Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • nwt pp. 471-475
  • A3 Yadda Muka Samu Littafi Mai Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • A3 Yadda Muka Samu Littafi Mai Tsarki
  • Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MASU KWAFE-KWAFE SUN ADANA KALMAR ALLAH
  • SANIN NASSOSIN IBRANANCI DA NA GIRKANCI DA ZA A YI AMFANI DA SU DON FASSARA
  • An Canja Ko Kuma Sake Sakon Littafi Mai Sarki Ne?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • An Kasa Canja Sakon da Ke Cikin Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
A3 Yadda Muka Samu Littafi Mai Tsarki

A3

Yadda Muka Samu Littafi Mai Tsarki

Wanda aka rubuta saƙonsa a cikin Littafi Mai Tsarki, da wanda ta wurinsa muka same shi ne ya kāre Littafi Mai Tsarki har zuwa yau. Shi ne Wanda ya sa aka rubuta wannan furucin cewa:

“Kalmar Jehobah takan dawwama har abada.” —1 Bitrus 1:25.

Wannan furucin gaskiya ne, duk da cewa babu rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na asali a Ibrananci da yaren Aramaika da kuma yaren Girka da muke da su a yau. Saboda haka, ta yaya za mu tabbata cewa abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki a yau daidai ne da saƙon da Allah ya sa aka rubuta?

MASU KWAFE-KWAFE SUN ADANA KALMAR ALLAH

Dalilin da ya sa har wa yau muna da Nassosin Ibrananci kuma sun yi daidai da saƙon da Allah ya sa a rubuta shi ne umurnin da Allah ya bayar cewa a riƙa kwafan Nassosi.b Alal misali, Jehobah ya umurci kowane sarkin Israꞌila ya sa a kwafa masa littafin Doka. (Maimaitawar Shariꞌa 17:18) Ƙari ga haka, Allah ya sa Lawiyawa su riƙa adana Dokar kuma su koya wa mutane Dokar. (Maimaitawar Shariꞌa 31:26; Nehemiya 8:7) Bayan da Yahudawa suka dawo daga bauta a Babila, an samu wani rukunin mutane da suke kwafan Nassosi da ake kiran su marubuta (ko kuma Sofarim). (Ezra 7:6) Da shigewar lokaci, marubutan sun yi kwafi da yawa na littattafai 39 da ke Nassosin Ibrananci.

Wani dalilin da ya sa ake bukatar a kwafa rubuce-rubuce na asali shi ne don an rubuta su a kan abubuwa da suke lalacewa.

Marubutan sun yi shekaru suna kwafan waɗannan littattafan da kyau. A shekara ta 500-1500, wani rukunin marubuta Yahudawa da ake kiran Masorete sun ci-gaba da wannan aikin. Cikakken rubuce-rubucen Masorete da suka fi daɗewa su ne Leningrad Codex, waɗanda aka rubuta daga shekara ta 1008 ko kuma 1009 bayan haifuwar Yesu. Amma a tsakiyar ƙarni na ashirin, an gano ƙananan rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki ɗari biyu da ashirin a cikin naɗaɗɗun littattafai da aka samo kusa da Tekun Gishiri. Waɗannan ƙananan rubuce-rubucen sun fi Leningrad Codex daɗewa fiye da shekara dubu ɗaya. Saꞌad da aka gwada naɗaɗɗun littattafai da aka samo kusa da Tekun Gishiri da Leningrad Codex, an tabbatar da wani batu mai muhimmanci: Ko da yake kalmomin da suke cikin naɗaɗɗun littattafai da aka samo kusa da Tekun Gishiri sun ɗan bambanta da na Leningrad Codex, hakan bai shafi saƙon da ke cikinsu ba.

Littattafai ashirin da bakwai na Nassosin Girkanci na Krista kuma fa? Wasu manzannin Yesu Kristi, da kuma kaɗan daga cikin almajiransa na farko ne suka rubuta asalin littattafan. Kristocin ƙarni na farko sun bi alꞌadar marubuta Yahudawa a yadda suka kwafa littattafan. (Kolosiyawa 4:16) Duk da cewa Sarkin Roma mai suna Diocletian tare da wasu sun yi ƙoƙari su hallaka dukan littattafan Kristoci na farko, an adana dubban ƙananan littattafan Littafi Mai Tsarki na dā har zuwa yau.

An fassara rubuce-rubucen Kristoci zuwa wasu yaruka. Da farko an fassara Littafi Mai Tsarki zuwa yaruka da suka daɗe sosai kamar yaren Armeniya, da yaren Kibdawa, da yaren Ethiopik, da yaren Georgiya, da yaren Latin, da kuma yaren Syriak.

SANIN NASSOSIN IBRANANCI DA NA GIRKANCI DA ZA A YI AMFANI DA SU DON FASSARA

Ba dukan kwafi na rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki ne suke ɗauke da kalmomi iri ɗaya ba. Ta yaya za mu iya sanin abin da ke cikin nassi na asali?

Za a iya kwatanta yanayin da wani malami da ya ce wa ɗalibansa guda ɗari su kwafa babin wani littafi. Ko da babi na asalin ya ɓata daga baya, idan aka gwada kwafi guda ɗarin, za a iya sanin abin da ke cikinsa. Ko da yake kowane ɗalibi zai iya yin kurakurai, ba zai yiwu dukan ɗaliban su yi kurakurai iri ɗaya ba. Haka ma, saꞌad da masana suka gwada dubban ƙananan rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki da kuma kwafi dabam-dabam na littattafan Littafi Mai Tsarki, za su iya gane kuskuren da masu kwafa suka yi kuma su gano kalmomi da aka yi amfani da su a cikin nassi na asali.

“Za mu iya faɗa cewa babu wani littafi na dā da aka kwafa daidai kamar sa.”

Ta yaya za mu iya kasance da tabbaci cewa saƙon da ke Littafi Mai Tsarki na yanzu ya yi daidai da saƙon da ke Littafi Mai Tsarki na asali? Da yake magana a kan Nassosin Ibrananci, wani masani mai suna William H. Green ya ce: “Za mu iya faɗa cewa babu wani littafi na dā da aka kwafa daidai kamar sa.” Haka ma yake da Nassosin Girkanci na Krista ko kuma Sabon Alkawari. Wani masani mai suna F. F. Bruce ya rubuta cewa: “Abubuwan da suka nuna cewa abin da aka rubuta a cikin Sabon Alkawari daidai ne suna da yawa fiye da na littattafan dā waɗanda sanannun mutane ne suka rubuta, duk da cewa babu wanda ya ƙaryata abubuwan da sanannun mutanen suka rubuta.” Ya kuma ƙara da cewa: “Da a ce Sabon Alkawari ba ya cikin Littafi Mai Tsarki, kuma wasu sanannun mutane ne suka rubuta shi, da yawancin mutane za su ce tabbas abin da suka rubuta gaskiya ne.”

Nassosin Ibrananci da ke naɗaɗɗun littattafai da aka samo kusa da Tekun Gishiri

Sura 40 ta littafin Ishaya da ke cikin naɗaɗɗun littattafai da aka samo kusa da Tekun Gishiri (daga shekara ta 125 zuwa 100 kafin haifuwar Yesu)

Saꞌad da aka gwada shi da rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na Ibrananci waɗanda aka rubuta wajen shekaru dubu ɗaya bayan sa, bambancin da aka gano kaɗan ne kawai, yawancinsu ma yadda aka rubuta kalmomin ne

Nassosin Ibrananci da ke Aleppo Codex

Sura 40 ta littafin Ishaya da ke Aleppo Codex. Wannan rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki mai muhimmanci ne, wanda Yahudawa da ake kira Masorete suka rubuta a wajen shekara ta 930 bayan haifuwar Yesu

Nassosin Ibrananci: An yi amfani da Biblia Hebraica, na Rudolf Kittel, saꞌad da ake fassara juyin Fassarar Sabuwar Duniya na Nassosin Ibrananci (1953-1960) na Turanci. Tun daga lokacin, an sake samun wasu juyin Nassosin Ibrananci, wato Biblia Hebraica Stuttgartensia da kuma Biblia Hebraica Quinta, kuma suna ɗauke da bincike da aka yi kwana-kwanan nan daga naɗaɗɗun littattafai da aka samo kusa da Tekun Gishiri da kuma wasu rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā. Wannan aikin da masana suka yi ne ya sa aka sake fitar da littafin Leningrad Codex, kuma a littafin akwai ƙarin bayanai da ke ɗauke da wasu makamantun kalmomi daga wasu littattafai kamar su Samaritan Pentateuch, da naɗaɗɗun littattafai da aka samo kusa da Tekun Gishiri, da Septuagint na yaren Girka, da Targum na yaren Aramaik, da Vulgate na yaren Latin, da kuma Peshitta na yaren Syriak. An bincika Biblia Hebraica Stuttgartensia da Biblia Hebraica Quinta saꞌad da ake shirin sake juyin Fassarar Sabuwar Duniya na Turanci.

Nassosin Girkanci: A ƙarshen ƙarni na goma sha tara, wasu masana masu suna B. F. Westcott da F.J.A. Hort sun gwada rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki da ake da su a lokacin da kuma wasu ƙananan rubuce-rubuce yayin da suke shirya Littafi Mai Tsarki na yaren Girka da za a yi amfani da shi wajen fassara, kuma sun yi imanin cewa littafin ya yi kama sosai da nassosi na asali. A tsakiyar ƙarni na ashirin, Kwamitin Juyin Fassarar Sabuwar Duniya ya yi amfani da littafin yayin da yake fassara. Kwamitin ya kuma yi amfani da rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki da aka yi a kan takardar da ake yi da ciyawa (wato papyrus). Kuma an yi imani cewa tun daga ƙarni na biyu zuwa ƙarni na uku ne aka yi rubutun. Tun daga lokacin, an samu ƙarin rubuce-rubucen da aka yi a kan takardar ciyawa (wato papyrus). Akwai kuma wasu Littafi Mai Tsarki na yaren Girka da ake amfani da su a yi fassara, kamar waɗanda Nestle da Aland da kuma United Bible Societies suka fitar. Littattafan suna ɗauke da bincike na kwana-kwanan nan da masana suka yi. An yi amfani da wasu daga cikin sakamakon bincike da suka yi yayin da ake fassara wannan juyin.

Bisa ga littattafan nan da ake amfani da su a yi fassara, an gano cewa wasu ayoyi da ke Nassosin Girkanci na Krista a wasu juyin Littafi Mai Tsarki kamar King James Version, ba sa cikin asalin saƙon Allah, amma ƙari ne da masu kwafan nassosi suka yi daga baya. A juyin Littafi Mai Tsarki da yawa, ba a fassara ayoyi nan ba. Ayoyin su ne Matiyu 17:21; 18:11; 23:14; Markus 7:16; 9:44, 46; 11:26; 15:28; Luka 17:36; 23:17; Yohanna 5:4; Ayyukan Manzanni 8:37; 15:34; 24:7; 28:29; da Romawa 16:24. A wannan juyin, an nuna cewa an cire ayoyin ta wurin saka ƙarin bayani a wurin da aka cire ayoyin.

Game da doguwar kammalawa da ke Markus 16 (ayoyi 9-20), da gajeriyar kammalawa da ke Markus 16, da kuma kalmomin da suke Yohanna 7:53–8:11, a bayyane yake cewa ba sa cikin asalin rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki. Don haka, waɗannan ƙari da aka yi da ba su dace ba, ba sa cikin wannan juyin.

An yi ma wasu kalmomi gyare-gyare don su yi daidai da kalmomin da masana suka amince cewa su ne suka yi kama da waɗanda suke cikin asalin rubuce-rubuce na Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ga yadda Matiyu 7:13 take a wasu rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki: “Ku shiga ta ƙaramar ƙofa, domin ƙofar zuwa hallaka na da girma kuma hanyarta na da fāɗi.” Ba a saka kalmar nan “ƙofar” a Fassarar Sabuwar Duniya na dā a Turanci ba. Amma bayan an ƙara bincika rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki, an ga tabbaci cewa “ƙofar” na cikin Littafi Mai Tsarki na asali. Don haka, an saka kalmar a wannan juyin. Akwai wasu kalmomi kamar haka da aka yi musu gyara. Amma waɗannan ƙananan gyare-gyare ne, kuma babu wani a cikinsu da ya canja ainihin saƙon da ke Kalmar Allah.

Rubutun Littafi Mai Tsarki a kan takardar ciyawa (wato papyrus)

Wani rubutun 2 Korintiyawa 4:13–5:4 da aka yi a kan takardar ciyawa (wato papyrus) daga wajen shekara ta 200 bayan haifuwar Yesu

a Daga wannan wurin, za a riƙa kiran sa Nassosin Ibrananci.

b Daga wannan wurin, za a riƙa kiran sa Nassosin Ibrananci.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba