Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwex talifi na 22
  • Sun Ci-gaba da Waꞌazi a Lokacin Korona

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sun Ci-gaba da Waꞌazi a Lokacin Korona
  • Labarai
  • Makamantan Littattafai
  • Ta Karfafa Mutane duk da Rashin Lafiyarta
    Labarai
  • Rayuwa Za Ta Koma Yadda Take Kafin Annobar Korona? Yadda Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka
    Karin Batutuwa
  • Sakamakon Yin Murmushi!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Kiwon Lafiya​—Abin da Mulkin Allah Zai Yi
    Karin Batutuwa
Labarai
ijwex talifi na 22
Masu shela biyu suna waꞌazi ta tarho da rubuta wasiku.

Sun Ci-gaba da Waꞌazi a Lokacin Korona

Da aka soma korona, ꞌyanꞌuwanmu da dama sun canja yadda suke waꞌazi don su taimaka wa mutane. Ba su je gidajen mutane suna waꞌazi ko su yi hakan a wurin da akwai jamaꞌa ba. Maimakon haka, sun koma rubuta wasiku da yin amfani da waya.a Mutane da yawa sun ji dadin waꞌazin kuma Jehobah ya sa albarka. (Karin Magana 16:​3, 4) Ga wasu labarai.

Kafin a soma korona, wata ꞌyarꞌuwa mai suna Helen tana ziyartar wata mata kuma ta so ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ita amma matar ta ki. Ana rana guda kafin a hana fita don annobar korona a yankinsu, Helen ta ba matar Littafi Mai Tsarki da littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? Bayan da aka hana fita, sai ꞌyarꞌuwa Helen ta sake ce wa matar su soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Kuma ta ce mata idan ta yarda ta waya za su rika yi. A wannan karon matar ta yarda, ta ji dadin tattaunawar da suke yi har ta ce Helen ta rika nazari da ita kowace rana. Ban da haka ma, matar ta soma halartan taro ta waya, tana bin abin da take koya kuma tana gaya wa mutane abin.

Da wasu ꞌyanꞌuwa suke waꞌazi, sai suka ce bari su rubuta ma ꞌyan sanda da ke yankinsu wasika, su yi godiya don aiki mai muhimmanci da suke yi. ꞌYan sandan sun yi mamaki da suka karanta wasikun. Wani hafsa ya gaya ma wani dattijo mai suna Jefferson cewa, “Na aza Shaidun Jehobah suna adawa da ꞌyan sanda.” Sai danꞌuwa Jefferson ya kara fahimtar da shi cewa ba haka ba ne. ꞌYan sandan sun ji dadin maganganun alheri da ꞌyanꞌuwan suka yi a wasikun. Har sai da suka manna wasikun a kofar shiga folistashan dinsu. Daya daga cikinsu ya ce: “Kila wannan ya taimaka wa mutane su fara ganinmu da mutunci.”

Akwai wasu majagaba biyu masu suna Edna da Ednalyn.b Ba su da sabis na intane a gidansu, don haka, a lokacin ba sa iya shiga taro da wayarsu. Da suka ga haka, sai suka kira wata makwabciyarsu da take da irin sabis da ake kira Wi-Fi. Sai suka roke ta ko za ta bar su su yi amfani da sabis din, saꞌan nan su rika hada kudi suna biya. Da matar ta ji haka, sai ta bar su su rika yin amfani da sabis din kyauta. Da Edna da Ednalyn suka gayyace ta ita ma ta zo taron, ta yarda. A yanzu haka, ita matar da wani danta da jikokinta biyu suna nazari da Shaidun Jehobah kuma suna zuwa taro a kai a kai.

Akwai wasu ꞌyanꞌuwa maza da mata ma da suka gayyaci makwabtansu da abokan aikinsu da dai sauransu su zo su saurari jawabi ga jamaꞌa da za a yi ta bidiyo. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Ellaine tana aiki a asibiti. Da farko ba ta so ta gayyaci abokan aikinta ba. Ta dauka cewa wasu likitocin ba za su so Shaidun Jehobah ba. Duk da haka, ta yi kokari ta tura wa likitocin da ke asibitinsu sakon gayyata. A sakon, ta musu magana da alheri. A cikin likitocin, akwai wani da matarsa, Helen ta yi jinkirin gayyatarsu. Amma da ta yi tunani kuma ta yi adduꞌa, sai ta tura musu sakon gayyata. Da matar ta ga sakon, sai ta amsa da cewa: “Kina son in zama Mashaidiyar Jehobah ke nan?” Sai Ellaine ta gaya mata cewa taron don kowa ne, ba Shaidun Jehobah kawai ba. Washegari, sai ga matar ta shiga taron, kuma ta shiga da wuri. Ellaine ta yi mamaki, ta ce: “Kafin ma a gama taron, matar ta tura min sakon tes tana cewa: ‘Wannan shi ne karo na farko da na zo taron Shaidun Jehobah. Kuma abin ya yi dadi. Na gode da kika gayyace ni.’”

Ellaine

Likitoci 20 ne Ellaine ta gayyata su zo taron, kuma 16 a cikinsu sun shiga taron da naꞌurorinsu. Ta tuna da abin da manzo Bulus ya fada kuma ta ce: “Na ji dadi sosai da na ‘yi karfin hali’ kuma na yi wa abokan aikina waꞌazin ‘bisharar Allah.’”​—1 Tasalonikawa 2:​2, Littafi Mai Tsarki.

Kowa ya sha wuya sosai don annobar nan. Amma ꞌyanꞌuwanmu a fadin duniya sun ci gaba da yin waꞌazi don su taimaka wa mutane kuma su yi musu taꞌaziyya. Kuma hakan ya taimaka ma ꞌyanꞌuwan su ci gaba da yin farin ciki yayin da suke waꞌazinsu.​—Ayyukan Manzanni 20:35.

a Shaidun Jehobah suna bin dokokin da aka kafa game da yin amfani da bayanan mutum.

b Majagaba na nufin Shaidun Jehobah da suke waꞌazi na cikakken lokaci.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba