Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwyp talifi na 76
  • Me Ya Sa Kake Bukatar Ka Rika Halartar Taro a Majami’ar Mulki?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Kake Bukatar Ka Rika Halartar Taro a Majami’ar Mulki?
  • Tambayoyin Matasa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Me ake yi a Majami’ar Mulki?
  • Me ya sa kake bukatar ka rika Halarta?
  • Ta Yaya Za Ka Amfana Daga Taron Shaidun Jehobah?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Wannan Wurin Ne Muke Bauta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Me Ya Sa Ya Kamata Mu Rika Halartan Taro don Ibada?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Karfafa Masu Son Sakonmu Su Halarci Taro
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
Dubi Ƙari
Tambayoyin Matasa
ijwyp talifi na 76
Wani matashi na kallon mutane sa’ad da suke shiga Majami’ar Mulki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Ya Sa Kake Bukatar Ka Rika Halartar Taro a Majami’ar Mulki?

Shaidun Jehobah suna halartar taro so biyu kowane mako a wurin ibadarsu da ake kira Majami’ar Mulki. Me ake yi a wurin, kuma ta yaya za ka amfana idan ka halarta?

  • Me ake yi a Majami’ar Mulki?

  • Me ya sa kake bukatar ka rika Halarta?

  • Abin da tsararka suka ce

Me ake yi a Majami’ar Mulki?

Majami’ar Mulki wuri ne da ake koyar da abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki da za su amfane mu a rayuwarmu. Taron da ake yi a wurin zai iya taimaka maka:

  • Ka koyi gaskiya game da Allah

  • Ka san dalilin da ya sa abubuwa suke faruwa a yau

  • Ka zama mutumin kirki

  • Ka sami abokai nagari.

Ka sani? Ana kiran wurin taron Shaidun Jehobah Majami’ar Mulki domin Mulkin Allah ne ake tattaunawa a wurin.—Matiyu 6:9, 10; 24:14; Luka 4:43.

Me ya sa kake bukatar ka rika Halarta?

Abin da za ka koya zai taimaka maka. Ka’idodin Littafi Mai Tsarki da ake tattaunawa a taron Shaidun Jehobah zai taimaka maka ka zama mai ‘hikima.’ (Misalai 4:5) Hakan yana nufin cewa Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka rika tsai da shawarwari masu kyau a rayuwa. Kari ga haka, zai taimaka maka ka sami amsoshin wadannan tambayoyin:

  • Mene ne ma’anar rayuwa?

  • Allah ne yake jawo wahalar da muke sha?

  • Me yake faruwa bayan mun mutu?

Ga kadan cikin wasu jawaban da ake yi a taronmu na karshen mako:

  • Ka Sa Littafi Mai Tsarki Ya Yi Maka Ja-gora

  • A Ina Ne Za Ka Sami Taimako a Lokacin Wahala?

  • Abin da Mulkin Allah Yake Yi Mana a Yanzu

Brenda ta ce: “Wani dan ajinmu ya halarci taronmu. Ya zauna tare da iyalinmu, kuma ya yi amfani da littattafanmu. Bayan haka, sai ya gaya mini cewa kalaman da mutane ke bayarwa lokacin da ake tattaunawa sun kayatar da shi. Ya kuma ce a cocinsu ba su da abubuwan nazarin Littafi Mai Tsarki kamar yadda muke da su.”

Ka sani? Ba a biyan kudi don wurin zama a Majami’ar Mulki kuma ba a karban baiko.

Tarayyar da kake yi a wurin zai karfafa ka. Littafi Mai Tsarki ya ce dalilin da ya sa Kiristoci suke bukatar su rika taro shi ne domin “karfafa wa juna zuciya.” (Ibraniyawa 10:24,25) Yin tarayya da mutanen da suke kaunar Allah da mutane na kawo kwanciyar hankali a wannan duniya da mutane suke son kansu kawai.

Elisa ta ce: “Harkokin yau da kullum sukan gajiyar da ni kuma su sa ni bakin ciki, amma mutanen da ke Majami’ar Mulki sukan kwantar mini da hankali. Ina koma gida da farin ciki kuma ina shirye in fuskanci matsalolina.”

Ka sani? Akwai ikilisiyoyin Shaidun Jehobah fiye da 120,000 a fadin duniya da suke yin taro a wurare fiye da 60,000. A kowace shekara, ana gina Majami’un Mulki kusan 1,500 domin masu halartan taro na dada karuwa.a

Abin da tsararka suka ce

Jessica

Jessica ta ce: “A lokacin da nake makarantar sakandare, ’yar ajinmu ta halarci wasu taronmu, kuma ta ji dadin yadda manya da kanana suke koyan abubuwa daga Littafi Mai Tsarki tare. A kwanan nan, shugaba na a wurin aiki ma ya halarta, kuma ya yi mamakin yadda muke yawan amfani da Littafi Mai Tsarki. Ganin yadda ya ji dadin taronmu ya karfafa ni.”

Timothy

Timothy ya ce: “Halartan taro yana taimaka mini na daina tunani game da abubuwan yau da kullum. A taron, muna koyan yadda za mu yi rayuwa mai gamsarwa da yadda za mu zama mutanen kirki da dai sauransu. Kullum na kan bar majami’ar Mulki cike da farin ciki da kuma karfafa da na samu.”

Jacob

Jacob ya ce: “Wani mutumin da na gayyata zuwa taro ya ce: ‘Na zo ne domin in karyata imaninku. Amma sai na ga cewa imanina ne ba daidai ba!’ Fara’ar da Shaidun Jehobah suka nuna masa ya burge shi sosai. Ya ce: ‘Ko da yake haduwarmu na farko ke nan, kun dauke ni kamar mun dade da sanin juna!’”

Madison

Madison ta ce: “Akwai lokutan da nake ganin cewa, ‘da zarar an gama taro zan tafi.’ Amma idan aka soma taron, sai tunanin nan ya bace. Bayan taron, ina hira da mutane kuma ba na iya tuna dalilin da ya sa nake son bari taron da farko. Da ba na zuwa taro, da ba ni da abokan kirki da nake da su a yau.”

a Don ka bincika wajen taro, ka je shafin “Taron Ikilisiya na Shaidun Jehobah” a wannan shafin sai ka bude “Ka Nemi Wurin da Ke Kusa da Kai”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba