Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Oktoba pp. 24-29
  • Mu Riƙa Yin Adduꞌa a Madadin Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mu Riƙa Yin Adduꞌa a Madadin Mutane
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ME YA SA YA KAMATA MU RIƘA YIN ADDUꞌA A MADADIN WASU?
  • WAƊANDA SUKE BUKATAR ADDUꞌOꞌINMU
  • SAꞌAD DA MUKE ADDUꞌA A MADADIN ꞌYANꞌUWANMU ƊAYA BAYAN ƊAYA
  • MU KASANCE DA RAꞌAYIN DA YA DACE SAꞌAD MUKE ADDUꞌA
  • Ka Rika Yin Addu’a don Ka Kusaci Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Gatan da Muke da Shi Na Yin Addu’a
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Yadda Za Ka Inganta Adduꞌarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Oktoba pp. 24-29

TALIFIN NAZARI NA 43

WAƘA TA 41 Allah Ka Ji Roƙona

Mu Riƙa Yin Adduꞌa a Madadin Mutane

“ Kuna yi wa juna adduꞌa . . . Adduꞌar mai adalci tana da ƙarfin aiki da iko sosai.”—YAK. 5:16.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da ya sa yake da muhimmanci mu riƙa yin adduꞌa a madadin mutane, da kuma shawarwari a kan yadda za mu yi hakan.

1. Ta yaya muka san cewa adduꞌoꞌinmu suna da muhimmanci ga Jehobah?

YIN adduꞌa babban gata ne. Jehobah ya ba wa malaꞌiku wasu ayyukan da za su yi. (Zab. 91:11) Ya kuma ba wa Ɗansa Yesu ayyuka masu muhimmanci. (Mat. 28:18) Amma bai ba wa kowa damar saurara da kuma amsa adduꞌoꞌi ba. Abu ne da shi da kansa yake yi. Jehobah Allah “mai jin adduꞌoꞌi” yana sauraran mu da kansa, kuma yana amsa adduꞌoꞌinmu.—Zab. 65:2.

2. Ta yaya manzo Bulus ya kafa misali mai kyau na yin adduꞌa a madadin wasu mutane?

2 Ko da yake za mu iya gaya wa Jehobah abubuwan da suke damunmu, zai dace mu riƙa yin adduꞌa ma a madadin wasu. Abin da manzo Bulus ya yi ke nan. Alal misali, ya yi adduꞌa a madadin ꞌyanꞌuwa da ke ikilisiyar Afisa, kuma ya gaya musu cewa: Nakan yi “adduꞌa dominku.” (Afis. 1:16) Ƙari ga haka, ya yi adduꞌa a madadin mutane ɗaɗɗaya. Alal misali, ya gaya wa Timoti cewa: “Ina gode wa Allah . . . saꞌad da nake tunawa da kai kullum dare da rana cikin adduꞌoꞌina.” (2 Tim. 1:3) Bulus yana da nasa matsaloli da yake bukatar ya yi adduꞌa a kai. (2 Kor. 11:23; 12:​7, 8) Duk da haka, ya yi adduꞌa a madadin wasu mutane.

3. Mene ne zai iya hana mu yin adduꞌa a madadin mutane?

3 A wasu lokuta, za mu iya manta mu yi adduꞌa a madadin mutane. Me ya sa? Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Sabrinaa ta ce: “Muna da ayyukan yi da yawa a rayuwa. Matsalolinmu za su iya yi mana yawa, har su sa mu riƙa yin adduꞌa don kanmu kawai.” Idan kai ma kana fama da hakan, talifin nan zai taimaka maka. Za ka ga, na ɗaya, dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu yi adduꞌa a madadin wasu. Na biyu, shawarwari a kan yadda za mu yi hakan.

ME YA SA YA KAMATA MU RIƘA YIN ADDUꞌA A MADADIN WASU?

4-5. Me ya sa adduꞌoꞌin da muke yi a madadin wasu suke da “ƙarfin aiki da iko sosai”? (Yakub 5:16)

4 Yin adduꞌa a madadin wasu yana da “ƙarfin aiki da iko sosai.” (Karanta Yakub 5:16.) Shin, adduꞌarmu za ta iya canja yanayin da wanda muke yi wa adduꞌa yake ciki? Ƙwarai kuwa. Alal misali, Yesu ya san cewa Bitrus zai yi musun sanin sa. Saboda haka, ya gaya masa cewa: “Na yi adduꞌa a madadin ka domin kada ka rasa bangaskiyarka.” (Luk. 22:32) Ƙari ga haka, Bulus ya san cewa idan muka yi adduꞌa a madadin mutane, hakan zai iya canja yanayin da suke ciki. Saꞌad da aka sa shi a kurkuku a Roma, ya rubuta wa Filimon cewa: “Ina sa rai cewa ta wurin adduꞌoꞌinku Allah zai mayar da ni gare ku.” (Fil. 22) Kuma abin da ya faru ke nan. Ba da daɗewa ba an saki Bulus, kuma ya ci-gaba da yin waꞌazi.

5 Babu shakka, hakan ba ya nufin cewa adduꞌoꞌinmu za su tilasta wa Jehobah ya yi wani abu. Yana lura da yadda bayinsa suke damuwa a kan abin da suke adduꞌa a kai, kuma a wasu lokuta, yakan yi abin da suka roƙa. Sanin hakan zai sa mu yi adduꞌa game da wani batu da dukan zuciyarmu kuma mu bar kome a hannun Jehobah.—Zab. 37:5; ka kuma duba 2 Kor. 1:11.

6. Yaya yin adduꞌa a madadin wasu zai sa mu ji game da su? (1 Bitrus 3:8)

6 Yin adduꞌa a madadin wasu zai sa mu zama masu “tausayin juna.” (Karanta 1 Bitrus 3:8.) Idan muna tausaya wa mutane, za mu lura da famar da suke yi, kuma mu kasance da niyyar taimaka musu. (Mar. 1:​40, 41) Wani dattijo mai suna Michael ya ce: “Idan ina adduꞌa a kan bukatun mutane, nakan fahimci yanayin da suke ciki da kyau kuma hakan na sa in ƙara ƙaunar su. Ina ji kamar muna fama tare, ko da yake ba za su sani ba.” Wani dattijo kuma mai suna Richard ya ce: “Idan muna adduꞌa a madadin mutane, hakan yana sa mu so taimaka musu.” Ya ƙara da cewa: “Idan muka yi wani abu don mu taimaka wa wanda muka yi adduꞌa a madadin sa, kamar muna taimaka wajen amsa adduꞌar da muka yi ne.”

7. Ta yaya yin adduꞌa a madadin wasu zai taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace game da namu matsalolin? (Filibiyawa 2:​3, 4) (Ka kuma duba hotunan.)

7 Yin adduꞌa a madadin wasu zai sa mu kasance da raꞌayin da ya dace game da namu matsalolin. (Karanta Filibiyawa 2:​3, 4.) Da yake muna rayuwa a duniyar da ke ƙarƙashin ikon Shaiɗan Iblis, kowannenmu na fama da nasa matsaloli. (1 Yoh. 5:19; R. Yar. 12:12) Idan muna adduꞌa a madadin mutane kowane lokaci, hakan zai tuna mana cewa ‘ꞌyanꞌuwanmu masu bi koꞌina a duniya, su ma suna shan’ irin wahalar da muke sha. (1 Bit. 5:9) Wata majagaba mai suna Katherine ta ce: “Yin adduꞌa a madadin wasu yana tuna min cewa su ma suna fama da matsaloli. Hakan yana sa ba na mai da hankali sosai a kan matsalolina.”

Hotuna: ꞌYanꞌuwa maza da mata da suke fama da nasu matsalolin, suna yin adduꞌa a madadin wasu. Na 1. Wata ƙaramar yarinya tana zaune a kan gadonta tana adduꞌa; a wani ƙaramin hoto akwai wani iyali da ke kwalekwale suna barin gidansu don ambaliyar ruwa ya shiga gidansu. Na 2. Iyalin da ke wannan ƙaramin hoton suna adduꞌa; akwai wani ƙaramin hoto da ya nuna wani ɗanꞌuwa a kurkuku. Na 3. Ɗanꞌuwan da ke kurkuku a ƙaramin hoton da muka gani ɗazu yana adduꞌa; akwai wani ƙaramin hoto da ya nuna wata ꞌyarꞌuwar da ta tsufa tana kwance a asibiti. Na 4. ꞌYarꞌuwar da aka nuna a ƙaramin hoton, tana adduꞌa; akwai wani ƙaramin hoto da ya nuna yarinyar da aka nuna a hoton na farko, tana zaune ita kaɗai a aji, sauran yaran kuma suna bikin zagayowar ranar haifuwa.

Yin adduꞌa a madadin wasu zai sa mu kasance da raꞌayin da ya dace game da namu matsalolin (Ka duba sakin layi na 7)d


WAƊANDA SUKE BUKATAR ADDUꞌOꞌINMU

8. Su waye ne za mu iya yin adduꞌa a madadinsu?

8 Su waye ne za mu iya yin adduꞌa a madadinsu? Za mu iya yin adduꞌa a madadin waɗanda suke rashin lafiya, da yaran da ake matsa musu su yi abin da bai dace ba a makaranta, da kuma waɗanda suke shan wahala don sun tsufa. ꞌYanꞌuwanmu da yawa suna fama da tsanantawa daga hannun danginsu ko gwamnati. (Mat. 10:​18, 36; A. M. 12:5) Wasu ꞌyanꞌuwanmu sun gudu sun bar gidajensu domin rikicin siyasa. Wasu kuma suna fama don wani balaꞌi ya auku. Mai yiwuwa ba za mu san dukan ꞌyanꞌuwan nan ba. Amma idan muka yi adduꞌa a madadinsu, muna bin umurnin da Yesu ya bayar ke nan saꞌad da ya ce “ku riƙa ƙaunar juna.”—Yoh. 13:34.

9. Me ya sa muke bukatar mu yi adduꞌa a madadin ꞌyanꞌuwan da suke mana ja-goranci da matansu?

9 Za mu iya yin adduꞌa a madadin waɗanda suke mana ja-goranci. Hakan ya ƙunshi Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu, da mataimakansu, da Kwamitin da Ke Kula da Reshen Ofishinmu, da dattawan da suke ja-goranci a rassan ofisoshinmu, da masu kula da daꞌira, da dattawan ikilisiya, da kuma bayi masu hidima. Da yawa daga cikin ꞌyanꞌuwan nan suna fama da matsaloli, duk da haka suna aiki tuƙuru don su taimaka mana. (2 Kor. 12:15) Alal misali, wani mai kula da daꞌira mai suna Mark ya ce: “Ɗaya daga cikin matsalolin da nake fama da su shi ne, zama da nisa daga wurin da iyayena da suka tsufa suke. Su biyun ba su da lafiya. Ko da yake ꞌyarꞌuwata da mijinta suna taimaka wajen kula da su, ina yawan damuwa cewa ba na iya zuwa in taimaka musu yadda nake so.” Ba za mu iya sanin dukan abubuwan da ꞌyanꞌuwan nan suke fama da su ba, amma zai dace mu riƙa yin adduꞌa a madadinsu. (1 Tas. 5:​12, 13) Za mu kuma iya yin adduꞌa a madadin matansu, domin su ma suna taimaka wa mazajensu su iya yin aikinsu da kyau.

10-11. Shin, Jehobah yana jin adduꞌoꞌin da muke yi a madadin ꞌyanꞌuwanmu ko da ba mu ambata sunayensu ba? Ka bayyana.

10 Kamar yadda muka tattauna, muna adduꞌa a madadin ꞌyanꞌuwa dabam-dabam. Alal misali, za mu iya roƙan Jehobah ya taimaka wa ꞌyanꞌuwan da suke kurkuku, ko kuma ya ƙarfafa waɗanda suka rasa wani da suke ƙauna, ko da ba mu ambata sunan su ba. Wani dattijo mai suna Donald ya ce, “Akwai ꞌyanꞌuwa da yawa da suke fama da matsaloli, shi ya sa a wasu lokuta mukan yi adduꞌa a madadin dukansu gabaki ɗaya.”

11 Jehobah yana jin irin adduꞌoꞌin nan kuwa? Ƙwarai kuwa! Ba mu san takamaiman abin da ꞌyanꞌuwanmu suke fama da shi ba. Saboda haka, zai dace mu yi adduꞌa a madadin dukansu. (Yoh. 17:20; Afis. 6:18) Yin irin wannan adduꞌar zai nuna cewa muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu.—1 Bit. 2:17.

SAꞌAD DA MUKE ADDUꞌA A MADADIN ꞌYANꞌUWANMU ƊAYA BAYAN ƊAYA

12. Ta yaya lura da yanayin da mutane suke ciki zai taimaka mana mu san abin da za mu yi adduꞌa a kai?

12 Ka lura. Ban da yin adduꞌa a madadin ꞌyanꞌuwa gabaki ɗaya, yana da kyau mu ambata sunayen ꞌyanꞌuwa ɗaya bayan ɗaya saꞌad da muke yin adduꞌa. Shin, akwai wani a ikilisiyarku da ke fama da ciwo mai tsanani? Akwai yaron da ya yi sanyin gwiwa don ana matsa masa a makaranta ya yi abin da bai dace ba? Akwai wani mahaifi ko mahaifiya da ita kaɗai ce take koya wa yaranta yadda za su ƙaunaci Jehobah? (Afis. 6:4) Idan kana lura da yanayin da mutane suke ciki, za ka ƙara ƙauna da kuma tausaya musu, kuma hakan zai sa ka yi adduꞌa a madadin su.b—Rom. 12:15.

13. Ta yaya za mu iya yin adduꞌa a madadin waɗanda ba mu taɓa haɗuwa da su ba?

13 Ka ambata sunayen mutane saꞌad da kake yin adduꞌa a madadin su. Za mu iya ambata har da sunayen waɗanda ba mu taɓa haɗuwa da su ba. Alal misali, akwai ꞌyanꞌuwanmu maza da mata da aka sa a kurkuku a ƙasashe kamar Crimea, da Iritiriya, da Rasha, da kuma Singapo. Za mu iya samun sunayen waɗannan ꞌyanꞌuwan a dandalin jw.org.c Wani mai kula da daꞌira mai suna Brian ya ce: “Nakan rubuta sunan wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa da aka sa a kurkuku kuma in riƙa maimaita sunan. Hakan yana sa in tuna da sunan a lokacin da nake adduꞌa.”

14-15. Me zai taimaka mana mu san ainihin abin da za mu roƙi Jehobah a madadin ꞌyanꞌuwanmu?

14 Ka roƙi Jehobah ainihin abin da kake so ya yi wa mutanen. Ɗanꞌuwa Michael, da aka ambata ɗazu ya ce: “Yayin da nake karanta labaran ꞌyanꞌuwan da aka sa a kurkuku a jw.org, nakan yi tunanin yadda zan ji da ni ne a cikin kurkukun. Da ni ne, na san cewa zan damu game da matata. Kuma zan so in tabbatar cewa tana nan lafiya kuma tana samun kulawar da ya kamata. Hakan yana sa in san ainihin abin da zan yi adduꞌa a kai, saꞌad da nake yin adduꞌa a madadin ꞌyanꞌuwa masu aure da aka sa a kurkuku.”—Ibran. 13:3.

15 Idan muka yi tunani game da irin rayuwar da ꞌyanꞌuwanmu suke yi a kurkuku, hakan zai sa mu san ainihin abin da za mu iya yin adduꞌa a kai a madadin su. Alal misali, za mu iya roƙan Jehobah ya sa masu gadin kurkuku su nuna musu alheri. Kuma ya sa hukumomin gwamnati su bar ꞌyanꞌuwanmu su bauta masa a sake. (1 Tim. 2:​1, 2) Za mu iya roƙan Jehobah ya sa labarin ꞌyanꞌuwan da suka riƙe amincinsu a kurkuku ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. Ko kuma ya sa waɗanda suke ganin halaye masu kyau na ꞌyanꞌuwanmu a kurkuku su so su saurari saƙonmu. (1 Bit. 2:12) Za mu iya yin hakan saꞌad da muke yin adduꞌa a madadin ꞌyanꞌuwanmu da suke fama da wasu matsaloli dabam. Idan muna lura da yanayin da ꞌyanꞌuwanmu suke ciki, da ambata sunayensu saꞌad da muke adduꞌa, da kuma faɗan ainihin abin da muke so Jehobah ya yi musu, hakan zai nuna cewa muna ƙaunar su sosai.—1 Tas. 3:12.

MU KASANCE DA RAꞌAYIN DA YA DACE SAꞌAD MUKE ADDUꞌA

16. Ta yaya za mu kasance da raꞌayin da ya dace saꞌad da muke yin adduꞌa? (Matiyu 6:8)

16 Kamar yadda muka gani, adduꞌarmu za ta iya canja yanayin da ꞌyanꞌuwanmu suke ciki. Amma muna bukatar mu kasance da raꞌayin da ya dace. Saꞌad da muke adduꞌa, kada mu ga kamar muna gaya wa Jehobah wani abin da bai sani ba, ko mu yi ƙoƙarin gaya masa yadda zai bi da yanayin. Jehobah ya san abin da bayinsa suke bukata kafin mu ko waɗanda muke musu adduꞌa ma su sani. (Karanta Matiyu 6:8.) To me ya sa muke bukatar mu yi adduꞌa a madadin mutane? Ban da abubuwan da aka riga aka ambata a talifin nan, yin adduꞌa a madadin mutane yana nuna cewa mun damu da su, kuma muna ƙaunar su. Ƙari ga haka, Jehobah yana farin ciki idan ya ga cewa muna nuna ƙauna kamar yadda shi yake yi.

17-18. Ka ba da misalin da ya nuna muhimmancin yin adduꞌa a madadin ꞌyanꞌuwanmu.

17 Ko da adduꞌoꞌin da muka yi, ba su canja yanayin da ꞌyanꞌuwanmu suke ciki ba, sun nuna cewa muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu, kuma Jehobah yana lura da hakan. Alal misali, a ce wasu iyaye suna da yara biyu wato, ta mace da namiji. Sai yaron ya soma rashin lafiya, kuma yarinyar ta roƙi mahaifinsu ta ce: “Don Allah ka taimaka wa ɗanꞌuwana, bai da lafiya sosai!” Mahaifin ya san game da yanayin da yaron yake ciki. Yana ƙaunarsa kuma yana iya ƙoƙarinsa don ya kula da shi. Amma zai yi farin ciki sosai don yadda ꞌyarsa ta nuna cewa tana ƙaunar ɗanꞌuwanta kuma ta roƙe shi ya taimaka masa.

18 Abin da Jehobah yake so mu yi ke nan. Yana so mu riƙa nuna cewa mun damu da juna kuma mu riƙa yin adduꞌa a madadin junanmu. Yayin da muke yin hakan, muna nuna cewa ba mu damu da kanmu kawai ba, amma mun damu da ꞌyanꞌuwanmu kuma muna ƙaunarsu sosai. Jehobah yana lura da hakan. (2 Tas. 1:3; Ibran. 6:10) Ƙari ga haka, kamar yadda muka tattauna, a wasu lokuta adduꞌoꞌinmu za su iya canja yanayin da ꞌyanꞌuwanmu suke ciki. Saboda haka, bari mu yi iya ƙoƙarinmu mu riƙa yin adduꞌa a madadin juna.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa adduꞌoꞌin da muke yi a madadin wasu suke da “ƙarfin aiki da iko sosai”?

  • Me ya sa yake da muhimmanci mu yi adduꞌa a madadin ꞌyanꞌuwanmu maza da mata?

  • Me zai taimaka mana mu san ainihin abin da za mu roƙi Jehobah ya yi wa waɗanda muke adduꞌa a madadin su?

WAƘA TA 101 Mu Riƙa Hidima da Haɗin Kai

a An canja wasu sunayen.

b Ka kalli bidiyon nan Takeshi Shimizu: Jehobah Mai “Jin Adduꞌoꞌi” Ne a dandalin jw.org/ha

c Don samun sunayen ꞌyanꞌuwanmu da aka sa a kurkuku ka shiga jw.org/ha, sai ka nemi, “Shaidun Jehobah da Aka Tsare a Kurkuku Saboda Imaninsu​—Bisa ga Kasa.”

d BAYANI A KAN HOTO: ꞌYanꞌuwa maza da mata da ke fama da nasu matsalolin suna adduꞌa a madadin wasu.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba