Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwhf talifi na 1
  • Yadda Za Ka Kame Kanka Idan Ka Yi Fushi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Ka Kame Kanka Idan Ka Yi Fushi
  • Taimako don Iyali
  • Ƙananan Jigo
  • Abin da ya kamata ka sani
  • Abin da za ka iya yi
Taimako don Iyali
ijwhf talifi na 1
Wata mata tana fushi cewa tana wanke-wanke mijinta kuma yana kallon talabijin

TAIMAKO DON IYALI

Yadda Za Ka Kame Kanka Idan Ka Yi Fushi

Mijinki ko matarka ta yi abin da ya bata maka rai, amma ka yi kokarin boye bacin ranka. Sai matarka ta gano cewa da akwai abin da ke damunka kuma ta soma tambayar ka. Hakan ya dada bata maka rai. Ta yaya za ka kame kanka a irin wannan yanayin?

  • Abin da ya kamata ka sani

  • Abin da za ka iya yi

Abin da ya kamata ka sani

  • Yin fushi yana iya cutar da kai. Masu bincike sun gano cewa idan mutum yana yawan yin fushi hakan yana iya jawo hawan jini ko ciwon zuciya ko yawan bakin ciki ko kuma ciwon ciki. Kari ga haka, yawan fushi yana iya sa rashin barci da alhini da cuta a fatar jiki da kuma bugun jini. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce “Kada ka yi fushi, wannan ba ya kawo kome sai mugunta.”—Zabura 37:8.

  • Boye bacin rai yana iya yi maka lahani. Idan ka ci gaba da yin fushi, hakan yana iya zama kamar wata cuta da ke jawo maka lahani a cikin jiki. Alal misali, kana iya zama mai yawan kushe mutane. Zama da mutum mai irin wannan halin yana da wuya sosai kuma zai iya jawo matsala a aurenka.

Abin da za ka iya yi

  • Ki mai da hankali ga halaye masu kyau na mijinki ko matarka. Ki lissafa halaye uku masu kyau na mijinki ko matarka da kake so. Idan mijinki ko matarka ta yi abin da ya bata maka rai ka tuna da halayenta uku da kake so da ka lissafa. Yin hakan yana iya taimaka maka ka kame kanka kuma ka guji yin fushi.

    Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ku kuma kasance masu godiya.”—Kolosiyawa 3:15.

    Wata mata da ta shagala da ayyuka tana tunanin yadda mijinta yake taimaka mata da aikace-aikace a gida, da yadda yake sauraranta da kuma yadda yake kula da ita idan tana rashin lafiya
  • Ka zama mai gafartawa. Da farko, ka yi kokarin fahimtar matarka ko mijinki. Yin hakan zai taimaka maka ka soma nuna tausayi. (1 Bitrus 3:8) Bayan haka, ka tambayi kanka ‘Abin da aka yi mini yana da muni sosai ne da ba zan iya gafartawa ba?’

    Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kyale laifin da aka yi . . . abu ne mai kawo . . . daraja.”—Karin Magana 19:11.

  • Ka fadi abin da ke zuciyarka a hanyar da ta dace kuma da basira. Ka yi amfani da kalmar nan “Ni.” Alal misali, maimakon ki ce, “A ganina ba ka damu da ni ba, domin ba ka kira ka gaya mini wurin da kake,” zai fi dacewa ki ce, “Ina damuwa sosai idan dare ya yi kuma ban san ko lafiyar ka ba.” Fadin abin da ke zuciyarka a cikin kwanciyar hankali zai iya sa ka kame kanka.

    Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “A koyaushe, bari maganarku ta kasance da alheri da kuma dadin ji.”—Kolosiyawa 4:6.

  • Ka saurara da kyau. Bayan ka fadi abin da ke zuciyarka, ka bar matarka ko mijinki ya yi magana ba tare da katse masa magana ba. Bayan haka, ki maimaita abin da ya fada don ki tabbatar kin fahimce shi da kyau. Saurara da kyau zai iya taimaka maka ka kame kanka.

    Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kowa ya kasance mai saurin ji, amma ba mai saurin magana ba.”—Yakub 1:19.

Tim da Jennifer

Wata ’yar’uwa mai suna Jennifer ta ce: “Idan ka boye abin da ke damunka, matsalar za ta ci gaba, a karshe hakan zai sa ka fushi sosai. Zai fi dacewa ka tattauna abin da ke damunka da matarka ko mijinki. Bayan ni da mijina mun tattauna matsalarmu, sai mu ce ‘Bar mu sake karfafa abutarmu.’”​—Jennifer da mijinta Tim.

Jade da Corey

Wata ’yar’uwa mai suna Jade ta ce game da mijinta Corey: “Abin da nake so da mijina shi ne yana saurarana da kyau kuma yana amincewa da abin da ke damuna. Ko da bai amince da ra’ayina ba, yana kokarin ya fahimce ni. Ba ya sa na ji kamar ban san abin da nake yi ba don yadda nake ji.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba