Ta Yaya Zan Iya Tsai da Shawarwari Masu Kyau?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana sosai don mu yanke shawara mai kyau. Zai iya sa mu ‘sami hikima [da] ganewa.’ (Karin Magana 4:5) A wasu batutuwa, Littafi Mai Tsarki yakan gaya mana abin da ya fi dacewa mu yi. A wasu kuma, ja-goranci yake mana don mu iya yanke shawara mai kyau.
A wannan talifin, za mu tattauna
Abubuwan da za su taimaka maka ka tsai da shawara mai kyau
Idan na riga na yanke shawara, ya kamata na canja shi?
Idan na tsai da shawara da bata dace ba kuma ba zan iya koma baya ba fa, yaya zan yi?
Abubuwan da za su taimaka maka ka tsai da shawara mai kyau
Kada ka yi hanzari wajen tsai da muhimmin shawara. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai hankali yakan yi tunani kafin ya fara wani abu.” (Karin Magana 14:15) Idan ka tsai da shawara cikin hanzari, kana iya yin kuskure. Ka dakata ka yi tunani a kan matakin da zai fi maka alheri kafin ka yi zabin.—1 Tasalonikawa 5:21.
Idan za ka tsai da shawara, kada ka bi raꞌayinka ko yadda kake ji a lokacin kawai. Littafi Mai Tsarki ya yi mana gargadi cewa zuciyarmu za ta iya rudin mu. (Karin Magana 28:26; Irmiya 17:9) Alal misali, zai yi mana wuya mu tsai da shawara mai kyau idan muna cikin fushi, ko damuwa, ko mun yi sanyin gwiwa, ko kuma muna fama da gajiya.—Karin Magana 24:10; 29:22.
Ka roki Allah ya ba ka hikima. (Yakub 1:5) Irin wannan adduꞌar yana sa Allah farin ciki kuma zai amsa shi. Shi kamar uba da ke kaunar ꞌyaꞌyan sa ne, ba ya so ya ga mun shiga matsala. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama Yahweh yana ba da hikima, sani da ganewa ma, daga bakinsa suke fitowa.”a (Karin Magana 2:6) Hanya ta musamman da Allah yake ba mu hikimarsa ita ce ta wajen rubutacciyar maganarsa, wato Littafi Mai Tsarki.—2 Timoti 3:16, 17.
Ka yi bincike kafin ka yanke shawara. Kafin ka yanke shawarar da ta dace, kana bukatar ka san gaskiya game da batun. Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘Mai hikima yakan ji ya kara karbar koyarwa.’ (Karin Magana 1:5) A ina za ka sami bayanin da za ka iya dogara da shi?
Ka fara da bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da batun. Mahaliccinmu ya san abin da ya fi dacewa da mu. Don haka, Kalmarsa za ta iya ba mu shawara mafi kyau. (Zabura 25:12) A wasu batutuwa, Littafi Mai Tsarki yakan gaya mana abin da ya kamata mu yi, a matsayin doka ko umurni. (Ishaya 48:17, 18) Amma a wasu batutuwan, Littafi Mai Tsarki ba ya gaya mana abin da za mu yi kai tsaye. A maimakon haka, yakan ba mu kaꞌidodin da za su bi da mu. Hakan yana iya taimaka mana mu tsai da shawara mai kyau, ko da ya bambanta da shawarar wani. Don ka san abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da wani batu, ka yi bincike ta wajen yin amfani da littattafai da kuma talifofin da suke bisa Littafi Mai Tsarki. Akwai su da yawa kuma kyauta a wannan dandalin.b
Amma kafin ka tsai da wasu shawarwari, za ka bukaci ka yi bincike a kan abin da wadanda suka san gaskiyar lamarin suka fada. Alal misali, kafin ka sayi wani abu, musamman idan yana da sada, ya kamata ka yi bincike a kan irin abin, da kuma wanda ya kera shi. Kari ga haka, za ka bincika abin da za ka iya yi idan abin ya lalace da batun dawowa da kayan idan bai biya bukatarka ba. Kuma ya kamata ka tabbatar da cewa abin da za ka saya zai biya maka bukata bisa ga abin da wanda ya kera ya ce.
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan babu shawara, shiri yakan lalace.” (Karin Magana 15:22) Don haka, kafin ka yanke shawara, ka tambayi wadanda suka san gaskiyar lamarin. Alal misali, kafin ka tsai da shawara game da yin jinya, zai dace ka ji daga wurin likita. (Matiyu 9:12) Idan za ka tsai da wasu shawarwarin ma, zai dace ka tambayi wadanda su ma suka taba fuskantar wannan yanayin. Yayin da kake hakan, ka tuna cewa kai ne za ka tsai da wannan shawarar, kuma duk abin da zai biyo baya a kanka yake ba wadanda suka ba ka shawarar ba.—Galatiyawa 6:4, 5.
Ka duba amfanin kowace shawara da kuma kasawarta. Bisa ga abin da ka gano, ka ayyana duka shawarwarin da za ka iya tsai da su, saꞌan nan ka rubuta amfanin da kuma rashin amfanin kowace shawara. Kuma ka yi tunani game da abin da zai biyo baya idan ka yi wannan zabin. (Maimaitawar Shari’a 32:29) Ka tambayi kanka, idan na tsai da wannan shawarar, yaya zai shafe ni da iyalina da kuma sauran mutane? (Karin Magana 22:3; Romawa 14:19) Idan ka yi wa kanka irin tambayar nan, kuma ka bi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, zai taimaka maka ka tsai da shawara mai kyau kuma wadda za ta nuna kauna.
Ka yanke shawara. Wani lokaci shakka yakan sa mu ki tsai da shawara. Amma idan ba mu tsai da shawara ba, zai iya sa wata dama ta wuce mu ko kuma mu tsinci kanmu a wani yanayi marar dadi. Wato da wanda ya ki tsai da shawara da wanda ya tsai da shawarar da bata dace ba, su biyun kusan daya ne. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta tsai da shawara da aikin manomi. Ya ce: “Duk wanda yake jiran iska, ba zai yi shuka ba, duk wanda ya kula da gizagizai, ba zai yi girbi ba.”—Mai-Wa’azi 11:4.
Ban da haka ma, ka tuna cewa ko da shawara mafi kyau ne ka tsai da, hakan ba ya nufin cewa ba za ka fuskanci matsaloli ba. A yawancin lokaci dai, dole mu sadakar da wani abu. Ban da haka ma, abubuwan da ba ka yi tsammani ba za su iya tasowa. (Mai-Wa’azi 9:11) Don haka, ka dai yi iya bincikenka, saꞌan nan ka tsai da shawarar da ka ga cewa shi zai fi maka alheri.
Idan na riga na yanke shawara, ya kamata na canja shi?
Za mu iya canja wasu shawarwarin da muke tsai da su. Kila don yanayinka ya canja, ko ka ga cewa shawarar tana jawo maka wata matsalar da baka zata ba. A irin wannan yanayin, mai yiwuwa abin da zai fi maka alheri shi ne ka sake duba shawarar da ka tsai da kuma ka canja ta. Ka yi wani abin da ka san zai fi kawo maka sakamako mai kyau.
Amma fa, akwai wasu shawarwarin da idan ka tsai da su, ba koma baya. (Zabura 15:4) Alal misali, Allah yana so maꞌaurata su cika alkawarin da suka yi ma juna.c (Malakai 2:16; Matiyu 19:6) Idan matsala ta taso tsakanin mata da miji, su yi iya kokarinsu su sasanta maimakon su rabu ko su kashe aurensu.
Idan na tsai da shawara da bata dace ba kuma ba zan iya koma baya ba fa, yaya zan yi?
Ba wanda bai taba yin kuskure wajen yanke shawara ba. (Yakub 3:2) Wani lokaci mukan yi da na sani, kuma mu ji zuciyarmu tana damun mu. Ba laifi ba ne mutum ya ji hakan ba. (Zabura 69:5) Hakan yana da kyau don zai iya taimaka mana kada mu sake yin irin wannan kuskuren! (Karin Magana 14:9) Amma Littafi Mai Tsarki ya ce, kada mu bar zuciyarmu ta yi ta damun mu har abin ya yi yawa domin zai iya sa mu sanyin gwiwa har ma ya shafi tunaninmu. (2 Korintiyawa 2:7)d Littafi Mai Tsarki ya ce, “Yahweh mai jinkai ne, mai alheri kuma.” (Zabura 103:8-13) Don haka, idan ka tsai da shawara marar kyau, wanda kuma ba za ka iya canjawa ba, ka dauki darasi kuma ka yi iya kokarinka don ka kyautata yanayin da kake ciki yanzu.
a Yahweh ko kuma Jehobah shi ne sunan Allah bisa ga Littafi Mai Tsarki.—Zabura 83:18.
b Za ka iya yin amfani da wurin neman abubuwa da ke jw.org ka yi bincike. Don ka yi hakan, ka rubuta kalmar ko kuma kalmomin da suka danganci shawarar da kake so ka tsai da a wurin, sai ka bincika. A dandalin nan, akwai shawarwari game da batutuwa da dama da aka dauko daga Littafi Mai Tsarki. Kari ga haka, za ka iya neman kalmomin da kake so a sashen da ake kira “Bible Words Index” da ke fassarar New World Translation of the Holy Scriptures na turanci.
c Nufin Allah shi ne mata da miji su zauna tare dukan rayuwarsu. Allah bai ba maꞌaurata dama su kashe aurensu kuma su sake yin aure ba sai dai idan daya daga cikinsu ya yi zina. (Matiyu 19:9) Idan kana samun matsala a aurenka, Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka san yadda za ka magance matsalar cikin kauna da kuma hikima.
d Don karin bayani, ka duba talifin da ya ce “Idan Zuciyata Tana Damu Na, Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Min?”