Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwfq talifi na 24
  • Me ya Sa Ba Ku Kiran Wajen Taronku Coci Ba?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me ya Sa Ba Ku Kiran Wajen Taronku Coci Ba?
  • Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Me ya sa muke kiransa “Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah”?
  • Abubuwan da Ke Cikin Littafin Filimon
    Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
  • Wannan Wurin Ne Muke Bauta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Me Ya Sa Kake Bukatar Ka Rika Halartar Taro a Majami’ar Mulki?
    Tambayoyin Matasa
  • Amfanin Yin Gaisuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Tambayoyin da Ake Yawan Yi
ijwfq talifi na 24

Me ya Sa Ba Ku Kiran Wajen Taronku Coci Ba?

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar Hellenanci da a kan fassara zuwa “coci” wani lokaci, tana nufin taron mutane masu ibada ne ba majami’ar da ake yin ibadar ba.

Ka yi la’akari da wannan misalin: Sa’ad da manzo Bulus ya rubuta wasika zuwa ga Kiristoci da ke Roma, bayan ya aika gaisuwa ga Akila da Biriska sai ya dada cewa: “Ku kuma gai da ikilisiyar [coci] da ke taruwa a gidansu.” (Romawa 16:5, Littafi Mai Tsarki) Bulus bai aika da gaisuwarsa zuwa ga ginin ba, amma ga mutanen ne, wato wadanda da ke taruwa a gidan.a

Saboda haka, maimakon a kira wajen da muke ibada coci, muna kiransa “Majami’ar Mulki.”

Me ya sa muke kiransa “Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah”?

Ga wasu dalilan da suka sa wannan sunan ya dace:

  • Ginin yana kama da majami’a ko kuma wajen taro.

  • Muna taruwa a wurin don mu yi wa Jehobah sujjada, wanda ya yi tanadin Littafi Mai Tsarki, kuma muna ba da shaida game da shi.​—Zabura 83:18; Ishaya 43:12.

  • Muna kuma taruwa don mu koya game da Mulkin Allah, wanda Yesu ya yi wa’azinsa sau da sau.​—Matta 6:9, 10; 24:14; Luka 4:43.

Muna gayyatarka zuwa Majami’ar Mulkin da ya fi kusa da kai don ka ga yadda Shaidun Jehobah suke gudanar da taronsu.

a An yi wasu kalamai makamancin haka a 1 Korintiyawa 16:19; Kolosiyawa 4:15; da kuma Filimon 2.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba