Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 122
  • Mene ne Ake Nufi da Attaurat?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Ake Nufi da Attaurat?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
  • Anya Shaidun Jehobah Sun Yarda da Tsohon Alkawari Kuwa?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Dokar ‘Jehobah Cikakkiya Ce’
    Ka Kusaci Jehobah
  • Shin Allah Ya Damu da Mata Kuwa da Gaske?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 122
Fallen Attaurat

Mene ne Ake Nufi da Attaurat?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Kalmar Turanci da ake ce da ita “Torah” ko Attaurat a Hausance, an dauko ta ne daga kalmar Ibrananci toh·rahʹ, kuma za a iya fassara ta a matsayin “koyarwa,” ‘koyo’ ko kuma “shari’a.”a (Misalai 1:8; 3:1; 28:4) Misalan da ke biye za su nuna yadda ake amfani da wannan Kalmar a cikin Littafi Mai Tsarki.

  • “Attaurat” tana nufin littattafai biyar na farko na Littafi Mai Tsarki, wato, Farawa, Fitowa, Levitikus, Littafin Lissafi, da Kubawar Shari’a kuma ana kiransu Pentateuch. An dauko kalmar nan Pentateuch daga kalmar Helenanci da ke nufin “kundin littattafai biyar.” Musa ne ya rubuta Attaurat, shi ya sa ake kiransa “littafin shari’ar Musa.” (Joshua 8:31; Nehemiya 8:1) Hakan ya nuna cewa da farko an hada littattafan ne a cikin kundi daya amma daga baya aka rarraba su domin a iya karanta su da sauki.

  • Ana amfani da kalmar nan Attaurat idan ana so a yi magana game da dokokin da aka ba wa Isra’ila a kan wasu batutuwa kamar su, “shari’ar hadaya ta zunubi” da “shari’a [a kan] kuturta,” da kuma “shari’a [a kan] Naziri.”​—Levitikus 6:25; 14:57; Littafin Lissafi 6:13.

  • A wasu lokuta, Attaurat tana nufin umurni ko koyarwa, da ake samu daga iyaye ko daga mutane masu hikima ko kuma daga wurin Allah.​—Misalai 1:8; 3:1; 13:14; Ishaya 2:3.

Mene ne ke cikin Attaurat ko Pentateuch?

  • Tarihi ne game da yadda Allah ya yi mu’ammala da mutane tun daga lokacin da ya halicci Adamu har zuwa lokacin da Musa ya mutu.​—Farawa 1:​27, 28; Kubawar Shari’a 34:5.

  • Dokar da Allah ya bayar ta hannun Musa. (Fitowa 24:3) Dokar ta kunshi fannoni fiye da 600. Mafi muhimmanci a cikin su shi ne ake kira Shema. A cikin Shema, an ambata cewa: “Ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan karfinka.” (Kubawar Shari’a 6:​4-9) Yesu ya ce wannan ita ce “babbar doka, ita ce kuwa ta fari.”​—Matta 22:​36-38.

  • Sunan Allah, wato Jehobah, kuma ya bayyana wajen sau 1,800. Attaurat tana dauke da dokar da ta ce ya kamata bayin Allah su rika kira sunansa.​—Littafin Lissafi 6:​22-27; Kubawar Shari’a 6:13; 10:8; 21:5.

Ra’ayin da ba daidai ba game da Attaurat

Karya: Dokokin da ke cikin Attaurat za su dawwama har abada.

Gaskiya: Wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun yi maganar wasu batutuwa da ke cikin Attaurat, wato kamar Assabaci da firistoci da kuma Ranar Yin Kafara a matsayin dokokin da za su ‘dawwama.’ (Fitowa 31:16; 40:15; Levitikus 16:​33, 34) Amma asalin kalmar Ibrananci da aka yi amfani da ita a nan tana nufin abin da zai dade ne, ba lalle zai kasance har abada ba.b Bayan da aka yi amfani da dokar da Allah ya ba Musa har wajen shekara 900, Allah ya ce zai tsara “sabon alkawari.” (Irmiya 31:​31-33) Sa’ad da Allah ya ce zai tsara “sabon alkawari,” hakan yana nufin cewa “ya mai da na fari tsoho ke nan.” (Ibraniyawa 8:​7-13) Yanzu, an yi wajen shekara 2,000 da aka tsara sabon alkawari ta wurin mutuwar Yesu.​​—Afisawa 2:15.

Karya: Al’adun da Yahudawa suka kafa da kuma Talmud suna da matsayi daya ne da Attaurat.

Gaskiya: Babu wani wuri a Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewa Allah ya ba Musa wasu dokoki ta baki, ban da wadanda ya rubuta a cikin Attaurat. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji ya ce ma Musa, . . . ka rubuta wadannan zantattuka.” (Fitowa 34:27) Farisiyawa ne suka sa a rubuta dokokin Yahudawa da ba sa cikin Attaurat, wadanda ake kira Mishnah, kuma daga baya aka kara wasu dokoki a kai sai aka soma kiransa Talmud. Yawancin dokokin da ke cikin Talmud ba su jitu da abin da ke cikin Attaurat ba. Don haka ne Yesu ya gaya wa Farisiyawa cewa: ‘Saboda al’adunku kun yi banza da Maganar Allah.’​—Matta 15:​1-9.

Karya: Bai kamata a koya wa mata abin da ke cikin Attaurat ba.

Gaskiya: Dokar da Allah ya ba Musa ta ce a karanta wa dukan mutanen Isra’ila dokokin Ubangiji har da mata da yara. Me ya sa? ‘Domin su ji, su koya, su ji tsoron Ubangiji Allahnsu, su kiyaye dukan zantattukan wannan shari’a.’​—Kubawar Shari’a 31:​10-12.c

Karya: Akwai abubuwa na sirri a cikin Attaurat.

Gaskiya: Musa wanda ya rubuta Attaurat, ya ce sakon da ke ciki mai sauki ne kuma dukan mutane za su iya koyon abin da ke ciki don ba sirri ba ne. (Kubawar Shari’a 30:​11-14) Al’adar Yahudawa da ake kira Kabbalah ta sa Yahudawa sun soma dauka cewa abin da ke cikin Attaurat sirri ne kuma sun yi hakan ne domin su suke “kaga” yadda za a bayyana Nassosi.d​—2 Bitrus 1:16.

a Ka duba Revised Edition of The Strongest Strong’s Exhaustive Concordance of the Bible, na 8451 a karkashin sashen “Hebrew-Aramaic Dictionary-Index to the Old Testament.”

b Ka duba Theological Wordbook of the Old Testament, Kundi na 2, shafi na 672-​673.

c Dokokin shari’a na Yahudawa sun hana mata karanta Attaurat, amma Attaurat ba ta haramta hakan ba. Alal misali, a cikin Mishnah, wani malami mai suna Rabbi Eliezer ben Hyrcanus ya ce: “Duk wanda ya koya wa ‘yarsa abin da ke cikin Attaurat yana mai da ita ‘yar iska ne.” (Sotah 3:4) A cikin Jerusalem Talmud ma an rubuta wani abu kuma da wannan malamin ya fada cewa: “Gwamma a kona Attaurat a wuta maimakon a koya wa mace abin da ke cikin ta.”​—Sotah 3:​19a.

d Alal misali, a cikin Encyclopædia Judaica, an bayyana ra’ayin da Yahudawa suke da shi game da Attaurat. Ga abin da littafin ya fada game da yadda Yahudawa suke daukan Attaurat: “Ba hanya daya ba ce za a iya fahimtar abin da ke cikin Attaurat domin akwai hanyoyi dabam-dabam na fahimtar ta bisa ga mai karanta ta.”​—Juyi na biyu, Kundi na 11, shafi na 659.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba