Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • bh p. 199-p. 201 par. 4
  • Yesu Kristi—Almasihu da Aka Yi Alkawarinsa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yesu Kristi—Almasihu da Aka Yi Alkawarinsa
  • Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Makamantan Littattafai
  • Annabce-annabce Game da Almasihu Sun Nuna Cewa Yesu Ne Almasihu Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Annabci Game da Almasihu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Sun Jira Zuwan Almasihu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Sun Samu Almasihu!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
bh p. 199-p. 201 par. 4

RATAYE

Yesu Kristi—Almasihu da Aka Yi Alkawarinsa

DOMIN a taimake mu mu gane Almasihu, Jehobah Allah ya huri annabawan Littafi Mai Tsarki da yawa su ba da bayani game da haihuwa, hidima, da kuma mutuwar wannan Mai Ceto. Dukan waɗannan annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki sun cika a kan Yesu Kristi. Abin ban sha’awa, daidai suke a bayaninsu. Alal misali, bari mu bincika wasu annabce-annabce da suka faɗi abubuwa da suka shafi haihuwa da kuma yaranta na Almasihu.

Annabi Ishaya ya annabta cewa Almasihu zai fito daga zuriyar Sarki Dauda. (Ishaya 9:7) Kuma hakika an haifi Yesu daga zuriyar Dauda.—Matta 1:1, 6-17.

Miƙah wani annabin Allah, ya annabta cewa wannan ɗan zai zama sarki a ƙarshe kuma ya ce za a haife shi a “Bai’talahmi Ephrathah.” (Miƙah 5:2) Sa’ad da aka haifi Yesu, akwai garuruwa biyu a Isra’ila da ake kira Bai’talahmi. Ɗaya tana kusa da Nazarat a yankin arewaci na ƙasar, ɗayar kuma tana kusa da Urushalima ta Yahuda. Bai’talahmi da ke kusa da Urushalima a dā ana kiranta Ephrathah. An haifi Yesu a wannan garin, daidai yadda aka ce a annabcin!—Matta 2:1.

Wani annabci na Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa Allah zai kira ɗansa daga “Masar.” An ɗauki Yesu zuwa Masar. An mai da shi bayan mutuwar Herod, da haka ya cika annabcin.—Hosea 11:1; Matta 2:15.

A taswira da ke shafi na 200, nassosi da aka jere a ƙarƙashin “Annabci” suna ɗauke da bayani dalla-dalla game da Almasihun. Don Allah ka gwada da nassosi da aka jera a ƙarƙashin “Cika.” Yin haka zai sake ƙarfafa bangaskiyarka game da gaskiyar Kalmar Allah.

Sa’ad da kake bincika waɗannan nassosin, ka tuna cewa waɗannan annabci ne da aka rubuta su shekaru ɗarurruwa kafin a haifi Yesu. Yesu ya ce: “Dukan abin da aka rubuta a kaina a cikin Attaurat ta Musa, da Annabawa, da Zabura, dole a cika su.” (Luka 24:44) Kamar yadda za ka gani a cikin naka Littafi Mai Tsarki, hakika sun cika!

 

ANNABCE-ANNABCE GAME DA ALMASIHU

AUKUWA

ANNABCI

CIKA

Haifa a zuriyar Yahuda

Farawa 49:10

Luka 3:23-33

Budurwa za ta haife shi Ishaya 7:14

Matta 1:18-25

Daga zuriyar Sarki Dauda

Ishaya 9:7

Matta 1:1, 6-17

Jehobah ya furta cewa Ɗansa ne

Zabura 2:7

Matta 3:17

Ba a gaskata shi ba

Ishaya 53:1

Yohanna 12:37, 38

Ya shiga Urushalima a kan jaki

Zechariah 9:9

Matta 21:1-9

Abokinsa na kusa ya ci amanarsa

Zabura 41:9

Yohanna 13:18, 21-30

An ci amanarsa domin zinariya 30

Zachariah 11:12

Matta 26:14-16

Ya yi shiru a gaban masu zarginsa

Ishaya 53:7

Matta 27:11-14

An jefa ƙuri’a domin tufafinsa

Zabura 22:18

Matta 27:35

An zazzage shi a kan gungume

Zabura 22:7, 8

Matta 27:39-43

Ba a fasa ƙasusuwansa ko ɗaya ba

Zabura 34:20

Yohanna 19:33, 36

An binne shi da masu arziki

Ishaya 53:9

Matta 27:57-60

An ta da shi kafin ya ruɓe

Zabura 16:10

Ayukan Manzanni 2:24, 27

Yana tsaye dama ga Allah

Zabura 110:1

Ayukan Manzanni 7:56

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba