana wasu halaye,” yakan zama nagarin abu. Yakan zama da amfani ga mutanen da kuma ga jama’ar yanki. Talifi na biye zai bayyana yadda wannan yake haka.