RATAYE
Yesu Kristi—Almasihu da Aka Yi Alkawarinsa
DOMIN a taimake mu mu gane Almasihu, Jehobah Allah ya huri annabawan Littafi Mai Tsarki da yawa su ba da bayani game da haihuwa, hidima, da kuma mutuwar wannan Mai Ceto. Dukan waɗannan annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki sun cika a kan Yesu Kristi. Abin ban sha’awa, daidai suke a bayaninsu. Alal misali, bari mu bincika wasu annabce-annabce da suka faɗi abubuwa da suka shafi haihuwa da kuma yaranta na Almasihu.
Annabi Ishaya ya annabta cewa Almasihu zai fito daga zuriyar Sarki Dauda. (Ishaya 9:7) Kuma hakika an haifi Yesu daga zuriyar Dauda.—Matta 1:1, 6-17.
Miƙah wani annabin Allah, ya annabta cewa wannan ɗan zai zama sarki a ƙarshe kuma ya ce za a haife shi a “Bai’talahmi Ephrathah.” (Miƙah 5:2) Sa’ad da aka haifi Yesu, akwai garuruwa biyu a Isra’ila da ake kira Bai’talahmi. Ɗaya tana kusa da Nazarat a yankin arewaci na ƙasar, ɗayar kuma tana kusa da Urushalima ta Yahuda. Bai’talahmi da ke kusa da Urushalima a dā ana kiranta Ephrathah. An haifi Yesu a wannan garin, daidai yadda aka ce a annabcin!—Matta 2:1.
Wani annabci na Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa Allah zai kira ɗansa daga “Masar.” An ɗauki Yesu zuwa Masar. An mai da shi bayan mutuwar Herod, da haka ya cika annabcin.—Hosea 11:1; Matta 2:15.
A taswira da ke shafi na 200, nassosi da aka jere a ƙarƙashin “Annabci” suna ɗauke da bayani dalla-dalla game da Almasihun. Don Allah ka gwada da nassosi da aka jera a ƙarƙashin “Cika.” Yin haka zai sake ƙarfafa bangaskiyarka game da gaskiyar Kalmar Allah.
Sa’ad da kake bincika waɗannan nassosin, ka tuna cewa waɗannan annabci ne da aka rubuta su shekaru ɗarurruwa kafin a haifi Yesu. Yesu ya ce: “Dukan abin da aka rubuta a kaina a cikin Attaurat ta Musa, da Annabawa, da Zabura, dole a cika su.” (Luka 24:44) Kamar yadda za ka gani a cikin naka Littafi Mai Tsarki, hakika sun cika!