Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mrt talifi na 34
  • Ta’addanci Zai Taba Karewa Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta’addanci Zai Taba Karewa Kuwa?
  • Karin Batutuwa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yaya Allah yake ji game da ta’addanci?
  • Abin da ke jawo ta’addanci
  • Za a kawo karshen ta’addanci
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • “Kada Ku Ji Tsoro, Kada Ku Yi Fargaba”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Karin Batutuwa
mrt talifi na 34
Wani dan kwana kwana yana taimaka wa mutanen da suka tsira daga gini da ya fadi.

Ta’addanci Zai Taba Karewa Kuwa?

Bayan ’yan ta’adda sun kai hari, mukan tambayi kanmu cewa: ‘Allah ya damu da mutane kuwa? Me ya sa wadannan abubuwan suke faruwa? Ta’addancia zai taba karewa kuwa? Ta yaya zan shawo kan tsoron da nake ji?’ Littafi Mai Tsarki ya ba da amsoshi masu gamsarwa.

Yaya Allah yake ji game da ta’addanci?

Allah ya tsani tashin hankali da kuma ta’addanci. (Zabura 11:5; Karin Magana 6:​16, 17) Kuma Yesu wanda yake wakiltar Allah ya ja kunnen mabiyansa a lokacin da suka so su kai ma wasu mutane hari. (Matiyu 26:​50-52) Ko da yake wasu suna da’awar cewa suna kai ma wasu hari ne a sunan Allah, amma Allah bai umurce su su yi hakan ba. Ban da haka, ba ya ma amsa addu’o’insu.​—Ishaya 1:15.

Allah ya damu da duk wadanda suke shan wahala har da wadanda ’yan ta’adda suka kai wa hari. (Zabura 31:7; 1 Bitrus 5:7) Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Allah zai dauki matakin kawo karshen tashin hankali da kuma zalunci.​—Ishaya 60:18.

Abin da ke jawo ta’addanci

Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da ke jawo ta’addanci ya ce: “Na ga wani yana da iko a kan wadansu, ikon kuwa ya cuce shi.” (Mai-Wa’azi 8:9) Mutane sun dade suna amfani da ta’addanci don su ci zalin wasu. A sakamakon irin wannan zaluncin, wasu suna yin amfani da ta’addanci don samun mafita.​—Mai-Wa’azi 7:7.

Za a kawo karshen ta’addanci

Allah ya yi alkawari cewa, zai kawar da tsoro da ta’addanci, kuma zai kawo salama a nan duniya. (Ishaya 32:18; Mika 4:​3, 4) Allah ya ce:

  • Zai kawar da abin da ke kawo ta’addanci. Allah zai sauya gwamnatin ’yan Adam da gwamnatinsa. Wanda zai yi mulki a wannan gwamnati, wato Yesu Kristi zai yi wa kowa adalci kuma zai kawar da ta’addanci da zalunci. (Zabura 72:​2, 14) A wannan lokacin, babu wanda zai yi ta’addanci. Mutane za “su sami farin cikinsu cikin salama a yalwace.”​—Zabura 37:​10, 11.

  • Zai kawar da dukan abin da ta’addanci ya jawo. Allah zai warkar da mutanen da ta’addanci ya shafa, ko ya yi musu illa. (Ishaya 65:17; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​3, 4) Ya yi alkawari cewa zai tā da wadanda suka mutu zuwa rayuwa a duniya cike da salama.​—Yohanna 5:​28, 29.

Littafi Mai Tsarki ya ba mu dalilai musu kyau da suka nuna cewa nan ba da dadewa ba Allah zai dauki mataki. Amma kana iya tunanin cewa, ‘Me ya sa Allah bai riga ya kawar da ta’addanci ba?’ Don ka sami amsar, ka kalli bidiyon nan Me Ya Sa Allah Ya Kyale Mutane Su Sha Wahala?

a “Ta’addanci” yana nufin tsoratar da mutane don kawo canji a gwamnati ko a addini ko kuma a yadda mutane suke bi da juna. Amma wasu mutane za su iya cewa wasu matakan da ake dauka ba ta’addanci ba ne.

Littafi Mai Tsarki yana taimaka wa mutane su jimre

Ga abubuwa biyu da Littafi Mai Tsarki ya ce da za su iya taimaka maka.

  • Ka yi addu’a ga Allah.​—Filibiyawa 4:​6, 7.

  • Ka mai da hankali ga begen da Littafi Mai Tsarki ya bayar.​—Ibraniyawa 6:19.

Don samun karin shawarwari daga Littafi Mai Tsarki, ka duba talifin nan “How to Control Worry.”

Shaidun Jehobah da suka jimre ta’addanci sun sami taimako daga ’yan’uwansu masu bi. Ka yi la’akari da misalai biyu nan:

  • An saka abin tunawa da mutanen da suka mutu a kusa da wata makaranta a birni Beslan, a Rasha.

    Wata mai suna Natalya da danta mai shekaru tara mai suna Aslan, suna makaranta a birnin Beslan a kasar Rasha sa’ad da ’yan ta’adda suka zo suka kwashi mutane fiye da 1,000 suka tafi da su. Abin takaici, daruruwan mutane sun rasa ransu kuma yawancinsu yara ne. Ko da yake Natalya da Aslan sun tsira, suna cikin tashin hankali. Ka ga abin da ya taimaka musu.

  • Pablo da Sophie.

    Pablo da Sophie sun rasa dansu a lokacin da aka kai wa tagwayen ginin Twin Towers a birnin New York hari. Ka kalli wannan bidiyon don ka ga abin da ya taimaka musu da kuma wasu da harin ta’addanci ya shafa.

Littafi Mai Tsarki yana taimaka wa mutane su canja rayuwarsu

Mutane da yawa suna fushi domin rashin adalci da kuma zalunci da ake yi a wannan duniya. Suna iya tunanin cewa tashin hankali da kuma ta’addanci ita ce kadai hanyar samun mafita. Irin mutanen nan za su iya canja ra’ayinsu? E. Don ka ga yadda sakon Littafi Mai Tsarki ya taimaka ma wasu su yi hakan, ka karanta talifin nan “Is a World Without Terrorism Possible?”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba