Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwyp talifi na 64
  • Zai Dace In Yi Abota da Mutane Dabam-dabam?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Zai Dace In Yi Abota da Mutane Dabam-dabam?
  • Tambayoyin Matasa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Matsalar yin abokai da wasu irin mutane kawai
  • Abin da za ka iya yi
  • Ka Zabi Abokan Kirki
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ta Yaya Ne Za Mu Iya Zaɓan Abokan Kirki?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Yi Abokantaka da Masu Kaunar Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Tambayoyin Matasa
ijwyp talifi na 64
’Yammata suna daukan hoton kansu

TAMBAYOYIN MATASA

Zai Dace In Yi Abota da Mutane Dabam-dabam?

Wani matashi mai suna Alan ya ce: “Ina son abokaina sosai, saboda haka, yana min wuya in yi abota da mutanen da ban san su ba.”

Wata mai suna Sara ta ce: “Abokaina kadan ne kuma ba na so in dada wasu da ban saba da su ba.”

Ra’ayinka daya ne da na Alan da Sara? Kana da abokai da kake jin dadin tarayya da su kuma ba ka son ka yi abota da wasu dabam?

Idan haka ne, za ka koyi wani abu daga wannan talifin!

  • Matsalar yin abokai da wasu irin mutane kawai

  • Abin da za ka iya yi

  • Abin da tsararka suka ce

Matsalar yin abokai da wasu irin mutane kawai

Yin abokai da mutanen da ka fi sabawa da su ba laifi ba ne. Irin wadannan abokan za su iya sa ka kasance da gaba gadi, don ka san cewa sun amince da kai sosai.

Wata ‘yar shekara 19 mai suna Karen ta ce: “Idan mutum yana da abokai da suke sonsa, zai so ya rika kasancewa tare da su kawai. Kuma idan mutum yana girma, zai so abokansa su amince da shi.”

Ka sani? Yesu yana da abokai da yawa hade da manzanninsa 12, amma a cikin wadannan manzannin Bitrus da Yakub da kuma Yohanna ne suka fi kusa da shi.​—Markus 9:2; Luka 8:51.

Amma, yin abokantaka da mutane iri daya kawai zai iya jawo wa mutum matsala. Alal misali:

  • Zai iya hana ka samun abokan kirki.

    Wani dan shekara 21 mai suna Evan ya ce: “Idan tsararka ne kawai abokanka, hakan zai iya hana ka yin abokantaka da wasu da za ka iya koyan abubuwa masu kyau daga wurinsu.”

  • Mutane za su iya ganin kamar kai mai girman kai ne.

    Wata ‘yar shekara 17 mai suna Sara ta ce: “Idan kana tarayya da mutane iri daya kawai, sauran mutane za su ga kamar ba ka son ka yi magana da su ne.”

  • Zai iya sa ka zama mai cin zalin mutane.

    Wani dan shekara 17 mai suna James ya ce: “Mai yiwuwa kai ba ka cin zalin wasu, amma idan abokanka suna yin hakan, a hankali za ka soma dauka cewa yin hakan ba laifi ba ne ko ma ya zama maka abin dariya.”

  • Zai iya jawo maka matsala, musamman ma idan kana so sai lalle-lalle ka yi abokantaka da wasu matasa.

    Wata ‘yar shekara 17 mai suna Martina ta ce: “Idan mutum daya a cikin abokanku bai da hankali, hakan zai iya shafan sauran wadanda kuke abokantaka da su.”

Abin da za ka iya yi

  • Ka bincika abin da ka fi darajawa.

    Ka tambayi kanka: ‘Ka’idodin wa nake bi a rayuwata? Abokaina suna taimaka mini in rika bin wadannan ka’idodin? Shin zan ci gaba da yin tarayya da su ko da hakan zai sa ni in yi abubuwa marar kyau?’

    Ka’idar Littafi Mai Tsarki: ‘Zama da miyagu takan bata halayen kirki.’​—1 Korintiyawa 15:33.

    Wata ‘yar shekara 14 mai suna Ellen ta ce: “Idan kana abokantaka da mutanen da ba sa bin ka’idodi iri daya da kai, hakan zai iya sa ka ka soma yin abubuwan da ba ka tsammani za ka yi ba.”

  • Ka bincika abin da yake da muhimmanci a gare ka.

    Ka tambayi kanka: ‘Dangantakata da abokaina tana da karfi sosai da har za ta sa ni in yi abin da bai da kyau don kawai mu ci gaba da tarayyarmu? Me zan yi idan wani abokina ya yi abin da bai da kyau?’

    Ka’idar Littafi Mai Tsarki: ‘Wadanda nake kauna, ina tsauta musu.’​—Ru’ya ta Yohanna 3:19.

    Wata ‘yar shekara 22 mai suna Melanie ta ce: “Idan wani a cikin abokanka ya yi abin da bai da kyau, ba za ka so ka kai kararsa ba domin ba ka so wani abu ya faru da shi.”

  • Ka kulla abota da mutane dabam-dabam.

    Ka tambayi kanka: ‘Zai dace in yi abokantaka da wadanda ban saba da su ba’?

    Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ba dai kowa yana lura da nasa abu ba, amma kowane a cikinku yana lura da na wadansu.”​—Filibiyawa 2:4.

    Wani dan shekara 19 mai suna Brian ya ce: “Yawancin yaran da ba a san da su a makaranta ba suna fama ne da matsaloli a gida. Idan ka yi abokantaka da su, za ka ga cewa su ma suna da halaye masu kyau.”

Gaskiyar al’amarin: Yin abokai da mutanen da ka fi sabawa da su ba laifi ba ne. Amma, za ka iya amfana idan ka kulla abota da wasu da ba ka saba da su ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka taimaki wadansu, su kuma za su taimake ka.”​—Misalai 11:​25, Littafi Mai Tsarki.

Abin da tsararka suka ce

Maryam

Wata mai suna Maryam, ta ce: “A lokacin da nake makaranta, na kulla abota da wasu ‘yammata amma daga baya sai na lura cewa wasu daga cikin su suna cin zalin mutane, sai na daina tarayya da su. Bayan haka, ya dauki lokaci kafin na sami wasu abokai, amma na yi farin ciki cewa na yi abin da ya dace.”

Alex

Wani mai suna Alex ya ce: “A makaranta, nakan bi wasu abokai don kawai a san da ni. Amma, daga baya na gane cewa bin abokai marasa hankali zai iya bata dangantakarka da mutane ko kuma ya sa ka yi irin rayuwar da ba ka so.”

Bethany

Wata mai suna Bethany ta ce: “Daga lokacin da nake aji daya zuwa aji uku a sakandare, na yi kokari in yi abokantaka da wasu ‘yan makarantarmu da ba sa so in zama abokiyarsu. Da na ga cewa hakata ba ta cim ma ruwa ba, sai na rabu da su kuma na ci gaba da tarayya da wadanda suke so na.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba