A5
Sunan Allah a Cikin Nassosin Girkanci na Krista
Masanan Littafi Mai Tsarki sun amince cewa sunan Allah da aka rubuta da baƙaƙen nan huɗu (יהוה), ya bayyana kusan sau 7,000 a cikin rubutun Nassosin Ibrananci na asali. Amma da yawa a cikinsu suna ganin babu sunan nan a cikin rubutun Nassosin Girkanci na Krista na asali. Saboda haka, yawancin Littafi Mai Tsarki da ake fassara zuwa Turanci a yau ba sa ɗauke da sunan nan Jehobah a cikin Sabon Alkawari. Ko saꞌad da suke fassara ayoyin da aka ɗauko su kai tsaye daga Nassosin Ibrananci da ke ɗauke da sunan Allah, yawancin mafassara suna amfani da “Ubangiji” a maimakon sunan Allah.
Amma juyin Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya bai bi wannan salon ba. Ya yi amfani da sunan nan Jehobah sau ɗari biyu da talatin da bakwai (237) a cikin Nassosin Girkanci na Krista. Mafassaran wannan Littafi Mai Tsarki sun tsai da wannan shawarar ce domin dalilai biyu masu muhimmanci: (1) Nassosin Girkanci da muke da su a yau ba na asali ba ne. Akwai dubban Nassosin Girkanci a yau, kuma yawancinsu an sake rubuta su ne aƙalla shekaru ɗari biyu bayan an rubuta na asalin. (2) A lokacin, waɗanda suka sake rubuta nassosin nan sun sauya sunan Allah da aka rubuta da baƙaƙen nan huɗu da kalmar Girkancin nan Kyʹri·os, wanda ke nufin “Ubangiji,” ko kuma sun kwafa daga littattafan da aka riga aka sauya sunan Allah a cikinsu.
Kwamitin Juyin Fassarar Sabuwar Duniya yana da hujjoji masu kyau da suka nuna cewa sunan Allah ya bayyana a cikin Nassosin Girkanci na asali. An tsai da shawarar yin amfani da sunan Allah don dalilai na gaba:
Nassosin Ibrananci da aka yi amfani da su a zamanin Yesu da manzanninsa sun ƙunshi sunan Allah (wato sunan Allah da aka rubuta da baƙaƙe huɗun nan na Ibrananci יהוה) daga farko har zuwa ƙarshe. A dā, wasu mutane ba su yarda da hakan ba. Amma yanzu da aka gano Nassosin Ibrananci da aka rubuta a ƙarni na farko a yankin Kwumran, hakan ya ba da tabbaci cewa nassosin suna ɗauke da sunan Allah.
A zamanin Yesu da kuma na manzanninsa, Nassosin Ibrananci da aka fassara zuwa Girkanci suna ɗauke da sunan Allah. Da daɗewa, masana sun ɗauka cewa baƙaƙe huɗu da ke wakiltar sunan Allah ba sa cikin Greek Septuagint, wato, Nassosin Ibrananci da aka fassara zuwa Girkanci. A tsakanin shekara ta 1940 da 1950, masanan Littafi Mai Tsarki sun yi nazarin wasu tsofaffin sassan juyin Girkanci na Septuagint da aka yi amfani da su a zamanin Yesu. Waɗannan sassan suna ɗauke da sunan Allah da aka rubuta da harufan Ibrananci. Saboda haka, mun san cewa a zamanin Yesu, Nassosi a yaren Girka suna ɗauke da sunan Allah. Amma a tsakanin shekara ta ɗari uku zuwa ɗari huɗu bayan haifuwar Yesu, wasu sanannun Nassosi a yaren Girka kamar su Codex Vaticanus da Codex Sinaiticus, ba su ƙunshi sunan Allah a littafin Farawa zuwa Malakai ba (duk da cewa sunan nan yana cikin littattafai na dā). Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa babu sunan Allah a cikin Sabon Alkawari ko kuma Nassosin Girkanci da aka adana daga wancan lokacin zuwa yau.
Yesu ya bayyana dalla-dalla cewa: “Na zo a cikin sunan Ubana.” Ya kuma nanata cewa cikin ‘sunan Ubansa’ ne yake yin ayyukansa
Nassosin Girkanci na Krista ma sun nuna cewa Yesu ya yi amfani da sunan Allah sosai kuma ya koya ma wasu. (Yohanna 17:6, 11, 12, 26) Yesu ya bayyana dalla-dalla cewa: “Na zo a cikin sunan Ubana.” Ya kuma nanata cewa cikin ‘sunan Ubansa’ ne yake yin ayyukansa.—Yohanna 5:43; 10:25.
Tun da yake Jehobah ne ya ja-goranci marubutan Nassosin Girkanci na Krista da kuma Nassosin Ibrananci, ɓacewar sunansa daga Nassosin Girkanci zai sa Nassosi biyun su yi dabam. Wajen shekara ta hamsin bayan haifuwar Yesu, almajiri Yaƙub ya gaya wa dattawa da ke Urushalima cewa: “Simeyon ya ba da labari dalla-dalla yadda Allah a karo na farko, ya mai da hankalinsa ga mutanen alꞌummai don ya zaɓa daga cikinsu mutane don sunansa.” (Ayyukan Manzanni 15:14) Ba yadda Yaƙub zai yi wannan furucin idan babu wanda ya san sunan Allah ko yake amfani da sunan a lokacin.
Nassosin Girkanci na Krista suna ɗauke da taƙaitaccen sunan Allah. A littafin Ruꞌuya ta Yohanna 19:1, 3, 4, 6, kalmar nan “Halleluyah” ta ƙunshi sunan Allah. Kalmar nan daga furucin Ibrananci ne da ke nufin “Ku yabi Jah.” Saboda haka, an ɗauko kalmar nan “Jah” daga sunan nan Jehobah. Sunaye da yawa a cikin Nassosin Girkanci na Krista sun ƙunshi sunan Allah. Alal misali, wasu littattafan bincike sun nuna cewa sunan Yesu yana nufin “Jehobah Ne Ceto.”
Littattafan Yahudawa na dā sun nuna cewa Kristoci Yahudawa sun yi amfani da sunan Allah a rubuce-rubucensu. Wani littafin dokokin Yahudawa da ake kira Tosefta da aka kammala rubutun sa wajen shekara ta ɗari uku bayan haifuwar Yesu, ya yi bayani a kan littattafan Kristoci da ꞌyan hamayya suka ƙona a Ranar Assabaci. Ya ce: “Suna ƙona dukan littattafan marubutan Linjila (Matiyu zuwa Yohanna) da kuma littattafan ꞌyan minim [sunan da ake kiran Yahudawa da suka zama Kristoci]. Sun ƙona littattafan ƙurmus, har da wuraren da ke ɗauke da sunan Allah.” Littafin ya yi ƙaulin wani Malamin Yahudawa mai suna Yosé, wanda mutumin Galili ne kuma ya yi rayuwa a ƙarni na biyu, yana cewa a sauran ranakun, “ana yanke wuraren da ke ɗauke da sunan Allah [wato, rubuce-rubucen Kristoci] kuma a adana su, saꞌan nan a ƙona sauran littattafan.”
Wasu masanan Littafi Mai Tsarki sun ce da alama akwai sunan Allah a wuraren da aka yi ƙaulin Nassosin Ibrananci a cikin Nassosin Girkanci na Krista. Wannan ƙamus The Anchor Bible Dictionary a ƙarƙashin jigon nan “Tetragrammaton in the New Testament,” (wato Baƙaƙe Huɗu a Cikin Sabon Alkawari) ya ce: “Akwai tabbaci cewa a lokacin da aka rubuta Sabon Alkawari, sunan Allah, wato Yahweh, ya bayyana a cikin wasu ko kuma dukan wuraren da aka yi ƙaulin Tsohon Alkawari.” Wani masani mai suna George Howard ya ce: “Tun da yake an rubuta baƙaƙe huɗu masu wakiltar sunan Allah a cikin Nassosi a yaren Girka, [wato Septuagint] wanda shi ne fassarar da Kristoci na farko suka yi amfani da shi, zai dace a amince cewa asalin marubutan Sabon Alkawari ba su cire sunan Allah a duk lokacin da suka yi ƙaulin Tsohon Alkawari ba.”
Sanannun mafassaran Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da sunan Allah a Nassosin Girkanci na Krista. Wasu daga cikinsu sun yi hakan da daɗewa kafin a buga Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya. Ga sunayen mafassaran da kuma littattafan da suka fassara: Herman Heinfetter (1863), mafassarin A Literal Translation of the New Testament . . . From the Text of the Vatican Manuscript; da Benjamin Wilson (1864), mafassarin The Emphatic Diaglott; da George Barker Stevens (1898), mafassarin The Epistles of Paul in Modern English; da W. G. Rutherford (1900), mafassarin St. Paul’s Epistle to the Romans; da kuma J.W.C. Wand, Bishop na Landan (1946), mafassarin The New Testament Letters. Ƙari ga haka, Pablo Besson, mafassarin wani Littafi Mai Tsarki a Sifanisanci a shekara ta 1919, ya yi amfani da “Jehová” a Luka 2:15 da Yahuda aya ta 14 da kuma fiye da sau ɗari a ƙarin bayanai a fassararsa. Ya faɗa cewa wataƙila yadda ya kamata a rubuta sunan Allah ke nan. Da daɗewa kafin a yi waɗannan fassarar, Nassosin Girkanci na Krista da aka fassara zuwa Ibrananci daga ƙarni na goma sha shida suna ɗauke da sunan Allah a wurare da yawa. A Jamusanci kaɗai, akwai fassarar Nassosin Girkanci na Krista guda goma sha ɗaya da ke ɗauke da “Jehovah” (ko kuma “Yahweh”) saꞌan nan mafassara huɗu sun rubuta sunan a cikin baƙa biyu a gaban wuraren da aka rubuta “Ubangiji.” Akwai sunan Allah a ƙarin bayanai a cikin fassarar Jamusanci sama da sabaꞌin.
Sunan Allah a Ayyukan Manzanni 2:34 a fassarar The Emphatic Diaglott, na Benjamin Wilson (1864)
Akwai sunan Allah a Nassosin Girkanci na Krista da aka fassara a yaruka sama da ɗari uku. Yaruka da yawa a nahiyar Afirka, da Amirka, da Asiya, da Turai, da kuma tsibirin Fasifik suna amfani da sunan Allah sosai. (Ka duba jerin yaruka a shafuffuka na 482 da 483.) Mafassaran Littafi Mai Tsarki a waɗannan yarukan sun yi amfani da sunan Allah ne saboda dalilai irin waɗanda aka ambata a baya. Wasu daga cikin waɗannan fassaran Nassosin Girkanci na Krista da aka yi kwanan nan su ne, Rotuman Bible (1999), wanda aka yi amfani da “Jihova” sau hamsin da ɗaya a ayoyi arbaꞌin da takwas da kuma fassarar yaren Batak (Toba) na ƙasar Indonesiya (1989), wanda aka yi amfani da “Jahowa” sau ɗari da goma.
Sunan Allah a Markus 12:29, 30 a wata fassarar yaren Hawaii
Hakika, mun ga cewa akwai hujjoji masu kyau na maido da sunan Allah, wato Jehobah, a cikin Nassosin Girkanci na Krista. Shi ya sa mafassaran Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya suka yi hakan. Sun daraja sunan Allah sosai, shi ya sa suka guji cire duk abin da ke cikin rubutun Littafi Mai Tsarki na asali.—Ruꞌuya ta Yohanna 22:18, 19.