Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 102
  • Shin, Yin Caca Zunubi Ne?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shin, Yin Caca Zunubi Ne?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 102
Wani dan caca yana duba sakamakon cacar da ya yi a kan tikitinsa na caca yayin da ake sanar da sakamakon a kan talabijin

Shin, Yin Caca Zunubi Ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai yi dogon bayani a kan batun caca ba, za mu iya ganewa daga nazarin ka’idodin Littafi Mai Tsarki cewa yin caca zunubi ne a gaban Allah.—Afisawa 5:17.a

  • Kwadayi ne yake sa mutane su yi caca kuma Allah ba ya son mai kwadayi. (1 Korintiyawa 6:9, 10; Afisawa 5:3, 5) Masu caca suna sa rai za su yi kudi daga hasarar wasu, amma Littafi Mai Tsarki ya haramta yin kyashi.—Fitowa 20:17; Romawa 7:7; 13:9, 10.

  • Yin caca, ko da da kudi kadan ne, yana iya sa mutum ya zama mai son kudi.​—1 Timotawus 6:9, 10.

  • A yawancin lokuta, masu yin caca suna dogara ne ga camfi ko kuma sa’a. Amma hakan bautar gumaka ne a gaban Allah kuma Allah ba ya amincewa da ibadar wadanda suke da irin wannan halin.—Ishaya 65:11.

  • Littafi Mai Tsarki ya karfafa mu mu yi aiki da karfinmu don mu ciyar da kanmu, maimakon mu yi sha’awar mallakar abin wasu. (Mai-Wa’azi 2:24; Afisawa 4:28) Wadanda suke bin wannan shawarar Littafi Mai Tsarki suna ‘yin aiki’ domin su sami abinci.—2 Tasalonikawa 3:10, 12.

  • Caca tana sa mutum ya kasance da halin gasa kuma Littafi Mai Tsarki ya haramta hakan.—Galatiyawa 5:26.

a A cikin Littafi Mai Tsarki, an ambata caca sau daya ne kawai dangane da abin da sojojin Romawa suka yi a kan rigar Yesu domin biya wa kansu muradi.—Matta 27:35; Yohanna 19:23, 24; Contemporary English Version; Good News Translation.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba