ilbusca/E+ via Getty Images
KU ZAUNA A SHIRYE!
Me Ya Sa Mutane Ba Sa Zaman Lafiya?—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
Shugabanai da kungiyoyin duniya ba su iya sa mutane su yi zaman lafiya ba. A yau, ana yake-yake fiye da duk wani yakin da aka taba yi tun daga lokacin da aka yi Yakin Duniya na Biyu. Mutane wajen biliyan biyu a duniya, wato kwata na mutane da ke duniya a yanzu suna zama a wuraren da ake wadannan yake-yaken.
Me ya sa ꞌyan Adam ba za su iya sa a samu matukar zaman lafiya ba? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?
Dalilai uku da suka sa ꞌyan Adam ba za su iya sa a zauna lafiya ba
1. Mutane suna nuna halayen da ke hana su yin kokarin zaman lafiya. Littafi Mai Tsarki ya ce a lokacinmu, “mutane za su zama masu son kansu, masu son kudi, masu takama, masu girman kai, . . . marasa tsarki, . . . masu rike juna a zuciya, . . . marasa kame kansu, marasa tausayi, . . . marasa hankali, masu cika da daga kai.”—2 Timoti 3:2-4.
2. ꞌYan Adam ba za su iya magance matsalolinsu ba tare da taimakon Mahaliccinsu, Jehobah ba.a Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa “ba mutum ne yake da iko ya kiyaye tafiyarsa ba.”—Irmiya 10:23.
3. Shaidan Iblis, wani mugu mai iko sosai ne yake ‘rudin dukan duniya.’ (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9) Muddin “duniya duka tana a hannun mugun nan,” za a ci gaba da yake-yake.—1 Yohanna 5:19.
Wane ne zai sa ꞌyan Adam su zauna lafiya?
Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Allah ne zai sa mutane su zauna lafiya ba ꞌyan Adam ba.
“Na san irin shirin da nake da shi domin ku. Shiri ne na alheri, ba na masifa ba, domin in ba ku sa zuciya da rayuwa ta nan gaba. Ni Yahweh na fada.”—Irmiya 29:11.
Ta yaya Allah zai cika wannan alkawarin? “Allah mai ba da salama kuwa zai tattaka Shaidan.” (Romawa 16:20) Allah zai yi amfani da gwamnati ta sama wadda Littafi Mai Tsarki ya kira “mulkin Allah,” don ya sa a yi zaman lafiya a fadin duniya. (Luka 4:43) Saꞌad da Yesu Kristi wanda shi ne sarkin Mulkin ya soma sarauta, za a koya wa mutane yadda za su zauna lafiya.—Ishaya 9:6, 7
Don samun karin bayani, ka karanta talifin nan“Mene Ne Mulkin Allah Zai Yi?”
a Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah.—Zabura 83:18.