Ƙarin Bayani
a Bayan mutuwar C. T. Russell, aka shirya wani littafi da aka ce shi ne kundi na bakwai na jerin Studies in the Scriptures da ya yi ƙoƙarin ba da fassarar littattafan Ezekiel da Ru’ya ta Yohanna. Kundin, rabinsa furcin da Russell ya yi ne a kan waɗannan littattafan Littafi Mai-Tsarki. Amma, lokacin bayyana waɗancan annabce-annabce bai kai ba tukuna, kuma a gabaɗayanta, bayani da aka bayar cikin Studies in the Scriptures ɗin a zaurance ne. Da wucewar shekaru, alherin Jehovah da kuma aukuwa na duniya sun sa Kiristoci sun fahimci ma’anar waɗannan littattafai na annabci sarai.