28 ASA
Ya Bauta wa Jehobah Dukan Rayuwarsa
SARKI ASA ya yi mamaki da abin da ya gani. Ya ga sojojin Itiyofiya masu ɗumbun yawa a ƙasar Yahuda, suna a shirye su yi yaƙi. Sau da yawa Jehobah ya sa mutanensa su yi yaƙi da wasu alꞌummai, amma ba su taɓa yin yaƙi da sojoji masu yawa kamar wannan ba. Sojojin sun kai miliyan ɗaya. Amma sojojin Asa dubu ɗari shida ne kawai. Me zai taimaka masa ya kasance da ƙarfin zuciya kuma ya kāre mutanensa?
Wannan ba shi ne ƙaro na farko da Asa ya bukaci ya nuna ƙarfin zuciya ba. Shekaru goma kafin wannan lokacin saꞌad da Asa ya soma sarauta, ya nuna cewa yana da hali iri na kakan-kakansa Dauda. Kamar Dauda, ya bi shawarar da annabi Oded da ɗansa Azariya suka ba shi. Asa ya nuna ƙarfin zuciya ta wajen hana mutane yin munanan abubuwan da ake yi tun lokacin da Sarki Sulemanu ya daina bauta wa Jehobah. Alal misali, ya hallaka dukan gumakan da mutane suke bauta wa, kuma ya kori mazajen da suke karuwanci a wuraren ibada daga Yahuda.
Ƙari ga haka, Asa ya hana munanan abubuwan da ake yi a gidansu. Kakarsa Maꞌaka sarauniya ce a Yahuda. Ta ƙera wani gunki wataƙila don ta sa mutane su riƙa yin lalata a sunan bauta. Asa ya nuna cewa kasancewa da aminci ga Jehobah ne ya fi muhimmanci. Asa bai bar dangantaka da ke tsakaninsa da ꞌyan gidansu ta hana shi yin abin da ya dace ba. Ya cire kakarsa daga matsayinta, kuma ya cire gunkin da ta ƙera. Waɗannan abubuwan da Asa ya yi sun faranta wa Jehobah rai. Don haka, an yi shekaru goma ba a yi yaƙi a Yahuda ba. Amma yanzu dai, sojojin Itofiya sun zo su yaƙi Yahuda. Mene ne Jehobah ya yi?
Sojojin da suka zo yaƙan Sarki Asa su ne sojojin da suka fi yawa da aka ambata a Littafi Mai Tsarki
Da Asa ya ga yadda sojojin Itofiya suka cika koꞌina a kwarin Yahuda, nan da nan ya yi adduꞌa ga Jehobah. Ka yi tunanin yadda sojojinsa suka ji saꞌad da ya yi adduꞌa ya ce: “Ya Yahweh, babu mai taimako kamarka, wanda zai taimaki marar ƙarfi a kan masu ƙarfi. Ka taimake mu, ya Yahweh Allahnmu, gama muna dogara a gare ka! Ya Yahweh, a cikin Sunanka muka zo domin mu fuskanci rundunar dubban sojojin nan. Ya Yahweh, kai ne Allahnmu! Kada ka bar wani mutum ya sha ƙarfinka.” Babu shakka, wannan adduꞌar da ya yi ta sa Jehobah farin ciki. Asa ya nuna ƙarfin zuciya kamar Jonatan ɗan Sarki Shawulu. Su biyun sun san cewa idan Jehobah yana tare da su, za su yi nasara a kan maƙiyansu kome yawansu. (1 Sam. 14:6) Babu shakka, duk wanda Jehobah yake tare da shi ne zai yi nasara!
Me ya faru saꞌad da Asa da mutanensa suka je yaƙin? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yahweh ne da sojojinsa suka halaka su.” Babu ko ɗayansu da ya tsira.
Bayan haka, Asa ya ƙarfafa mutanen su ci-gaba da bauta wa Jehobah. Mutane da yawa daga ƙabilu goma na arewacin Israꞌila sun ƙaura zuwa Yahuda don su riƙa bauta wa Jehobah a haikalin da ke Urushalima. Asa ya sa mutanen Yahuda su yi alkawari cewa za su ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci.
