“Ku Duka Kuwa ’Yan’uwa Ne”
“Kada a kira ku Malam: gama malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa ’yan’uwa ne.”—MATTA 23:8.
1. Wane batu ne ya dace mu bincika?
“WA YA cancanci a fi girmama shi, mai wa’azi a ƙasan waje ko kuma mai hidima a Bethel?” wata Kirista a ƙasar Gabas cikin rashin sani ta tambayi wata da take wa’azi na ƙasar waje daga Australiya. Tana so ta san wanda ya kamata a fi ba shi daraja, mai wa’azi da ya zo daga ƙasan waje ko kuma ɗan ƙasa da yake hidima a ofishin reshe na Watch Tower Society. Wannan tambaya da aka yi cikin rashin sani, ya nuna al’ada da ta amince da matsayi, ta ba mai wa’azin nan ta ƙasan waje mamaki. Tambayar nan waye ya fi girma, ta taso ne daga muradin sanin wa suka fi iko da kuma tasiri.
2. Yaya ya kamata mu ɗauki ’yan’uwanmu masu bi?
2 Wannan damuwar ba sabuwar aba ba ce. Har almajiran Yesu ma sun yi jayayya game da waye ya fi girma tsakaninsu. (Matta 20:20-24; Markus 9:33-37; Luka 22:24-27) Su ma sun fito ne daga al’ada inda aka amince da matsayi, na addinin Yahudawa a ƙarni na farko. Da irin jama’ar nan a zuci, Yesu ya yi wa almajiransa gargaɗi: “Kada a kira ku Malam: gama malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa ’yan’uwa ne.” (Matta 23:8) Manazarcin Littafi Mai-Tsarki Albert Barnes ya lura cewa lakabi na addini irinsu “Malam,” da ke nufin “Mai Koyarwa,” “ya kan sa fahariya da tunanin fifiko ciki waɗanda suke amsarsa, kuma ya sa waɗanda ba su amsarsa kishi da tunanin su ba wani abu ba ne; kuma ilahirin ruhu da halin ya saɓa da yadda Kristi ya kasance da sauƙi.” Hakika, Kiristoci suna guje wa kiran masu kula tsakaninsu “Dattijo Kaza da kaza,” a yin amfani da kalmar “dattijo” kamar lakabi na kiran daɗin baki. (Ayuba 32:21, 22) A wata sassa kuma, dattiɓai da suke bin gargaɗin Yesu suna daraja waɗanda suke cikin ikklisiya, yadda Jehovah yake daraja masu bauta masa da aminci, Yesu Kristi kuma yana daraja mabiyansa masu aminci.
Misalin Jehovah da Kuma na Yesu
3. Ta yaya Jehovah ya ba halittunsa na ruhu daraja?
3 Ko da yake Jehovah “Maɗaukaki Duka” ne, tun daga farko ya daraja halittunsa ta wurin haɗa su cikin ayyukansa. (Zabura 83:18) Lokacin da ya halicce mutum na farko, Jehovah ya haɗa Ɗansa makaɗaici ‘gwanin aiki’ cikin aikin halitta. (Misalai 8:27-30; Farawa 1:26) Jehovah ya gayyaci mala’ikunsa na sama su faɗa yadda za a halaka mugun Sarki Ahab lokacin da Ya ƙuduri aniyar yin hakan.—1 Sarakuna 22:19-23.
4, 5. Ta yaya Jehovah ya ba halittunsa mutane daraja?
4 Jehovah yana sarauta shi Mafifici Mai Ikon Mallakar sararin samaniya. (Kubawar Shari’a 3:24) Ba ya bukatar ra’ayin mutane. Duk da haka, ya ƙasƙantar da kansa don ya lura da su. Mai zabura ya rera waƙa: “Wanene kinin Ubangiji Allahnmu, wanda ya ke da kursiyinsa cikin ɗaukaka, wanda ya kan ƙasƙantarda kansa domin ya duba abubuwan da ke cikin sama da duniya? Ya kan tada matalauci daga cikin turɓaya.”—Zabura 113:5-8.
5 Kafin ya halakar da Saduma da Gwamarata Jehovah ya saurari tambayoyin Ibrahim kuma ya gamsar da muradinsa na yin gaskiya. (Farawa 18:23-33) Ko da yake Jehovah ya riga ya san sakamakon roƙon Ibrahim, ya saurari Ibrahim da haƙuri kuma ya amince da tunaninsa.
6. Menene sakamakon daraja da Jehovah ya ba wa Habakkuk lokacin da ya yi masa tambaya?
6 Jehovah ya kuma saurari Habakkuk, wanda ya yi tambaya: “Ya Ubangiji, har yaushe zan yi kira, kai kuwa ba ka yarda ka ji ba?” Jehovah ya ji kamar ana zargin ikonsa ne? A’a, ya ɗauki tambayar Habakkuk aba da take daidai, kuma saboda haka ya bayana nufinsa cewa zai tada Chaldiyawa su zartar da hukunci. Ya tabbatar wa annabin cewa ‘wannan hukunci da aka annabta lallai zai zo.’ (Habakkuk 1:1, 2, 5, 6, 13, 14; 2:2, 3) Ta wajen ɗauka damuwar Habakkuk da muhimmanci da kuma amsa masa, Jehovah ya daraja annabin. A sakamakon haka, annabi da yake baƙin ciki ya yi murna, da cikakken dogara ga Allah mai cetonsa. Wannan ya bayyana a huraren littafin Habakkuk da ya ƙarfafa dogararmu ga Jehovah a yau.—Habakkuk 3:18, 19.
7. Me ya sa matsayin Bitrus a Fentikos 33 A.Z. yake da muhimmanci?
7 Yesu Kristi misali ne mai kyau na ba wasu daraja. Yesu ya gaya wa almajiransa cewa “wanda za ya yi musun sanina a gaban mutane, shi zan yi musunsa a gaban Ubana.” (Matta 10:32, 33) Duk da haka, a daren da aka ci amanansa, duk almajiransa suka yasar da shi, kuma manzo Bitrus ya yi musun saninsa sau uku. (Matta 26:34, 35, 69-75) Yesu ya duba fiye da yadda yake a jiki, ya lura da yadda Bitrus yake ji a ciki, tubansa na ƙwarai. (Luka 22:61, 62) Kwanaki 51 kawai bayan haka, Kristi ya ba manzon da ya tuba girma, ya sa shi ya wakilci almajirai 120 na Yesu a ranar Fentikos kuma ya yi amfani da “muƙullai na mulkin” na farko. (Matta 16:19; Ayukan Manzanni 2:14-40) An ba Bitrus zarafi ya ‘dawo ya kuma ƙarfafa ’yan’uwansa.’—Luka 22:31-33.
Ka Girmama Waɗanda Suke Cikin Iyali
8, 9. Yaya maigida zai yi koyi da Jehovah da kuma Yesu wajen ba matarsa girma?
8 Yana da kyau magidanta da iyaye su yi koyi da Jehovah da kuma Yesu Kristi a nuna iko da Allah ya ba su. Bitrus ya yi gargaɗi: ‘Ku maza, ku zauna da matanku bisa ga sani, kuna ba da girma ga mace, kamar ga wadda ta fi rashin ƙarfi.’ (1 Bitrus 3:7) Ka yi tunanin yin amfani da tulu, babu shakka, yana saurin fashewa fiye da akushi. Ba za ka mai da hankali sosai ba? Maigida zai yi hakan ta wurin koyi da Jehovah, ya saurari ra’ayin matarsa lokacin da suke yin shawara game da al’amura na iyali. Ka tuna cewa Jehovah ya mai da hankali ya saurari abin da Ibrahim zai faɗa. Tun da yake ajizi ne, maigida ba zai gane duka abin da al’amarin ya ƙunsa ba. Saboda haka ba zai yi kyau ya ba matarsa girma ta wurin yin la’akari da ra’ayinta da gaske ba?
9 A ƙasashe inda matsayin namiji yake da ƙarfi sosai, maigida zai tuna cewa matarsa za ta sha ɗamara kafin ta faɗi abin da yake zuciyarta. Ka yi koyi da hanyar da Yesu Kristi ya bi da almajiransa, sashen ajin amaryarsa a gaba, lokacin da yake duniya. Yana daraja su, yana yin la’akari da kasawarsu na jiki da na ruhaniya kafin ma su faɗa bukatarsu. (Markus 6:31; Yohanna 16:12, 13; Afisawa 5:28-30) Ƙari ga haka, ka lura da abin da matarka take yi maka da iyalinka, kuma ka furta godiyarka cikin kalmomi da kuma ayyukanka. Jehovah da Yesu sun yi godiya, yaba ma, kuma sun albarkaci waɗanda suka cancanta. (1 Sarakuna 3:10-14; Ayuba 42:12-15; Markus 12:41-44; Yohanna 12:3-8) Da maigidanta ya zama Shaidan Jehovah, wata mata Kirista a Gabas ta ce: “Maigidana yana tafiya taƙu uku ko huɗu a gaba da ni, ya bar ni na ɗauki kome. Yanzu yana ɗaukan jakan kaya kuma ya nuna godiya don abubuwa da na ke yi a gida!” Furta kalmomin godiya na gaske yana taimakawa sosai wajen sa matarka ta ji tana da daraja.—Misalai 31:28.
10, 11. Menene iyaye za su iya koya daga misali mai kyau na Jehovah a bi da al’ummar Isra’ila mai tawaye?
10 A bi da yaransu, musamman ma lokacin da ake bukatar horo, ya kamata iyaye su yi koyi da misalin Allah. “Ubangiji ya shaida ma Isra’ila da Yahuda” su juyo ga barin miyagun ayyukansu, amma suka “taurare wuyansu.” (2 Sarakuna 17:13-15) Isra’ilawa “suka yi masa daɗin baki, suka yi masa ƙarya da harshensu.” Iyaye da yawa mai yiwuwa suna ji cewa yaransu wasu lokatai suna yin hakanan. Isra’ilawa “suka jarabci Allah” suka cakune shi, suna ɓata masa rai. Duk da haka, Jehovah yana “da tausayi, ya gafarta laifinsu, ba ya halaka su ba.”—Zabura 78:36-41.
11 Jehovah ya ma roƙi Isra’ilawa: “Zo yanzu, mu yi bincike tare, . . . ko da zunubanku sun yi kamar mulufi, za su yi fari kamar snow.” (Ishaya 1:18) Ko da yake Jehovah ba shi da laifi, ya gayyace al’umma mai tawaye ta zo su daidaita al’amura. Hali mai kyau ne da iyaye za su yi koyi da shi a bi da yaransu! Idan bukata ta kama, ku ba su girma ta wurin saurara ga nasu labarin, kuma ku gaya musu dalilin da ya sa za su canja.
12. (a) Me ya sa ya kamata mu guje ba yaranmu girma fiye da Jehovah? (b) Me ake bukata idan za mu ga kwarjinin yaranmu lokacin da muke hore su?
12 Babu shakka, a wasu lokatai yara suna bukatar gargaɗi mai ƙarfi. Bai kamata iyaye su yi kamar Eli, wanda ‘ya fi ba da girma ga ’ya’yansa fiye da Jehovah.’ (1 Samuila 2:29) Har ila yau, matasa suna bukatar su ga cewa ƙauna ce ta sa aka yi musu horo. Ya kamata su gane cewa iyayensu suna ƙaunarsu. Bulus ya yi wa ubanni gargaɗi: “Kada ku yi ma ’ya’yanku cakuna har su yi fushi: amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afisawa 6:4) Lokacin da aka ɗauki matsayin maigida, abin da ake nufi shi ne uba ya mai da hankali ga kwarjinin yaran, kada yana sa su fushi domin yawan tsanantawansa. Gaskiya, yin la’akari da kwarjinin yara yana bukatar lokaci da ƙoƙari a wajen iyayen, amma ribar yin haka ya cancanci dukan sadaukarwarsu.
13. Menene ra’ayin Littafi Mai-Tsarki game da tsofaffi cikin iyali?
13 Girmama waɗanda suke cikin iyali ya wuce ganin kwarjinin mata da yara. “Idan ka tsufa, ka yi biyayya wa yaranka,” in ji wani karin magana na mutanen Japan. Abin da karin maganar nan ke nufin shi ne cewa ya kamata iyaye tsofaffi su guje wa wuce matsayinsu na iyaye, ya kamata su ji abin da yaransu da suka yi girma suke faɗa. Ko da Nassosi ya ce iyaye su ba yaransu girma ta wurin sauraron abin da suke faɗa, bai kamata yara su raina tsofaffi cikin iyalin ba. Misalai 23:22 ya ce: “Kada ka raina uwarka lokacinda ta tsufa.” Sarki Sulemanu ya yi amfani da wannan karin magana wajen ba wa uwarsa girma lokacin da ta zo don ta yi wani roƙo. Sulemanu ya ajiye wata kujerar sarauta a gefen damarsa don ya saurari abin da Bath-sheba, uwarsa tsohuwa, za ta gaya masa.—1 Sarakuna 2:19, 20.
14. Ta yaya za mu girmama tsofaffi da suke cikin ikklisiya?
14 A cikin iyalinmu na ruhaniya mai girma, muna da matsayi mai kyau mu “gabatarda juna” a ba da girma ga tsofaffi da suke cikin ikklisiya. (Romawa 12:10) Ba za su iya yin abubuwa da yawa yadda suke yi a dā ba, wannan zai sa suna baƙin ciki. (Mai-Wa’azi 12:1-7) Wata Mashaidiya tsohuwa shafaffiya da take inda ake kula da waɗanda ba su da lafiya ta taɓa furta irin baƙin cikin nan da cewa: “Ba zan iya jira sai na mutu ba kafin in soma aiki.” Ga irin waɗannan tsofaffi, abin taimako ne idan mun fahimce su kuma muka ba su girma da ya dace. An umurci Isra’ilawa: “Za ka tashi tsaye a gaban mai-furfura, a bada girma ga fuskar dattijo.” (Leviticus 19:32) Ka ba da girma ga tsofaffi ta wurin nuna musu ana bukatarsu kuma ana sonsu. ‘Tashi tsaye’ zai haɗa da mu zauna mu saurari abin da suka cim ma a shekaru da suka gabata. Wannan zai girmama kuma ƙara kyautata rayuwarmu ta ruhaniya.
‘Wajen Ba da Girma Ka Yi Ja-gora’
15. Menene dattiɓai za su iya yi don su girmama waɗanda suke cikin ikklisiya?
15 Waɗanda suke cikin ikklisiya suna ci gaba sosai yayin da dattiɓai suka kafa musu misali mai kyau. (1 Bitrus 5:2, 3) Duk da yawan aikinsu, dattiɓai masu kula suna kusato matasa, magidanta, iyaye gwamraye, matan aure, da kuma tsofaffi, ko suna fuskantar matsaloli ko babu. Dattiɓai suna saurara ga abin da waɗanda suke cikin ikklisiya za su faɗa kuma suna yaba musu don abin da suka yi. Dattijo da yake lura kuma yake yaba wa abin da ɗan’uwa ko ’yar’uwa suke yi yana yin koyi da Jehovah, wanda yake nuna godiya ga halittunsa a duniya.
16. Me ya sa ya kamata mu girmama dattiɓai tare da sauran da suke cikin ikklisiya?
16 Ta yin koyi da Jehovah, dattiɓai suna kafa misali mai kyau a yin amfani da gargaɗin Bulus: “Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ’yan’uwa; kuna gabatarda juna cikin bangirma.” (Romawa 12:10) Wannan zai yi wa dattiɓai waɗanda suke ƙasashe inda nuna bambanci shi ne ƙa’idar wajen wuya. Alal misali, a wata ƙasa ta Gabas, kalmar nan “ɗan’uwa,” tana da ma’ana biyu, ɗaya domin waɗanda suke da girma ɗayan kuma domin talakawa. Har a baya bayan nan, waɗanda suke cikin ikklisiya suna kiran dattiɓai da waɗanda sun tsufa da irin wannan furci na ba da girma, suna yin amfani da furci don talakawa ga wasu. Amma, an ƙarfafa su su yi amfani da furci na talakawa a dukan lokatai, domin yadda Yesu ya gaya wa mabiyansa, “ku duka kuwa ’yan’uwa ne.” (Matta 23:8) Amma, mai yiwuwa wannan bambanci ba haka yake a wasu ƙasashe ba, muna bukata mu lura da halin ’yan Adam na nuna bambanci.—Yaƙub 2:4.
17. (a) Me ya sa ya kamata dattiɓai su kasance da sauƙi a guso wurinsu? (b) A waɗanne hanyoyi ne dattiɓai za su yi koyi da Jehovah a bi da waɗanda suke cikin ikklisiya?
17 Hakika, Bulus ya ƙarfafa mu mu ba wasu dattiɓai da suka cancanci “bangirma ninki biyu,” amma duk da haka ’yan’uwa ne. (1 Timothawus 5:17) Idan za mu iya mu “guso fa gaba gaɗi zuwa kursiyi na alheri” na Mai Mallakar Sararin Samaniya, bai kamata mu guso wajen dattiɓai, waɗanda ya kamata su yi koyi da Jehovah ba? (Ibraniyawa 4:16; Afisawa 5:1) Masu kula su lura da yadda suke da sauƙi a guso wajensu ta yin la’akari da yadda wasu suke zuwa wurinsu don su nemi shawara. Ka koya daga yadda Jehovah yake haɗa wasu cikin ayyukansa. Yana ba wasu daraja ta wurin ba su nawayoyi. Ko idan wasu shawarwari da wani Mashaidi ya bayar kamar ba ta da amfani, ya kamata dattiɓai su nuna godiya ga damuwa da suka nuna. Ka tuna da yadda Jehovah ya bi da tambayoyin Ibrahim na bincike da kukan Habakkuk na baƙin ciki.
18. Ta yaya dattiɓai za su yi koyi da Jehovah a gyara waɗanda suke bukatar taimako?
18 Wasu Kiristoci masu bi suna bukatar gyara. (Galatiyawa 6:1) Duk da haka, suna da daraja a gaban Jehovah, sun cancanta a ba su girma. Wani Mashaidi ya ce: “Idan mai ba da gargaɗi ya bi da ni da daraja, zan je wurinsa da sauƙi.” Yawancin mutane suna yin amfani da shawara idan an ba su girma. Mai yiwuwa zai ci lokaci, amma sauraron waɗanda suka yi kuskure zai sa ya yi sauƙi su amince da gargaɗi da suke bukata. Ka tuna da yadda Jehovah ya yi magana da Isra’ilawa cikin juyayi a kai a kai. (2 Labarbaru 36:15; Titus 3:2) Gargaɗi da aka bayar cikin juyayi da tausayi zai taɓa zuciyar waɗanda suke bukatar taimako.—Misalai 17:17; Filibbiyawa 2:2, 3; 1 Bitrus 3:8.
19. Yaya ya kamata mu ɗauki mutane da ba su gaskata ba yadda Kiristoci suka yi?
19 Ba wasu girma ya haɗa da waɗanda mai yiwuwa za su zama ’yan’uwanmu na ruhaniya a nan gaba. Irin waɗannan mutane ƙila za su yi jinkiri game da karɓan saƙonmu a yanzu, amma har ila ya kamata mu haƙura da su mu fahimci mutuncinsu na ’yan Adam. Jehovah “ba shi nufin kowa da halaka ba, amma duka su kai ga tuba.” (2 Bitrus 3:9) Bai kamata mu kasance da ra’ayin Jehovah ba? A yin la’akari da mutane, za mu samu hanyar ba da shaida idan muna da halin maƙwabtaka. Babu shakka, za mu guje wa tarraya da zai kawo haɗari na ruhaniya. (1 Korinthiyawa 15:33) Duk da haka muna nuna “nasiha,” ba tare da raina mutane da ba su gaskata ba yadda muka yi.—Ayukan Manzanni 27:3.
20. Menene ya kamata misalin Jehovah da Yesu Kristi su motsa mu mu yi?
20 Hakika, Jehovah da Yesu Kristi suna ɗaukan kowanne cikinmu da daraja. Bari mu ma mu tuna ko da yaushe yadda suka ba da daraja kuma mu yi ja-gora wajen ba ma juna girma. Kuma bari mu riƙa tunawa da kalmomin Ubangijinmu Yesu Kristi ko da yaushe: “Ku duka kuwa ’yan’uwa ne.”—Matta 23:8.
Yaya Za Ka Amsa?
• Yaya ya kamata ka ɗauki ’yan’uwa masu bi?
• Ta yaya misalin Jehovah da na Yesu ya motsa ka ka girmama wasu?
• Ta yaya magidanta da iyaye za su girmama wasu?
• Ɗaukan Kiristoci masu bi ’yan’uwansu, zai motsa dattiɓai su aikata a waɗanne hanyoyi?
[Hotuna a shafi na 14]
Ka ba matarka girma ta kalmomin godiya
Ku ga kwarjinin yaranku ta wurin sauraronsu
Bi da waɗanda suke cikin ikklisiya da mutunci