27 MEFIBOSHET
Bai Yi Fushi Ba Saꞌad da Aka Yi Masa Rashin Adalci
MEFIBOSHET jiƙan Shawulu Sarkin Israꞌila ne, kuma shi ɗan Jonatan mutumin da ya bauta wa Jehobah da ƙarfin zuciya ne. Amma saꞌad da ya kai shekara biyar, rayuwarsa ta canja gabaki ɗaya. Kakansa Shawulu ya ji rauni a yaƙi kuma ya kashe kansa. Babansa Jonatan ma ya mutu a yaƙin. Saꞌad da matar da take kula da Mefiboshet ta ji abin da ya faru da Shawulu da Jonatan, ta ɗauke shi ta kama gudu don tana tsoro kada wasu su zo su kashe shi. Saꞌad da take guduwa, Mefiboshet ya faɗi daga hannunta kuma ya ji rauni sosai a ƙafarsa. Hakan ya sa ya zama gurgu duk rayuwarsa.
Mefiboshet bai yi fushi ba duk da cewa rayuwa ba ta yi masa sauƙi ba. Ya yi godiya don abin da yake da shi. Ya zauna da wani Baꞌisraꞌile mai suna Makir. Ana nan, sai Sarki Dauda ya tuna cewa ya yi wa abokinsa Jonatan alkawarin kula da membobin iyalinsa. (1 Sam. 20:14-17) Sai Dauda ya aika a kira masa Mefiboshet.
Mefiboshet ya ji tsoron zuwa wurin Dauda. Shi daga zuriyar mugun Sarki Shawulu ne. Wataƙila ya ɗauka cewa Dauda yana so ya kashe shi ne. Duk da haka, ya yi biyayya kuma ya je wurin Sarki Dauda. Dauda ya yi masa magana da alheri kuma ya mayar masa da dukiyar kakansa Shawulu. Sai ya ce masa: “Za ka dinga cin abinci tare da ni.” Mefiboshet ya yi wa Sarki Dauda godiya sosai duk da cewa yana ganin bai cancanta ba. Ya tambayi sarkin abin da ya sa zai kula da shi duk da cewa ba shi da muhimmanci. Har ma ya ce bai fi karen da ya riga ya mutu daraja ba!
Mefiboshet ɗan yaro ne saꞌad da ya zama gurgu kuma ya rasa iyayensa. Daga baya, an ci amanarsa kuma an yi masa rashin adalci
Daga baya, Mefiboshet ya sake fuskantar matsaloli. Absalom ɗan Dauda yana so ya kashe Dauda domin ya zama sarki kuma mutane da yawa sun goyi bayansa. Hakan ya sa Dauda ya gudu ya bar Urushalima. Bawan Mefiboshet, wato Ziba ya je ya goyi bayan Dauda amma ya bar Mefiboshet a Urushalima. Duk da cewa Mefiboshet bai samu ya bi su ba, ya nuna cewa ya riƙe amincinsa, kuma ya damu da abin da ya faru da Dauda. Bai aske gashin bakinsa da gemunsa ba domin a alꞌadarsu haka mutumin da yake makoki yake yi. Bayan da Dauda ya yi nasara a kan Absalom, ya dawo Urushalima. Amma Dauda bai ji daɗin abin da Mefiboshet ya yi ba. Me ya sa?
A lokacin da Ziba ya je ya taimaka wa Dauda, ya yi masa ƙarya game da Mefiboshet. Ya gaya wa Dauda cewa Mefiboshet ya zauna a Urushalima ne domin shi ma yana so ya zama sarki. Ka yi tunanin yadda Dauda zai ji. Bai daɗe da ɗansa ya so ya ƙwace mulki a hanunsa ba. Ban da haka ma, Ahitofel mai ba shi shawara ya ci amanarsa. Mai yiwuwa shi ya sa ya yarda cewa Mefiboshet ma zai iya cin amanarsa. Dauda ya ba da doka cewa duk abin da yake na Mefiboshet ya zama na Ziba.
Saꞌad da Mefiboshet ya ji cewa Ziba ya yi wa Dauda ƙarya game da shi, ya so ya haɗu da Dauda don ya bayyana masa abin da ya faru. Dauda ya tambayi Mefiboshet dalilin da ya sa bai bi shi lokacin da ya bar Urushalima ba. Sai Mefiboshet ya tuna masa cewa shi gurgu ne kuma Ziba ya tafi ya bar shi. Mai yiwuwa Dauda ya lura cewa Mefiboshet yana baƙin ciki shi ya sa bai gyara gashin bakinsa da gemunsa ba. Hakan ya nuna cewa Mefiboshet bai yi ƙoƙarin zama sarki saꞌad da Dauda ya gudu ba. Duk da haka, Dauda ya yi fushi sosai, kuma bai so ya ji bayanin da Mefiboshet yake yi ba. Sai ya mayar wa Mefiboshet wasu gādonsa, kuma ya ce Mefiboshet da Ziba su raba gādon.
Shin, Mefiboshet ya yi fushi ne domin zai raba gādonsa tare da bawansa da ya yi ƙarya a kansa? Aꞌa! (M. Sha. 19:18, 19) Ko da yake an ci amanarsa, bai yi fushi ko ya yi sanyin gwiwa ba. Ya kasance da ƙarfin zuciya domin ya fi mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci, wato gafarta wa mutane da kuma zaman lafiya da su.
Abin da ya gaya wa Dauda ya nuna cewa shi mai sauƙin kai ne sosai. Ya ce: “A ma bar wa Ziba duka. Tun da ka dawo lafiya, wannan ma ya ishe ni!” Mefiboshet ya damu sosai da sarkin da Jehobah ya zaɓa. Ko da yake an yi ƙarya a kansa kuma an ƙwace dukiyarsa, ya ci-gaba da yin farin ciki da kuma bauta wa Jehobah da aminci. Duk da cewa Mefiboshet bai taɓa yin yaƙi a matsayin soja ba, ya nuna ƙarfin zuciya fiye da sojoji da yawa!
Ka karanta labarin a:
2 Samaꞌila 4:4; 9:1-13; 16:1-4; 19:24-30
Mene ne raꞌayinka?
A waɗanne hanyoyi ne Mefiboshet ya nuna ƙarfin zuciya?
Ka Yi Bincike Sosai
1. Kafin Mefiboshet ya je wurin Dauda, ya zauna a “gidan Makir.” Mene ne kuma ya nuna cewa Makir mutum ne mai aminci da kuma karimci? (2 Sam. 9:3, 4; it “Makir” Na 2-wcgr)
2. Me ya sa Mefiboshet ya kwatanta kansa da “mataccen kare”? (2 Sam. 9:8; it “Kare” sakin layi na 5-wcgr) Ka duba hoto na 1
PhotoStock-Israel/Photodisc via Getty Images
Hoto na 1: A Israꞌila a dā ana ganin karnuka a matsayin dabbobi masu ƙazanta da ke cin mushe da bola
3. Mene ne muka sani game da Mefiboshet da ya nuna cewa ba zai so ya zama sarki a maimakon Dauda ba? (w02 3/1 4 sakin layi na 11, da ƙarin bayani) Ka duba hoto na 2
Hoto na 2: Mai yiwuwa Jonatan ya gaya wa Mefiboshet mutumin da Jehobah ya zaɓa ya zama sarki
4. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya albarkaci Mefiboshet bayan abubuwan da suka faru da shi? (w22.03 13 sakin layi na 4-5)
Ka Yi Tunani a kan Darussan
Mutane da yawa suna fama da ciwon tsananin damuwa ko kuma wasu matsaloli dabam da mai yiwuwa ꞌyanꞌuwa ba za su gama ganewa ba. Waɗanne darussa ne za su iya koya daga labarin Mefiboshet da za su iya ƙarfafa su?
Saꞌad da Dauda ya ji zance daga gefe ɗaya, ya ba ma wani dukiyar Mefiboshet. Me ya sa muke bukatar mu bincika batu da kyau kafin mu yanke shawara? Ka duba hoto na 3
Hoto na 3
Ta yaya za ka yi koyi da irin ƙarfin zuciya da Mefiboshet ya nuna?
Ka Ƙara Yin Tunani Sosai
Mene ne labarin nan ya koya mini game da Jehobah?
Ta yaya abin da ya faru a labarin nan ya jitu da nufin Jehobah?
Mene ne zan so in tambayi Mefiboshet idan muka haɗu a aljanna?
Ƙarin Darussa
Ka kalli bidiyon nan don ka ga yadda za mu yi koyi da Mefiboshet idan muna ganin kamar an yi mana rashin adalci.
Yadda Suka Nemi Salama Kuma Suka Same Ta—Mephibosheth (3:25)
Idan yaro yana ganin kamar wasu ba sa son shi, ta yaya iyaye za su yi amfani da labarin Mefiboshet don su taimaka masa? Ka karanta talifin nan don ka ga amsar.
“Shin, Ka Taɓa Ji Kamar Ka Kaɗaita Duk da Cewa Akwai Mutane Tare da Kai?” (w11 6/1 26-27-wcgr)