Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mrt talifi na 88
  • Yake-Yake​—Abin da Mulkin Allah Zai Yi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yake-Yake​—Abin da Mulkin Allah Zai Yi
  • Karin Batutuwa
  • Makamantan Littattafai
  • Wa Zai Ceci ꞌYan Farar Hula?​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
    Karin Batutuwa
  • An Shiga Shekara Ta Biyu a Yakin Yukiren​—Wane Bege ne Ke Littafi Mai Tsarki?
    Karin Batutuwa
  • ꞌYan Siyasa Masu Cin Hanci da Rashawa​—Abin da Mulkin Allah Zai yi
    Karin Batutuwa
  • Rasha ta Kai wa Yukiren Hari
    Karin Batutuwa
Dubi Ƙari
Karin Batutuwa
mrt talifi na 88
Wani mutum yana tura kekensa a hanyar da ke cike da burbudin makaman yaki.

Chris McGrath/Getty Images

WAꞌAZI NA MUSAMMAN

Yake-Yake​—Abin da Mulkin Allah Zai Yi

A fadin duniya, yake-yake sun ci gaba da sa mutane shan wahala. Ga wasu rahoto:

  • A ranar 7 ga Yuni, 2023, wata kungiyar bincike da ake kiran Peace Research Institute Oslo ta ce: “A shekarar da ta shige, karin mutane sun mutu domin yake-yake, musamman a Ethiopia da Yukiren.”

  • A ranar 8 ga Fabrairu, 2023, The Armed Conflict Location & Event Data Project (ACLED) sun ce: “Yakin da ake yi a Yukiren daya ne daga cikin yake-yake da suka yi muni a shekara ta 2022. A duk fadin duniya tashin hankali don siyasa ya karu da kashi 27 bisa 100 a shekarar da ta shige, kuma ya shafi mutane wajen biliyan 1.7.”

Littafi Mai Tsarki yana sa mu kasance da bege. Ya ce: “Allah na sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taba rushewa ba.” (Daniyel 2:44) A Mulkin ko gwamnatin ne Allah zai “tsai da yake-yake a dukan duniya.”​—Zabura 46:9.

Mene ne Mulkin Allah?

Mujallar “Hasumiyar Tsaro” mai jigo “Mene ne Mulkin Allah?”

A ranar Satumba 2023, Shaidun Jehobah za su yi waꞌazi na musamman don su gaya wa mutane abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da mulkin Allah. Za mu so ka karanta mujallar Hasumiyar Tsaro mai jigo “Mene ne Mulkin Allah?” Za ka sami amsoshi ga tambayoyi kamar:

  • Wane ne Sarkin Mulkin Allah?

  • Yaushe Ne Mulkin Allah Zai Zo Duniya?

  • Mene Ne Mulkin Allah Zai Yi?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba