Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwyp talifi na 81
  • In Ba na Jin Annashuwa Fa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • In Ba na Jin Annashuwa Fa?
  • Tambayoyin Matasa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da ya kamata ka sani
  • Abin da za ka iya yi
  • Me Zan Yi In Dana Ya Gaji da Zama Ba Abin Yi?
    Taimako don Iyali
Tambayoyin Matasa
ijwyp talifi na 81
Matashi yana da na’ura iri iri, amma kuma ya kwanta a gado yana kallon silin kawai

TAMBAYOYIN MATASA

In Ba Na Jin Annashuwa Fa?

Ba abin da wasu mutane suka tsana kamar a ce ruwan sama ya tsare mutum a gida, ya hana ka fita, ba abin yi kuma ba wurin zuwa. “Wani matashi mai suna Robert ya ce: “A irin wannan yanayin, zan zauna kawai, in rasa abin da zan yi da rai na.”

Ka taba samun kanka a irin wannan yanayin? Idan haka ne, wannan talifin zai taimaka maka!

  • Abin da ya kamata ka sani

  • Abin da za ka iya yi

  • Abin da tsararku suka ce

Abin da ya kamata ka sani

  • Yin amfani da na’urar zamani ba zai taimaka maka ba.

    Yin amfani da intane zai iya taimaka maka ka dan kashe lokaci, amma kuma zai iya gurgunta zurfi tunaninka ya kuma kara maka rashin jin annashuwa. Jeremy, mai shekara 21 ya ce: “Za ka ga cewa kana kallon na’urar amma kuma hankalinka ba ya wurin.”

    Wata budurwa mai suna Elena ta yarda da hakan. Ta ce, “Ba dukan abubuwa ba ne za ka iya yi da na’ura. Zai janye hankalinka daga abubuwa masu muhimmanci, da zarar ka ajiye na’urar, za ka fi jin rashin annashuwa!”

  • Hali shine mutum.

    Shin yawan abubuwan yi zai sa ka ji annishuwa ne? Kome ya dangana ga yadda ka ke sha’awar abin da ka ke yi. Alal misali, wata budurwa mai suna Karen ta tuna kuma ta ce: “Ba na jin dadin makaranta, ko da yake ina da abubuwan yi a makaranta. Dole ne mutum ya shaku a abin da yake yi in ba haka ba ba za ka ji annashuwa ba.”

Ka sani? “Rashin abin yi” ba hujja ba ce amma wani zarafi ne​—yanayin yana kama da kasa mai inganci da mutum zai iya yin shuki.

Tukunya mai shuki da ya nuna garaya da alkalami da takarda da faranti na mai zane na tsira daga cikinta

Lokacin da ka ke da shi yana kamar kasa mai inganci da mutum zai iya yin shuki.

Abin da za ka iya yi

Ka kara yawan abubuwan da za ka so ka dinga yi. Ka nemi sabon abokai. Ka soma yin wani abin da za ka ji dadinsa. Ka yi bincike akan wasu sababbin batutuwa. Mutanen da ke yawan yin abubuwa dabam dabam ba za su ji rashin annishuwa ba yayinda su ke nan su kadai​—ko kuma suke tare da wasu!

Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Dukan abin da hannunka ya iske na yi, ka yi shi da karfinka”​—Mai Wa’azi 9:​10.

Wata mai suna Melinda ta ce: “Bai dade da na fara koyon yaren Mandarin na kasar Sin ba, kuma yayinda nake zuwa wurin koyo, na gano cewa lallai fa abubuwa masu kyau sun wuce ni domin ban soma koyon tuntuni ba. Ina jin dadin samun akin yi. Domin yana sa in mai da hankali na a abin da na ke yi kuma in yi amfani da lokaci na yadda ya kamata.”

Ka mai da hankali ga manufarka. Za ka dada sa kuzari cikin abin da ka ke yi idan ka ga cewa abin da ka ke yi yana da amfani. Ba za ka ji kyuyar yin aikin makaranta ba idan ka san manufarsa.

Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Babu abin da ya fi ga mutum . . . ya ji wa ransa dadi cikin aikinsa.”​—Mai-Wa’azi 2:24.

Hannah ta ce: “Lokacin da na kusa kamala makaranta, ina karatun tsawon sa’o’i takwas domin dā ma ban yi wani karatu ba. Na ji kyuyan yin haka ne? Ko kadan domin na sa zuciya na in cim ma buri na. Na mai da hankali akan abin da zan cim ma, wato sauke karatu, kuma hakan ya motsa ni sosai.”

Ka yi na’am da abubuwan da ba za ka iya canjawa ba. Ba kome ne za ka ji dadin yi cikin abubuwan da ka ke son yi ba. Ko abokanka na kud da kud ma za su iya kin yin wasu abubuwa da kai, kuma hakan zai sa ka rasa na yi. Ka yi kokari ka kasance da hali mai kyau maimakon barin irin wadannan abubuwa su raunana ka.

Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Mai farin zuciya yana da buki tuttur.”​—Karin Magana 15:15.

Ivy ta ce: “Abokiyata ta ce mini in yi kokari in mori lokaci da nake zama ni kadai. Ta ce mini ya kamata in koyi yadda zan iya jin dadin zama ni kadai da kuma sa’ad da nake tare da wasu, domin wannan hali ne mai kyau da ya kamata kowa ya koya.”

Abin da tsaranku suka ce

Hannah

Hannah ta ce: “Dā na kan ji kishin mutanen da nake ganin kamar suna jin dadin rayuwa. Sai na gano cewa su mutane ne kamar kowa da ke yin abubuwa. Sai ni ma na soma yin abubuwa. Sai na fara wasu ayuka da nake jin dadinsu kuma na soma yin bincike akan batutuwa masu ban sha’awa. Yayinda ka ke kara zurfin iliminka na duniya, abubuwa da yawa za su soma burge ka, kuma za ka soma jin annashuwa.”

Caleb

Caleb ya ce: “A lokacin da nake matashi, ina yin wasan bidiyo domin in magance halin rashin jin annishuwa. Yayinda na kara shekaru, na ga cewa wasan bidiyo zaman kashe wando ne kawai. Zai dauka lokacinka, amma bayan da ka gama ba za ka ga ribanta ba. Yanzu ina abubuwa masu amfani da lokaci na.”

Micaela

Micaela ta ce: “Dā na kan ji rashin annishuwa kuma ina ganin kamar lokaci ba ya tafiya, amma daga baya na zo na gane cewa idan ina son mutane su yi hira da ni, dole ne ni ma in zama abokin hira. Na soma yin haka, kuma hakan ya taimaka min sosai. Yanzu dai, ina jin dadin lokacin da nake ‘zama ni kadai’, domin yanzu da kyar na ke samun irin wannan lokacin!”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba