Thomas Jackson/Stone via Getty Images
KU ZAUNA A SHIRYE!
Ya Dace Ne Mu Sa Zuciya a Shekara ta 2024—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
Mutane da yawa suna ganin babu mafita daga matsalolin da za su adabi duniya a shekara ta 2024. Duk da haka, za mu iya kasancewa da bege don nan gaba. Ta yaya?
Littafi Mai Tsarki yana sa mu kasance da bege
Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa Allah zai magance matsalolin da suke sa mu ji kamar ba mu da bege. Ba da dadewa ba, Allah “zai share . . . dukan hawaye daga idanun[mu]. Babu sauran mutuwa, ko bakin ciki, ko kuka, ko azaba.”—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4.
Don ka kara koya game da alkawuran da suke cikin Littafi Mai Tsarki don nan gaba, ka karanta talifin nan “A Real Hope for a Better Tomorrow.”
Yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka a yau
Littafi Mai Tsarki yana sa mu kasance da bege, da kuma raꞌayin da ya dace don mu daina ji kamar ba mu da bege. (Romawa 15:13) Shawarwarin Littafi Mai Tsarki za su taimaka maka ka jimre da matsalolin da kake fuskanta a yanzu, kamar talauci ko rashin adalci ko kuma rashin lafiya.
Ka koya yadda kasancewa da begen da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya taimaka ma wani mutum ya samu kwanciyar hankali kuma ya rika farin ciki duk da cewa ya yi girma cikin talauci. Ka kalli bidiyon Juan Pablo Zermeño: Jehobah Ya Ba Ni Rayuwa Mai Maꞌana.
Ka ga yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka idan zuciyarka tana damunka don abin da ka yi ko kana bakin ciki ko yawan damuwa ko kuma wani naka ya rasu. Ka karanta talifin “Shin Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taꞌazantar da Ni Kuwa?”
Ka ga yadda wata soja a dā da ta kwatanta kanta a matsayin ‘marar tausayi kuma ba ta damuwa da mutane’ ta kasance da bege don abin da ta koya a Littafi Mai Tsarki.Ka kalli bidiyon Na Bar Aikin Soja.
Ka sa shekara ta 2024 ta zama mai kyau a gare ka da iyalinka ta wajen kara koya yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka muku. Ka yi kokari ka sa a soma nazarin Littafi Mai Tsarki da kai kyauta. Ka koya yadda Allah zai iya sa ka kasance da kwanciyar hankali a yanzu da kuma yadda za ka sa zuciya a “rayuwa ta nan gaba.”—Irmiya 29:11.