Amma Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa, Asa ya yi kurakurai masu tsanani. A lokacin da sarkin Israꞌila yake so ya zo ya yaƙi mutanen Yahuda, Asa bai nemi taimakon Jehobah ba. A maimakon haka, ya ba wa sarkin Suriya cin hanci don ya zo ya yaƙi sarkin Israꞌila. Kuma saꞌad da Jehobah ya tura wani annabi mai suna Hanani zuwa wurin Sarki Asa, ya yi fushi sosai kuma ya sa aka jefa annabin cikin kurkuku. Saꞌad da Asa ya tsufa, ya yi rashin lafiya sosai. Amma maimakon ya nemi taimakon Jehobah, ya nemi wasu hanyoyin samun lafiya. Akwai alama cewa Asa bai ci-gaba da riƙe amincinsa ga Jehobah ba.
Amma Jehobah mai yawan jinƙai ne. A dukan shekaru 41 da Asa ya yi yana sarauta, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Asa ya miƙa zuciyarsa gaba ɗaya ga Yahweh dukan kwanakinsa.” Labarin Asa ya nuna cewa, Jehobah yana ƙaunar masu ƙaunar sa. Kuma ya koya mana cewa kada mu taɓa manta da abin da Jehobah ya yi mana. Yin tunani a kan waɗannan abubuwan za su sa mu ƙara kasancewa da bangaskiya da kuma ƙarfin zuciya!
Ka karanta labarin a:
1 Sarakuna 15:8-24
2 Tarihi 14:1–16:14
Mene ne raꞌayinka?
A waɗanne hanyoyi ne Asa ya nuna ƙarfin zuciya?
Ka Yi Bincike Sosai
1. Mene ne “gunkin ban ƙyamar nan na Ashera,” kuma ta yaya abubuwan da aka tono suka nuna cewa wasu Israꞌilawa marasa aminci sun bauta wa allahiyar da gunkin yake wakilta? (1 Sar. 15:12, 13; w08 7/1 16 sakin layi na 1-5) Ka duba hoto na 1
Hoto na 1: Asa ya cire kakarsa daga babban matsayinta kuma ya hallaka gunkin ban ƙyamar nan na Ashera da take bauta wa
Hoto na 1: Asa ya cire kakarsa daga babban matsayinta kuma ya hallaka gunkin ban ƙyamar nan na Ashera da take bauta wa
2. Waye ne ɗan Hanani, kuma ta yaya ya yi koyi da irin ƙarfin zuciya da mahaifinsa ya nuna? (it “Hanani” Na 2-wcgr)
3. Ko da yake Asa ya yi kurakurai, me ya yi da ya nuna cewa “ya miƙa zuciyarsa gaba ɗaya ga Yahweh”? (1 Sar. 15:14; w17.03 19 sakin layi na 5-6)
4. Shin Sarki Asa ya kawar da dukan “wuraren sujada da ba su dace ba”? (2 Tar. 14:2-5; 15:17; w05 12/1 30 sakin layi na 2)
Ka Yi Tunani a kan Darussan
Yadda annabi Azariya ya ƙarfafa Asa ya sa Asa ya taimaka wa dukan mutanen Yahuda su soma bauta wa Jehobah a hanyar da ta dace. Ta yaya kai ma za ka iya ƙarfafa mutane? Ka duba hoto na 2
Hoto na 2
Asa ya dogara ga Jehobah don ya taimaka masa ya yi nasara a kan sojoji masu yawa sosai, amma ya nemi taimakon ꞌyanꞌadam lokacin da sojojin da ba su da yawa suka kawo masa hari. Mene ne hakan ya koya mana game da muhimmancin dogara ga Jehobah a dukan fannonin rayuwarmu? (K. Mag. 3:5, 6)
Ta yaya za ka yi koyi da irin ƙarfin zuciya da Asa ya nuna?
Ka Ƙara Yin Tunani Sosai
Mene ne labarin nan ya koya mini game da Jehobah?
Ta yaya abin da ya faru a labarin nan ya jitu da nufin Jehobah?
Mene ne zan so in tambayi Asa idan muka haɗu a aljanna?
Ƙarin Darussa
Idan kana zama a ƙasa inda kana da ꞌyancin yin waꞌazi da kuma ayyukan ibada, ta yaya za ka yi koyi da Asa kuma ka yi amfani da wannan ꞌyancin da kyau? Ka karanta talifin nan don ka ga amsar.
“Ka Yi Amfani da Zarafin da Kake da Shi Yanzu” (w20.09 14-19)
Ka karanta talifin nan don ka ga yadda labarin Asa zai taimaka maka a lokacin da kake bukatar ka yi abin da Jehobah yake so.