Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 193
  • Abin da Littafi Mai Tsarki ya Ce Game da Daniyel?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Littafi Mai Tsarki ya Ce Game da Daniyel?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
  • Wane ne Daniyel
  • Darussa Daga Littafin Daniel
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ka Mai Da Hankali Ga Kalmomin Annabci Na Allah Don Kwanakinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 193
Annabi Daniyel a ramin zakuna yana adduꞌa.

Abin da Littafi Mai Tsarki ya Ce Game da Daniyel

Amsar Littafi Mai Tsarki

Daniyel Bayahude, annabi ne da ya kware sosai, kuma ya yi rayuwa wajen shekaru 600 kafin haihuwar Yesu. Allah ya sa Daniyel ya iya bayyana mafarkai da nuna masa wahayi game da abubuwan da za su faru a nan gaba, kuma ya sa ya rubuta littafin da ke dauke da sunansa a cikin Littafi Mai Tsarki.​—Daniyel 1:17; 2:19.

Wane ne Daniyel

Daniyel ya yi girma a Yahuda, wurin da birnin Urushalima da haikalin Yahudawa yake. A shekara ta 617 kafin haihuwar Yesu, Nebukadnezzar sarki Babila ya ci Urushalima kuma ya kwashi “manyan mutanen kasar” zuwa bauta a Babila. (2 Sarakuna 24:15; Daniyel 1:1) An tafi da Daniyel ma, wanda watakila shi matashi ne a lokacin.

Masu tsaron gidan sarauta suna raka Daniyel da wasu matasa zuwa fadar Babila.

An kai Daniyel da wasu matasa (har da Shadrak da Meshak da kuma Abednego) zuwa fadar sarki a Babila don a yi musu koyarwa ta musamman da zai taimaka musu su rika yi wa gwamnatin Babila aiki. Ko da yake an matsa musu su yi abubuwan da ba su dace ba, Daniyel da abokansa uku sun rike aminci ga Allahnsu, Jehobah. (Daniyel 1:​3-8) Bayan an koyar da su shekara uku, Sarki Nebukadnezzar ya yaba musu don hikimarsu da iyawarsu, ku ya ce “sun fi dukan masu dabo da masu sihiri wadanda suke cikin mulkinsa har sau goma.” Sai ya nada Daniyel da abokansa su rika hidima a fadar sarki.​—Daniyel 1:​18-20.

Bayan shekaru da yawa, watakila saꞌad da Daniyel yake shekara 90, an ce ya zo fadar sarki. Sarki Belshazzar da ke sarautar Babila a lokacin ya gaya wa Daniyel ya bayyana maꞌanar rubutun da wani yatsun hannu ya yi a bango. Da taimakon Jehobah, Daniyel ya bayyana cewa Mediya da Fashiya za su ci Babila a yaki. A daren nan, an ci Babila a yaki.​—Daniyel 5:​1, 13-31.

Daniyel yana bayyana rubutu da ke bango.

Saꞌad da Mediya da Fashiya suke sarauta, an nada Daniyel hakimi kuma Sarki Dariyus ya so ya kara masa matsayi. (Daniyel 6:​1-3) Sauran maꞌaikata masu kishin Daniyel sun kulla su kashe shi ta wurin jefa shi cikin ramin zakuna, amma Jehobah ya cece shi. (Daniyel 6:​4-23) A lokacin da Daniyel ya tsufa sosai, wani malaꞌika ya zo ya karfafa shi sau biyu cewa shi “mai daraja ne sosai.”​—Daniyel 10:​11, 19.

Ka kalli yadda wadannan abubuwa suka faru a wasan kwaikwayo mai sashe biyu mai jigo Daniyel: Mutum Mai Bangaskiya.

Mene ne tarihi ya nuna game da littafin Daniyel?

Daniyel ya ce: Nebukadnezzar ya yi gunki mai girma sosai, ya ba talakawansa umurni su rika bauta wa gunkin, kuma ya jefa wadanda suka yi masa rashin biyayya a cikin wuta.​—Daniyel 3:​1-6.

Abin da tarihi ya nuna: Littafin Encyclopædia Britannica ya ce Nebukadnezzar ya yi manyan gine-gine a Babila “ba don kawai a girmama shi ba amma don a daukaka allolinsa. Ya yi daꞌawa cewa shi ne ke sa mutanen su rika bauta wa allolin.”

A cikin rahotannin Babila na dā an ambata yadda ake kakkashe mutane, har da wadanda wani sarki ya ba da doka a yi. Wani littafi da aka rubuta a lokacin sarautar Nebukadnezzar ya bayyana irin hukuncin da ake yi wa maꞌaikata da suka ki daraja allolin Babila. Littafin ya ce: “Ka hallaka su, ka kona, ka gasa su, . . . a tandan mai gashi . . . Ka sa wutan ya yi zafi sosai don ya kashe su.”a

Daniyel ya rubuta: Sarki Nebukadnezzar ya yi fahariya don gine-ginen da ya yi.​—Daniyel 4:​29, 30.

Wani tubali da aka tono a Babila da aka rubuta sunan Nebukadnezzar a jiki

Abin da tarihi ya nuna: “Abubuwan da Nebukadnezzar ya rubuta game da kansa sun nuna cewa yana ganin shi sarki ne mai girma mai adalci da kuma iko sosai.”b Alal misali, wani rubutu da aka yi a wani gini yana dauke da wannan fahariya da Nebukadnezzar ya yi cewa: “Na gina wani bango da tubali da kwalta da ya yi girma kamar tudun da ba za a iya kawar da shi ba . . . Na sa ganuwar Esagila da Babila ta yi karfi don mutane su tuna da sarautata har abada.”c An rubuta sunan Nebukadnezzar a jikin tubali da yawa da aka tono a Babila.

Daniyel ya rubuta: Sarki Belshazzar ya ba Daniyel “matsayi na uku a cikin masu mulkin kasar” Babila.​—Daniyel 5:​1, 13-16.

Wannan dutse da aka tono daga shekara ta 550 kafin haihuwar Yesu ya ambata Sarki Nabonidus da dansa Belshazzar

Abin da tarihi ya nuna: Wani mutum mai suna Nabonidus ne sarki a lokacin da abubuwan da aka rubuta a Daniyel sura 5 suka faru. Amma Nabonidus bai yi yawancin sarautarsa a Babila ba, ya yi a Arabia. Wane ne ya yi sarauta a Babila a lokacin da ba ya nan? Wani dan tarihi mai suna Raymond Philip Dougherty a littafinsa Nabonidus and Belshazzar ya bayyana cewa “wani rubuce-rubuce na dā ya ce Nabonidus ya ba Belshazzar dansa na fari mulkin. Belshazzar ne ya yi ayyukan da ya kamata babansa ya yi.” Belshazzar ya ba Daniyel matsayi na uku tun da yake Nabonidus da Belshazzar sun dauki matsayi na farko da na biyu a mulkin.

a Littafin Journal of Biblical Literature, Littafi na 128, Na 2, shafuffuka na 279, 284.

b Littafin nan Babylon​—City of Wonders da Irving Finkel da Michael Seymour suka rubuta, shafi na 17.

c Littafin Archæology and the Bible, da George Barton ya rubuta, shafi na 479.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba