Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 180
  • Me Zai Taimaka Mana Mu Kasance da Halin Sa Zuciya ko Bege?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Zai Taimaka Mana Mu Kasance da Halin Sa Zuciya ko Bege?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
  • Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai sa mu kasance da raꞌayin da ya dace?
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya yi wa dukan ꞌyan Adam Alkawarinsa?
  • Ka Ci Gaba da Karfafa Begenka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Dalilan Kasancewa da Bege a 2023—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
    Karin Batutuwa
  • Ka Yi Sauraron Jehobah Da Bege Da Gaba Gaɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Littafi Mai Tsarki Ya Ce Za Mu Ji Dadin Rayuwa
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 180
Wata mata da take a tsaye tana kallon waje da sa zuciya.

Me Zai Taimaka Mana Mu Kasance da Halin Sa Zuciya ko Bege?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki ya ce Allah yana so ya ba mu “sa zuciya da rayuwa ta nan gaba.”a (Irmiya 29:11) Wani dalilin da ya sa Allah ya ba mu Littafi Mai Tsarki shi ne “mu zama da sa zuciya ta wurin . . . karfafawa wadanda Rubutacciyar Maganar Allah sukan ba mu.” (Romawa 15:4) Kamar yadda za mu gani, shawara da ke cikin Littafi Mai Tsarki za ta taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace game da matsalolinmu na yau da kullum. Kuma alkawarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki zai sa mu kasance da bege.

A shafin nan za ka ga

  • Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai sa mu kasance da raꞌayin da ya dace?

  • Ta yaya Littafi Mai Tsarki ke sa dukan ꞌyan Adam su kasance da bege?

  • Ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka yi magana game da sa zuciya

Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai sa mu kasance da raꞌayin da ya dace?

Ta wajen gaya mana abubuwan da za mu iya yi don mu inganta rayuwarmu, Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace. Ga wasu misalai.

  • Ka nemi shawara daga Littafi Mai Tsarki. Zabura 119:105 ta ce: “Maganarka fitila ce ga kafafuna, haske kuma ga hanyata.” Ana iya yin abubuwa biyu da wuta mai haske sosai. Za ta iya haskaka abin da ke gabanmu da kuma abin da ke da nisa. Hakazalika, shawarwarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu san yadda za mu bi da matsalolin da muke fuskanta a yanzu. Kuma zai sa mu kasance da raꞌayin da ya dace yau da kullum. Koyarwa da ke cikin Littafi Mai Tsarki zai karfafa mu kuma ya ‘farantar da zuciyarmu.’ (Zabura 19:​7, 8) Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki ya ba da karin haske game da nufin Allah don duniya da kuma ꞌyan Adam. Wannan begen zai sa mu rika farin ciki kuma mu kasance da gamsuwa.

  • Ka bar mutane su taimaka maka. Idan muna cikin wani yanayi mai wuya, za mu iya ganin kamar zai fi mu guji ꞌyanꞌuwanmu ko kuma abokai. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa bai kamata mu yi hakan ba, don zai sa mu dauki matakan da ba su dace ba. (Karin Magana 18:1) ꞌYanꞌuwa da abokanka za su taimaka maka ka yi tunanin kirki. Za su iya ba ka shawarwari game da yadda za ka magance wani mawuyacin yanayi. (Karin Magana 11:14) Kari ga haka, za su iya karfafa mu don mu iya jimre yanayi da muke ciki har lokacin da abubuwa za su canja.​—Karin Magana 12:25.

  • Ka yi adduꞌa ga Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Danka wa Yahweh damuwarka, shi kuwa zai lura da kai, ko kadan ba zai bar masu adalci su jijjigu ba.”b (Zabura 55:22) Shi ya sa ake kiran Jehobah “Allah mai kawo sa zuciya.” (Romawa 15:13) Za ka iya gaya masa ‘dukan damuwarka,’ da tabbaci cewa zai taimaka maka. (1 Bitrus 5:7) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zai mai da ku cikakku, zai kafa ku, zai kuma karfafa ku.”​—1 Bitrus 5:10.

  • Ka bar matsaloli su karfafa begenka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wadanda suka saurare [Allah] za su zauna lafiya. Za su kuwa zauna rai a kwance, babu tsoron azaba.” (Karin Magana 1:33) Saꞌad da mahaukaciyar guguwa ta lalace gidan wata mata mai suna Margaret a Ostiraliya, ta yi hasara dukiyoyinta da yawa. Maimakon ta rika bakin ciki, ta koyi darasi cewa mutum zai iya yin hasara dukiyarsa dare daya. Bayan abin da ya faru da ita, ta kuduri niyya cewa za ta mai da hankali ga abubuwan da suka fi muhimmanci. Abubuwan su ne, iyalinta da abokanta da dangantakarta da Allah da kuma alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki.​—Zabura 37:34; Yakub 4:8.

Mene ne Littafi Mai Tsarki ya yi wa dukan ꞌyan Adam Alkawarinsa?

Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa ꞌyan Adam za su yi farin ciki a nan gaba kuma duniya za ta zama aljanna. Kuma hakan zai faru nan ba da dadewa ba. Matsalolin da ꞌyan Adam suke fuskanta a yau sun nuna cewa muna “kwanakin karshe” na zamanin nan. (2 Timoti 3:​1-5) Nan ba da dadewa ba, Allah zai dauki mataki kuma ya kawar da rashin adalci da kuma shan wahala. Zai yi amfani da Mulkinsa don ya cim ma wadannan abubuwan. (Daniyel 2:44; Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 11:15) Yesu yana maganar gwamnatin nan saꞌad da ya yi adduꞌa cewa: “Mulkinka ya zo, bari a yi nufinka a cikin duniya.”​—Matiyu 6:​9, 10.

An fadi nufin Allah dalla-dalla a cikin Littafi Mai Tsarki. Ga wasu matsalolin da Mulkin Allah zai kawar:

  • Ba za a kara yunwa ba. “Kasa ta ba da amfaninta.”​—Zabura 67:6.

  • Ba za a kara cututtuka ba. “Ba mazaunin kasar da zai ce, ‘Ina ciwo.’ ”​—Ishaya 33:24.

  • Ba za a kara mutuwa ba. Allah “zai share musu dukan hawaye daga idanun [ꞌyan Adam]. Babu sauran mutuwa, ko bakin ciki, ko kuka, ko azaba. Gama abubuwan dā sun bace.”​—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​3, 4.

a Muna sa rai samun abin da muke so kuma mukan gaskata cewa za mu samu abin. Bege kuma yana iya zama abin da muke sa ran samu.

b Jehobah ko kuma Yahweh ne sunan Allah kamar yadda aka nuna a Littafi Mai Tsarki.​—Zabura 83:18.

Ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka yi magana game da sa zuciya

Ayuba 5:16: “Talakawa su sami sa zuciya.”

Abin da hakan yake nufi: Wadanda suke ganin ba a kula da su a zamanin nan za su iya kasance da tabbaci cewa Allah zai kula da su idan suka nemi taimakonsa.

Zabura 27:14: “Sa zuciya ga Yahweh, ka karfafa, ka kasance da ƙarfin zuciya! I, sa zuciya ga Yahweh!”

Abin da hakan yake nufi: Idan muka dogara ga Jehobah, za mu samu karfafa. Ba zai yasar da wadanda suka dogara gare shi ba.

Zabura 62:5: “Ya raina, nemi kwanciyar rai daga wurin Allah kadai, . . . a gare shi ne sa zuciyarka take.”

Abin da hakan yake nufi: Wadanda suke dogara ga Allah kuma suke jimre matsaloli, suna da tabbaci cewa zai kawar da matsalolinsu a lokacin da ya dace.

Karin Magana 20:22: “Kada ka ce, ‘Zan rama mugunta,’ amma ka jira Yahweh, shi zai cece ka.”

Abin da hakan yake nufi: Idan mutum ya bata mana rai, za mu guji yin ramako idan muka dogara ga Jehobah. Yana da iko kuma yana so ya cece mu kuma ya kawo karshen matsalolin da muke fama da su.

Ibraniyawa 6:19: “Wannan sa zuciyar nan tamu tabbatacciya ce mai tsayar da hankalinmu, ba tare da jin tsoro ko yin shakka ba.”

Abin da hakan yake nufi: Kamar yadda anka take rike jirgin ruwa saꞌad da ake iska, begen cewa Allah zai sāka mana zai sa mu rage damuwa kuma ya taimaka mana mu natsu mu rika tunanin kirki. Ban da haka zai sa mu ci gaba da kasancewa da bege. Bege zai kuma sa mu jimre da matsaloli.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba