Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Yuni p. 32
  • Raga Iri-iri na Kamun Kifi a Zamanin Dā

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Raga Iri-iri na Kamun Kifi a Zamanin Dā
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Makamantan Littattafai
  • Ya Yaƙi Tsoro da Kuma Shakka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Yesu Ya Je Wajen Masu Kama Kifi
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Yuni p. 32

BATU MAI BAN SHA’AWA DAGA LITTAFI MAI TSARKI

Raga Iri-iri na Kamun Kifi a Zamanin Dā

Wasu almajiran Yesu sun yi sanaꞌar kamun kifi. (Mar. 1:​16-20) Sun yi amfani da ragar kamun kifi a tekun Galili.

Don a saƙa raga, akan yi amfani da igiyoyin saƙa. Akwai raga na kamun ƙananan kifaye, akwai kuma na kamun manyan kifaye. A ragar kamun ƙananan kifaye, ana ɗaɗɗaura ƙananan ƙarfe ko duwatsu a jikin ragar don ta yi nauyi ta iya nitsewa cikin ruwa. A ragar kamun manyan kifaye kuma, ana ɗaɗɗaura wani abu kamar ƙaramar ƙwarya a jikin ragar kuma ba sa nitsewa cikin ruwa.

A lokacin, ragar kamun kifi na da tsada sosai. Duwatsu cikin ruwa ko kuma nauyin kifayen da aka kama za su iya tsintsinke ragar. (Luk. 5:6) Littafi Mai Tsarki ya ce akwai lokacin da Yakub da Yohanna suke “gyaran ragarsu.” Mai yiwuwa sun yi hakan da tsinken saƙa da kuma zare. (Mat. 4:21) A duk lokacin da masu kamun kifi suka kama kifi, sai su yi gyara idan da bukata. Luka ya kuma rubuta cewa masu kamun kifi “suna wanke ragarsu” don su cire datti. (Luk. 5:2) Bayan haka, sai su shanye ragar don ya bushe kada ya ruɓe.—Ezek. 47:10.

Yesu ya gaya wa mutane da sun san yadda ake kamun kifi su zo su zama “masu jawo mutane.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba