Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwyp talifi na 12
  • Me zan yi idan aka yi mini zolaya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me zan yi idan aka yi mini zolaya?
  • Tambayoyin Matasa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mene ne zolaya?
  • Me ya sa mutane suke zolayar wasu?
  • Su waye ne aka fi zolayar su?
  • Me za ka yi idan aka zolaye ka?
  • Me Zan Yi Idan Aka Zolaye Ni a Makaranta?
    Amsoshi ga Tambayoyi 10 da Matasa Suke Yi
  • Ta Yaya Za Ka Taimaka Wa Yaronka Idan Ana Cin Zalinsa?
    Taimako don Iyali
  • Ka Dogara ga Jehobah Saꞌad da Ake Cin Zalin Ka
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Me Zan Yi Idan Ana Cin Zalina ta Intane?
    Tambayoyin Matasa
Tambayoyin Matasa
ijwyp talifi na 12

TAMBAYOYIN MATASA

Me zan yi idan aka yi mini zolaya?

  • Mene ne zolaya?

  • Me ya sa mutane suke zolayar wasu?

  • Wa aka fi yi wa zolaya?

  • Me za ka yi idan ana zolayar ka?

Kari ga haka, ka karanta wasu shawarwari da tsararka suka bayar da kuma kalami da wani malami ya yi game da zolaya, bayan haka sai ka wasa kwakwalwarka.

Zolaya ba batun wasa ba ne. Wani bincike da aka yi a kasar Britaniya ya nuna cewa matasa fiye da kashi arba’in cikin dari da aka ba da labari cewa sun kashe kansu a sakamakon zolayar da aka yi musu ne.

Mene ne zolaya?

Zolaya ba kawai a ce an duki mutum ba. Ya kunshi abubuwa na biye.

  • Zagi. Celine ’yar shekara 20 ta ce: “’Yammata sukan yi zagi sosai. Ba zan taba manta da irin sunayen da suke kirana da su da kuma abubuwan da suke gaya mini ba.” Suna sa in ji ni ba komi ba kuma an ki ni, ban da haka, ban da amfani. Gwamma duka da zagi.”

  • Ware kai daga mutane. “Wata yarinya mai suna Haley ’yar shekara 18 ta ce: “’Yan ajinmu sun soma guduna. Kuma a lokacin cin abinci ba sa so in zauna tare da su. Na yi shekara guda ina cin abinci ni kadai kuma ina ta kuka.”

  • Zolaya ta Intane. “Wani yaro mai suna Daniel dan shekara 14 ya ce: “Da kalilan kalmomi kawai za ka iya bata sunan mutum ko kuma rayuwarsa ta Intane. Hakan ba kara gishiri ba ne, yana faruwa!” Kari ga haka, zolaya ta Intane ya kunshi aika hotuna da sakonnin banza ta wayar salula.

Me ya sa mutane suke zolayar wasu?

Ga wasu dalilai nan.

  • Su ma an taba zolayar su. Wani matashi mai suna Antonio ya ce: “Na gaji da yadda tsarata suke zolayana sai ni ma na soma zolayar wasu. Amma daga baya na gane cewa bai dace in rika zolayan wasu ba!”

  • Ba su da gurbi mai kyau. Wani littafi mai suna Life Strategies for Dealing With Bullies da Jay McGraw ya rubuta, ya ce: “A yawancin lokaci yara da suke zolayar wasu suna hakan ne don sun ga yadda iyayensu da ’yan’uwansu da danginsu suke zolayar wasu.

  • Suna yi kamar sun fi kowa karfi, amma hakan ba gaskiya ba ne. Wata mai suna Barbara Coloroso ta rubuta a littafinta mai suna The Bully, the Bullied, and the Bystande, cewa: “Yaran da suke zolayar mutane, a yawancin lokaci suna nuna kamar sun fi wasu karfi don su boye wani abu ko kuma kasawarsu ne.

Su waye ne aka fi zolayar su?

  • Wadanda suke ware kansu. Matasan da suke ware kansu da ba sa cudanya da mutane, su ake yawan yi wa zolaya.

  • Matasan da suke dabam. A kan zolayi wasu matasa saboda irin tufa da suke sanyawa, don kabilarsu ko kuma addininsu, har ma da wanda ya nakasa, abin da dai zai sa mai zolayar jin dadin yin zolayarsa.

  • Matasan da ba su da gaba gadi. Ana yawan zolayar matasan da ba sa daraja kansu. Wadannan ne aka fi zolayarsu da yake an san cewa ba za su iya ramawa ba.

Me za ka yi idan aka zolaye ka?

  • Ka kyale su. Wata matashiya mai suna Kylie ta ce: “Masu zolaya suna son su yi nasara wajen sa ka ji kamar kai ba kome ba. Idan ka kyale su lokacin da suke zolayarka za su rabu da kai.” Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai-hikima ya kan danne shi ya kwabe shi.”—Misalai 29:11.

  • Kada ka rama. Ramako ba shi ne zai magance matsalar ba, amma kara matsalar zai yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku sāka wa kowane mutum mugunta da mugunta.”—Romawa 12:17; Misalai 24:19.

  • Kada ka sa kanka cikin matsala. Idan zai yiwu, ka guji wurare da kuma yanayoyin da za su sa a yi maka zolaya.​Misalai 22:3.

  • Ka gwada yadda za ka iya ba da amsar da ba ka zata ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Amsa magana da tattausan harshe takan kwantar da hasala.”—Misalai 15:1.

  • Ka yarda da hakan. Alal misali, idan aka zolaye ka cewa kana da kiba, za ka iya yarda ka ce, “Da a ce zan iya rage kiban nan!”

  • Ka bar wurin. Nora ’yar shekara 19 ta ce: “Idan ka yi shiru zai nuna cewa ka manyanta kuma ka fi wanda yake maka zolayar karfi. Kuma hakan yana nufin kana da kamewa, wato halin da wanda yake maka zolayar bai da shi.”

  • Ka kasance da gaba gadi. Wata yarinya mai suna Rita ta ce: “Masu zolaya suna sanin lokacin da muka damu kuma a wannan lokacin ne za su zolaye mu don mu ji kunya.”

  • Ka gaya wa wani. Wani bincike ya nuna cewa fiye da rabin mutanen da ake zolayar su ta Intane ba sa gaya wa kowa abin da suke fuskanta, watakila saboda kunya (musamman idan maza ne) ko kuma suna jin tsoron ramawa. Amma ya kamata mu sani cewa, masu zolaya sukan ji dadin yin hakan a boye. Amma gaya wa wasu game da yanayin mataki ne na farko da zai sa a daina yi ma ka zolaya.

Shawara daga tsararka

Antonio ya ce: “Ka guji wurare da kuma yanayoyin da zai sa a zolaye ka. Ya kamata mu tuna cewa masu zolaya suna da nasu matsaloli. Sanin hakan zai rage yadda kake jin zafin zolaya.”

Jessica ta ce: “Ka kasance da gaba gadi. Kada ka ji tsoron bin abin da ka gaskata. Masu zolaya sukan daina yin hakan idan suka ga cewa ba ka jin tsoronsu.”

Kalamin wani malami

“Zolaya babbar matsala ce. A makarantar da nake koyarwa, har fada ake yi cikin aji! Wasu yara suna jin dadin zolayar wasu don yana sa su shahara kuma su ga sun fi kowa.

Wata malama daga Amirka mai suna Jenilee ta ce: “A yawancin lokaci, wadanda ake zolayarsu ba sa so su kai kara don suna tsoron cewa mai zolayar zai rama ko kuma ’yan ajin su ki shi. Watakila suna shakkar iya magance matsalar zolaya. Duk da haka, ina karfafa duk wani da ake masa zolaya ya gaya wa wani. Abin da ya kamata a yi ke nan, domin hakan zai iya sa a dauki matakin da zai sa a daina yi wa mutum zolaya.”

Wasa kwakwalwa

Gaskiya ko Karya

  1. An dade ana yin zolaya.

  2. Zolaya tsokana ce kawai da ake wa mutane.

  3. Za ka yi kokari sosai idan kana son ka sa a daina yi maka zolaya.

  4. Kai ne ka sa ake zolayar ka.

  5. Wasu da aka yi musu zolaya sun zama masu zolaya su ma.

  6. Idan an zolaye ka, bai kamata ka rama ba.

  7. A yawancin lokaci masu yin zolaya ba su da karfi, zakin baki gare su.

  8. Masu yin zolaya za su iya su daina.

AMSOSHI

  1. Gaskiya. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce Nephilim, wato mutanen da sunansu yake nufin wadanda suke sa wasu su fādi.—Farawa 6:4.

  2. Karya. Zolaya zai iya sa wasu su kashe kansu. Abin bakin ciki, wasu da aka yi wa zolaya kullum sun kashe kansu.

  3. Karya. Sau da yawa masu yin zolaya sun fi wadanda suke zolaya karfi, shi ya sa wadanda ake zolaya ba sa iya ramawa.

  4. Karya. Babu wanda ya dace a yi masa zolaya! Mai zolaya yana da alhakin abin da yake yi.

  5. Gaskiya. Abin bakin ciki, wasu sun rama abin da aka yi musu a kan wasu.

  6. Karya. Karya ce cewa wanda ya ga ana wa wani zolaya bai da laifi. Idan ka ga sa’ad da ake wa wani zolaya kuma ba ka ce kome ba, za ka sa yanayin ya yi muni maimakon magance matsalar.

  7. Gaskiya. Da yake wasu masu zolaya suna fahariya, yawancinsu ba su da wani karfi, zakin baki ne kawai don su ce sun fi wasu.

  8. Gaskiya. Ta wurin sa baki ko kuma bada taimako, yana sa masu yin zolaya za su iya daina halinsu.—Afisawa 4:23,24.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba