Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 7/1 p. 19
  • “Kun San Littafi Mai-Tsarki Ainun”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Kun San Littafi Mai-Tsarki Ainun”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za Ka Faranta Ran Malaminka
    Tambayoyin Matasa
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 7/1 p. 19

Rahoto Daga Masu Shelar Mulki

“Kun San Littafi Mai-Tsarki Ainun”

LOKACIN da Yesu yake da shekara 12 da yake magana da gaba gaɗi da shugabannen addini a Urushalima, “dukan waɗanda suka ji shi suka yi mamaki da fahiminsa da magana da ya ke mayarwa.” (Luka 2:47) Haka yake a yau, bayin Jehovah matasa da yawa suna ƙarfin zuciya su yi magana da malamansu da abokansu na makaranta game da Allah da Littafi Mai-Tsarki, sau da yawa kuwa suna ganin sakamako iri ɗaya na farin ciki.

Tiffany, ’yar shekara 14 cikin wani aji da ake tattauna zance game da annabcin Littafi Mai-Tsarki na makonni 70 na shekaru, da ke a Daniel 9:24-27. Malamin ya ɗan bayyana wasu ayoyi sai kuma bai iya karasa bayanin ba.

Da farko, Tiffany tana ɗan jinkiri wajen ɗaga hannunta. “Amma don wani abu,” in ji ta, “na damu saboda ba a bayyana ayoyin sosai ba. Ban san lokacin da na ɗaga hannuna sama ba.” Malamin ya yi mamakin cewa wani zai ƙara bayani a kan zancen, da yake yawancin ɗaliban sun iske shi da wuyan ganewa.

Da aka ba ta zarafin ta bayyana annabcin, Tiffany ta tashi tsaye ta yi magana sosai babu shiri. Da ta gama, duk cikin ajin aka yi tsit. Tiffany ta yi ɗan rawan jiki. Sai duk cikin ajin suka tafa mata sosai.

“Wannan ya yi kyau sosai, Tiffany, kin burge ni ƙwarai,” malamin ya yi ta maimaitawa sau da yawa. Yana cewa ya san akwai ƙarin bayani ga waɗannan ayoyi, amma Tiffany ce ta farko da ta fayyace masa su. Da suka tashi, ya tambayi Tiffany ta yaya ta san Littafi Mai-Tsarki sosai haka.

“Saboda ni Mashaidiyar Jehovah ce,” in ji ta. “Iyaye na sun bayyana mini wannan annabcin sau da yawa kafin na gane.”

Abokan ajinta ma suka yi mamakin sanin da take da shi na Littafi Mai-Tsarki. Wata ɗaliba ta ce wa Tiffany: “Yanzu na san abin da ya sa ku Shaidun Jehovah ku ke tafiya ƙofa zuwa ƙofa; saboda kun san Littafi Mai-Tsarki ainun.” Wasu suka yi alkawarin cewa ba za su sake yi mata ba’a domin imaninta ba.

Da Tiffany ta gaya wa iyayenta abin ya faru, suka ba ta shawara ta ba malaminta littafin nan Sanin Da Ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada. Da ta yi hakanan ta nuna wa malaminta wajen da ya bayyana annabcin Daniel, ya karɓi littafin nan da nan kuma ya gode mata.

Hakika, idan matasa Kiristoci suka yi magana da gaba gaɗi game da abin da iyayensu suka koya masu game da Allah da kuma Littafi Mai-Tsarki, suna kawo yabo da kuma daraja ga Jehovah da albarka wa kansu.—Matta 21:15, 16.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba