Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwyp talifi na 57
  • Me Ya Sa Zai Dace In Sulhunta da ’Yan’uwana?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Zai Dace In Sulhunta da ’Yan’uwana?
  • Tambayoyin Matasa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Abokai masu ban haushi”
  • Dalilai biyu da suka sa ya kamata ku sulhunta
  • Yesu Ya Yi Aure Ne? Yana da ’Yan’uwa Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Su Waye Ne ’Yan’uwanmu?
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
Tambayoyin Matasa
ijwyp talifi na 57
Yaya da kanuwarsa suna dafuwa a kicin

TAMBAYOYIN MATASA

Me Ya Sa Zai Dace In Sulhunta da ’Yan’uwana?

  • “Abokai masu ban haushi”

  • Dalilai biyu da suka sa ya kamata ku sulhunta

  • Abin da tsararku suka ce

“Abokai masu ban haushi”

Wasu sukan ce, ’yan’uwa “abokai ne masu ban haushi.” Ma’ana, kana kaunarsu kuma su ma suna kaunarka amma a yawancin lokuta kuna fada. Wata ’yar shekara 18 mai suna Helena ta ce, “Kanina yana yawan ba ni haushi, ya san abin da zai yi da zai bata min rai sosai.”

Yana yiwuwa a sasanta matsalolin da sukan taso tsakanin ’yan’uwa ta wurin tattaunawa kawai. Alal misali:

  • Yaya da kani da suke zaune a daki daya za su iya yin fada domin wani yana tsoma baki a sha’anin da bai shafe shi ba. Me ya kamata su yi? Ya kamata su guji nacewa a kan ra’ayinsu kuma su daina shisshigi a batun da bai shafe su ba. Kari ga haka, su bi ka’idar da ke cikin littafin Luka 6:31.

  • ’Yan’uwa mata biyu za su iya yin “aron” rigunan juna ba tare da neman izinin mai shi ba. Me ya kamata su yi? Ya kamata su tattauna batun da kyau don su san yadda za su rika taba kayan juna kuma su bi ka’idar da ke littafin 2 Timotawus 2:24.

A wasu lokuta, matsalolin da suke tasowa tsakanin ’yan’uwa suna iya zama da tsanani har su haifar da munanan sakamako. Ga misalai biyu daga Littafi Mai Tsarki:

  • Maryamu da Haruna sun yi kishin Musa kuma hakan ya jawo musu mummunan sakamako. Ka karanta labarin a Littafin Lissafi 12:1-15. Sa’an nan, ka tambayi kanka: ‘Me zai taimaka min don kada in yi kishin ’yar’uwata ko dan’uwana?’

  • Kayinu ya ji haushin dan’uwansa Habila har ya kashe shi. Ka karanta labarin a littafin Farawa 4:1-12. Sa’an nan, ka tambayi kanka: ‘Me zai taimaka mini in bi da ’yan’uwana cikin hakuri?’

Dalilai biyu da suka sa ya kamata ku sulhunta

Akwai dalilai biyu da suka sa ya kamata ku sulhunta da ’yan’uwanku, ko da yin hakan bai da sauki.

  1. Hakan zai nuna cewa kun yi girma. Wani mai suna Alex ya ce, “Ina saurin fushi da kannena biyu mata. Amma yanzu na girma shi ya sa ina yawan hakuri da abubuwan da suke yi min.”

    Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum mai kamewa yana da hikima, amma mai zafin rai yana bayyana wautarsa a fili.”—Misalai 14:29, Littafi Mai Tsarki.

  2. Hakan zai taimaka muku nan gaba. Idan kuna iya sulhuntawa da ’yan’uwanku a yanzu, a nan gaba zai zama muku da sauki ku sulhunta da abokin aurenku ko abokan aikinku ko ma wasu dabam.

    Gaskiyar lamarin: A gida ne mutum zai iya koyan yadda zai kulla dangantaka mai kyau da mutane kuma hakan zai taimaka masa daga baya in ya girma.

Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Idan zai yiwu, ku zauna lafiya da dukan mutane.’—Romawa 12:18.

Idan kuna neman abin da zai taimaka muku ku warware matsaloli tsakaninku da ’yan’uwanku, ku bincika “Abin da tsararku suka ce” da kuma shafin rubutun nan: “Ta Yaya Zan Zauna Lafiya da ’Yan’uwana?”

Abin da tsararku suka ce

Jessica

Wata mai suna Jessica ta ce: “Ina da ’yan’uwa mata guda uku kuma ba kowane lokaci ba ne muke jituwa. Amma na san cewa su ne suka san ni ciki da waje kuma ba za su taba yin watsi da ni ba.”

Tyler

Tyler ya ce: “A wasu lokuta ina iya bata wa dan’uwana rai kuma shi ma yakan bata min rai, amma ba wai ba ma kaunar juna ba ne. Ina son yadda yake aiki da kwazo, har ma ya yi fiye da abin da ake bukata a gare shi.”

Cameo

Cameo ta ce: “Ina son kasancewa tare da mutane shi ya sa ina farin cikin samun ’yan’uwa maza biyu. Zama da su ya sa na koyi yadda zan iya zauna lafiya da wadanda halayenmu ba daya ba. Na gode wa Allah da ya ba ni wadannan ’yan’uwan.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba