Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 128
  • Shin an Ambaci Kalmar nan Purgatory a Littafi Mai Tsarki?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shin an Ambaci Kalmar nan Purgatory a Littafi Mai Tsarki?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 128
Hoton da ya bayyana ma’anar purgarory

An Ambaci Kalmar nan Purgatory (Gidan Azaba) a Littafi Mai Tsarki?

Amsar Littafi Mai Tsarki

A’a. Babu kalmar nan “purgatory” a Littafi Mai Tsarki kuma Kalmar Allah ba ta koyar da cewa za a tsarkake kurwar wadanda suka mutu a purgatory ba.a Ka yi la’akari da abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da zunubi da mutuwa da kuma yadda hakan ya karyata koyarwar purgatory.

  • Bangaskiya ga hadayar fansar Yesu ce ke tsabtace mutum, ba wata rayuwa a purgatory ba. Littafi Mai Tsarki ya ce “jinin Yesu Dansa [dan Allah] yana tsarkake mu kuma daga zunubi duka” kuma ya kara da cewa ‘Yesu Kristi . . . ya kwance mu daga zunubanmu cikin jininsa.’ (1 Yohanna1:7; Ru’ya ta Yohanna 1:5) Yesu “ya ba da ransa kuma abin fansar mutane da yawa.” ​—Matta 20:28.

  • Matattu ba su san kome ba. “Gama masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san kome ba.” (Mai-Wa’azi 9:5) Wanda ya mutu ba ya iya sani ko jin kome, don haka, wutar purgatory ba za ta iya tsarkake shi ba.

  • Allah ba ya horar da mutum don zunubin da ya yi kafin ya mutu. Littafi Mai Tsarki ya ce “hakkin zunubi mutuwa ne” ya kuma ce “wanda ya mutu ya kubuta daga zunubi.” (Romawa 6:7, 23) Mutuwa ce kadai sakamakon zunubin da mutum ya yi.

Mece ce koyarwar purgatory?

Bisa ga koyarwar Katolika, purgatory yanayi ne, ko wuri, ko kuma inda ake tsarkake kurwar mutanen da suka mutu don gafarar zunuban da ba a yafe musu ba. bBisa ga koyarwar Catechism of the Catholic Church, ana bukatar wannan tsarkakewar “don mutum ya zama wanda ya cancanta zuwa sama.” Littafin Catechism ya dada cewa “bisa ga al’adar Cocin . . . an yi magana game da tsabtacewa ta wuta,” kamar yadda aka nuna a hoton da yake wannan talifin. Amma wannan ba koyarwar Littafi Mai Tsarki ba ce.

A ina aka samo koyarwar purgatory?

Helenawa na dā sun yi imani da koyarwar Limbo da na purgatory. Clement na birnin Alexandria wanda ya bi ra’ayin falsafar Hellenanci ya yi da’awa cewa, ana iya tsarkake matattu daga zunubi a wuta. Ban da haka ma, a littafin nan The History of Christian Doctrines, Paparoma Gregory na Daya ya ce ba wanda ya isa ya karyata koyarwar wutar purgatory. A wannan binciken, an dada da cewa shi Gregory, wanda shi ne paparoma daga shekara ta 590 zuwa 604 bayan haihuwar Yesu “ne suke ganin ya ‘kirkiro koyarwar purgatory.’” A taron da aka yi na councils of Lyons (1274) da na Florence (1439) ne Cocin Katolika ta ce ta yarda da koyarwar purgatory kuma ta sāke tabbatar da hakan a taron Council of Trent a shekara ta 1546.

a Littafin nan Orpheus: A General History of Religions ya bayyana ma’anar purgatory cewa, “babu wani abu da ya goyi bayan wannan ra’ayin a Linjila.” Hakan nan ma littafin nan the New Catholic Encyclopedia ya ce: “A bincike na karshe da aka yi, an gano cewa koyarwar nan ta Katolika game da purgatory ba ta cikin Littafi Mai Tsarki, amma bisa ga al’ada take.”​—Bugu na Biyu, Littafi na 11, shafi na 825

b Duba littafin nan New Catholic Encyclopedia, Bugu na Biyu, Littafi na 11, shafi na 824.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba