Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 114
  • Akwai “Zunubai Bakwai da Ke Sa Mutuwa”?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Akwai “Zunubai Bakwai da Ke Sa Mutuwa”?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
  • Mene Ne Ake Nufi da Zunubi?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Allah “Mai Yin Gafara”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Allah Zai Gafarta Mini Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Yadda Muke Amfana Idan Jehobah Ya Gafarta Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 114
Wani mutum mai bakin ciki

Akwai “Zunubai Bakwai da Ke Sa Mutuwa”?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki bai kwatanta jerin “zunubai bakwai da ke sa mutuwa” ba. Amma ya koyar cewa yin zunubai masu tsanani zai hana mutum samun ceto. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce “ayyukan jiki” kamar yin lalata da bautar gunki da sihiri da yawan fushi da kuma yin maye suna cikin zunubai masu tsanani. Ya kuma ce: “Wadanda ke aika wadannan al’amura ba za su gaji mulkin Allah ba.”—Galatiyawa 5:19-21.a

Amma Littafi Mai Tsarki ya ambata abubuwa bakwai da Ubangiji yake kyamarsu, ko ba haka ba?

Kwarai kuwa. Littafin Misalai 6:16 ya ce: “Akwai abu shida wadanda Ubangiji ya ki: I, har bakwai ma wadanda ransa yake kyamarsu.” Amma, ba a ambata dukan zunubai a cikin littafin Misalai 6:17-19 ba. Maimakon haka, an kwatanta ainihin ayyukan da ba su kyau da suka hada da tunaninmu da furucinmu da abubuwan da muke yi.b

Mene ne “zunubi da ke na mutuwa”?

Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa dukan zunubai suna kai ga mutuwa. (1 Yohanna 5:16) Amma za a cece mu daga zunubi da mutuwa ta wurin hadayar fansa da Yesu Kristi ya ba da. (Romawa 5:12; 6:23) Saboda haka, fansa da Kristi ya ba da ba ta ceton mutum daga “zunubi da ke na mutuwa.” Mutumin da yake yin irin wannan zunubin ya yi niyyar bin tafarki na zunubi kuma ba zai taba canja halinsa ba. Don haka, Littafi Mai Tsarki ya kuma ce “ba za a gafarta” wa mutum irin wannan zunubin ba.—Matta 12:31; Luka 12:10.

Ina ne aka samo jerin zunubai bakwai da ke sa mutuwa?

Zunubai bakwai da ke sa mutuwa sun samo asalinsu daga munanan halaye guda takwas. Evagrius Ponticus ne ya jera wadannan ayyuka a karni na hudu bayan haihuwar Yesu, shi ne ya motsa John Cassian wanda sufi ne ya yi wadannan rubuce-rubucen. A karni na shida, Paparuma Gregory na daya ya canja munanan halaye guda takwas da Cassian ya rubuta zuwa zunubai bakwai da ke sa mutuwa na koyarwar addinin Katolika. Wadannan zunuban sun kunshi alfahari da hadama da kyashi da kishi da yin maye da yawan fushi da kuma ragwanci. Gregory yana ganin cewa wasu zunubai sun fito daga wadannan ne.

a Ko da yake an lissafa zunubai masu tsanani guda 15 a littafin Galatiyawa 5:19-21, hakan ba ya nufin cewa sun kāre ke nan, don bayan ya lissafa su, Littafi Mai Tsarki ya ce “da irin wadannan.” Saboda haka, an karfafa mai karatu ya yi amfani da basira don ya fahimci abubuwan da ba a ambata a ciki ba amma suna cikin ‘irin wadannan’ zunuban.

b Littafin Misalai 6:16 yana dauke da misalin karin magana na Ibrananci da ya nuna bambanci da ke tsakanin furuci na farko da na biyun. Ana yawan ganin irin wannan furucin a cikin Nassosi.—Ayuba 5:19; Misalai 30:15, 18, 21.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba