Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mrt talifi na 57
  • Yadda Za a Amfana Daga Mutuwar Yesu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za a Amfana Daga Mutuwar Yesu
  • Karin Batutuwa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Taron Shaidun Jehobah
  • Talifofi da bidiyoyi na dandalinmu
  • Ta Yaya Za Ka Amfana Daga Taron Shaidun Jehobah?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Abin da Halartan Taro Yake Nunawa Game da Mu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Amfani da Bidiyoyi don Koyarwa
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Wane ne Yesu?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Karin Batutuwa
mrt talifi na 57
Yesu na dauke da gungume da za a rataye shi a kai.

Yadda Za a Amfana Daga Mutuwar Yesu

Kamar yadda Yesu ya umurce mu, sau daya a kowace shekara Shaidun Jehobah tare da miliyoyin mutane da suka gayyata a duk fadin duniya, suna taruwa don su tuna da mutuwar Yesu. (Luka 22:19) Taron nan na taimaka mana mu fahimci muhimmancin abin da Yesu ya yi saꞌad da ya ba da ransa a madadin ꞌyan Adam. Yana kuma nuna mana yadda za mu amfana daga mutuwar Yesu yanzu da kuma a nan gaba.​—Yohanna 3:16.

Ko ka halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu na wannan shekara ko aꞌa, ta yaya za ka amfana daga mutuwar Yesu? Yesu ya ce mu yi abubuwa biyun nan da suke da muhimmanci:

  1. 1. Mu koya game da Allah da kuma Yesu. A adduꞌar da Yesu ya yi ga Ubansa da ke sama ya ce: “Rai na har abada kuwa shi ne, mutane su san ka, kai da kake Allah makadaici na gaskiya, su kuma san Yesu Almasihu wanda ka aiko.”​—Yohanna 17:3.

  2. 2. Mu yi abin da muka koya. Sau da yawa, Yesu ya ce wajibi ne mu rika yin abin da ya koya mana. Alal misali, a Hudubarsa a kan Dutse Yesu ya kammala da yaba wa duk wanda ya ‘saurare shi kuma ya yi abin da ya ce ya yi.’ (Luka 6:​46-48) A wani lokaci kuma Yesu ya ce: “Yanzu da kun san wadannan abubuwa za ku zama masu albarka idan kun yi su.”​—Yohanna 13:17.

Shin za ka so ka kara koya game da Allah da kuma Yesu? Kana son taimako don ka san yadda za ka yi abin da kake koya? Ga abubuwan da za su iya taimaka maka.

Nazarin Littafi Mai Tsarki

Nazarin Littafi Mai Tsarki da muke yi da mutane kyauta ya taimaka wa mutane da yawa su bincika Littafi Mai Tsarki kuma su yi abin da suke koya.

  • Ka shiga shafin nan Nazarin Littafi Mai Tsarki da Taimakon Wani ko Wata don karin bayani game da yadda muke nazari

  • Ka kalli bidiyon nan Maraba da Zuwa Nazarin Littafi Mai Tsarki don ka ga yadda Shaidun Jehobah suke nazari da mutane.

Taron Shaidun Jehobah

Sau biyu a kowane mako, Shaidun Jehobah sukan taru a wurin ibadarsu da ake kira Majamiꞌar Mulki. A wannan taron, mukan tattauna Littafi Mai Tsarki da kuma yadda za mu yi amfani da koyarwar da ke ciki.

Ba sai mutum ya zama Mashaidin Jehobah kafin ya halarci taron ba, kowa zai iya halarta. Bisa ga yanayinka za ka iya ka je wurin taron ko ka halarta ta bidiyo.

  • Ka kalli bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? don ka ga abin da ake yi a taron.

  • Ka shiga shafin nan Taron Ikilisiya na Shaidun Jehobah don ka nemi wurin taro da ke kusa da kai.

Talifofi da bidiyoyi na dandalinmu

Talifofi da bidiyoyi a dandalin nan za su taimaka maka ka kara koya game da koyarwar Yesu da kuma yadda mutuwarsa take da muhimmanci.

Alal misali, don ka san yadda mutuwar mutum daya ya amfane miliyoyin mutane ka karanta talifofin nan “Ta Yaya Yesu Ya Cece Mu?” da “Me Ya Sa Yesu Ya Sha Wahala Kuma Ya Mutu?” ko ka kalli bidiyon nan Me Ya Sa Yesu Ya Mutu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba