Mene ne Baibul Ya Ce Game da Yin Abokantaka?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Abokai na kwarai za su taimaka mana mu yi farin ciki kuma mu yi nasara a rayuwa. Ban da haka ma, za su iya taimaka mana mu zama mutanen kirki. Kari ga haka, abokai za su iya taimaka ma juna su kasance da halaye masu kyau.—Karin Magana 27:17.
Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa zai dace mu zabi abokanmu da kyau. Duk da haka, ya ce idan muka zabi abokai marar kirki, za su bata halayenmu. (Karin Magana 13:20; 1 Korintiyawa 15:33) Irin wadannan abokan za su iya sa mutum ya yanke shawara marar kyau ko su sa mutum ya soma yin abubuwan da ba su dace ba.
A talifin nan za mu tattauna
Ta yaya za mu gane abokin kirki?
Littafi Mai Tsarki ya ce wadanda za mu kulla abota da su ba sai lallai wadanda raꞌayinmu ya zo daya ba. Alal misali, Zabura 119:63 ta ce: “Ni abokin dukan masu tsoronkaa ne, abokin dukan masu kiyaye kaꞌidodinka.” Kun ga irin abokan da marubucin zaburar nan ya zaba? Ya ce ya zabi masu tsoron Allah, wadanda suke bin kaꞌidodinsa.
Littafi Mai Tsarki ya gaya mana halayen da ya kamata abokin kirki ya kasance da su. Ga wasu cikinsu:
“Aboki na kwarai yana nuna kauna a koyaushe, kuma shi danꞌuwa ne da ke ba da taimako a lokacin damuwa.”—Karin Magana 17:17, New World Translation.
“Akwai abokan da sukan yi abokantaka kawai, amma akwai irin abokin da ya fi danꞌuwa aminci.”—Karin Magana 18:24.
Wadannan ayoyin sun nuna mana cewa abokin kirki yana da aminci da kauna da alheri da kuma karimci. Abokin kirki danꞌuwa ne da za mu dangana a gare shi ya taimaka mana saꞌad da muke cikin wata matsala. Ban da haka ma, irin wannan abokin zai zama da karfin halin ja mana kunne idan muna yin abin da bai dace ba ko kuma muna so mu tsai da shawara marar kyau.—Karin Magana 27:6, 9.
Wadanne misalan abokan kirki ne Littafi Mai Tsarki ke dauke da su?
Littafi Mai Tsarki na dauke da misalan abokai wadanda shekarunsu ba daya ba, ba su fito daga wuri daya ba, alꞌadunsu ba daya ba kuma matsayinsu ba daya ba. Bari mu bincika misalai uku daga cikinsu.
Rut da Naomi. Rut surkuwar Naomi ce kuma Naomi ta girme Rut sosai. Kari ga haka, alꞌadar Rut da Naomi ba daya ba. Duk da haka, su abokan juna ne kuma sun kaunaci juna sosai.—Rut 1:16.
Dauda da Jonathan. Ko da yake mai yiwuwa Jonathan ya girme Dauda da shekaru 30, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Dauda da Jonathan sun ‘so’ juna sosai.—1 Samaꞌila 18:1.
Yesu da manzanninsa. Yesu yana da iko a kan manzanninsa don shi ne malaminsu da shugabansu. (Yohanna 13:13) Duk da haka, Yesu bai rena su ba, a maimakon haka, ya kulla abota da su. Kuma duk wanda yake bin koyarwarsa, abokinsa ne. Ya ce: “Amma ina ce da ku abokai gama na gaya muku dukan abin da na ji daga wurin Ubana.”—Yohanna 15:14, 15.
Shin mutum zai iya zama abokin Allah?
E, zai yiwu mutane su zama aminan Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah “yana amincewa da mai gaskiya a zuci.” (Karin Magana 3:32) Wato abokan Allah su ne wadanda suke yin gaskiya, suke girmama shi kuma suke kokari su yi rayuwa da ta jitu da kaꞌidodinsa. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya kira mai amincin nan Ibrahim abokin Allah.—2 Tarihi 20:7; Ishaya 41:8; Yakub 2:23.
a Mahallin wannan zaburar ya nuna cewa “tsoronka” da aka ambata a wurin yana nuni ne ga Allah.