TALIFIN NAZARI NA 36
WAƘA TA 103 Jehobah Ya Yi Tanadin Makiyaya
Ka ‘Kira Dattawa’
“Sai ya kira dattawan jamaꞌar masu bin Yesu.”—YAK. 5:14.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu tattauna dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu nemi taimakon dattawa a lokacin da muke bukata.
1. Ta yaya Jehovah ya nuna cewa yana ƙaunar bayinsa kuma yana kula da su?
JEHOBAH yana ƙaunar dukan bayinsa. Yana kula da su kamar yadda makiyayi yake kula da tumakinsa. Ya ba da makaɗaicin ɗansa domin su, kuma ya yi tanadin dattawa don su kula da su. (A. M. 20:28) Allah yana so dattawa su bi da bayinsa cikin ƙauna. Dattawa suna bin ja-gorancin Yesu ta wurin ƙarfafa ꞌyanꞌuwa maza da mata da kuma taimaka musu su riƙe amincinsu ga Jehobah.—Isha. 32:1, 2.
2. Bisa ga Ezekiyel 34:15, 16, su waye ne Jehobah yake taimaka wa?
2 Jehobah ya damu da dukan bayinsa, amma ya fi damuwa da waɗanda suke shan wahala. Wasu suna shan wahala ne domin sun yi zunubi kuma Jehobah yana amfani da dattawa ya taimaka musu. (Karanta Ezekiyel 34:15, 16.) Amma Jehobah yana so dukanmu mu nemi taimako a lokacin da muke bukata. Idan mun ga cewa muna bukatar taimakon Jehobah, zai dace mu roƙe shi ya taimaka mana. Amma ba shi ke nan ba. Yana so mu nemi taimakon “makiyaya da masu koyarwa” a ikilisiya.—Afis. 4:11, 12.
3. Ta yaya dukanmu za mu amfana daga yadda Jehobah yake amfani da dattawa?
3 A wannan talifin, za mu tattauna yadda Jehobah yake amfani da dattawa wajen taimaka wa waɗanda dagantakarsu da Jehobah ta yi sanyi. Za mu amsa waɗannan tambayoyi: A wane lokaci ne za mu nemi taimakon dattawa? Me ya sa zai dace mu yi hakan? Kuma ta yaya dattawa suke taimaka mana? Mai yiwuwa, dangantakarmu da Jehobah na da ƙarfi yanzu kuma ba ma bukatar taimakon dattawa. Duk da haka, wannan talifin zai taimaka mana mu ƙara godiya don yadda Jehobah yake amfani da dattawa, kuma zai taimaka mana mu san abin da za mu yi idan muna bukatar taimakonsu.
A WANE LOKACI NE MUKE BUKATAR MU ‘KIRA DATTAWA’?
4. Ta yaya muka san cewa Yakub 5:14-16, 19, 20, suna magana ne game da wanda dangantakarsa da Jehobah ta yi sanyi? (Ka kuma duba hotunan.)
4 Yakub ya bayyana yadda Jehobah yake amfani da dattawa ya taimaka mana. Ya ce: “Ko akwai wani mai rashin lafiya a cikinku? Sai ya kira dattawan jamaꞌar masu bin Yesu.” (Karanta Yakub 5:14-16, 19, 20.) Yakub yana magana ne game da wanda yake bukatar ya gyara dagantakarsa da Jehobah. Me ya sa muka ce hakan? Domin Yakub ya ce mai rashin lafiyar ya kira dattawa ba likita ba. Ƙari ga haka, ya ce marar lafiyar zai warke idan an gafarta masa zunubansa. Amma, akwai alaƙa tsakanin yadda likita yake bi da mai rashin lafiya, da yadda dattawa suke bi da wanda ya yi zunubi. Idan muna rashin lafiya, muna zuwa wurin likita mu gaya masa yadda muke ji, kuma mu bi shawarwarin da ya ba mu. Haka ma, idan muka yi zunubi kuma muna so mu sake kusantar Jehobah, muna bukatar mu tattauna da dattawa, mu gaya musu damuwarmu, kuma mu bi shawarwarin da suka ba mu daga Littafi Mai Tsarki.
Idan ba mu da lafiya muna zuwa wurin likita; haka ma idan bangaskiyarmu ta soma sanyi muna zuwa wurin dattawa don su taimaka mana (Ka duba sakin layi na 4)
5. Ta yaya za mu san cewa dangantakarmu da Jehobah ta soma sanyi?
5 A Yakub sura 5, Yakub ya ƙarfafa mu mu nemi taimakon dattawa a duk lokacin da muke ganin dangantakarmu da Jehobah ta soma sanyi. Muna bukatar mu yi hakan kafin dangantakarmu da Jehobah ta yi tsami! Wajibi ne mu gaya wa kanmu gaskiya. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa idan ba mu mai da hankali ba, za mu ga kamar muna da dangantaka mai kyau da Jehobah, alhali kuma ba mu da shi. (Yak. 1:22) Wasu Kiristoci a Sardis a ƙarni na farko sun yi irin wannan kuskuren, kuma Yesu ya gaya musu cewa ba sa yin abin da zai sa Jehobah farin ciki. (R. Yar. 3:1, 2) Ta yaya za mu san ko muna da dangantaka mai kyau da Jehobah? Hanya ɗaya ita ce yin tunani a kan yadda muka ji a lokacin da muka yi baftisma, da yadda muke ji a yanzu. (R. Yar. 2:4, 5) Za mu iya mu tambayi kanmu cewa: ‘Ina jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki da yin bimbini kamar yadda na saba yi? Ina fasa taro ba gaira ba dalili, kuma ina shiri kafin in halarci taro? Ina zuwa waꞌazi da ƙwazo kamar yadda nake yi a dā, ko na fi mai da hankali a kan kayan duniya da kuma nishaɗi?’ Idan amsarmu e ce ga ɗaya daga cikin tambayoyin nan, hakan na iya nufin cewa dangantakarmu da Jehobah ta soma sanyi. Kuma idan ba mu ɗau mataki ba, dangantakarmu da shi za ta yi tsami. Idan muna ganin kamar ba za mu iya ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah da kanmu ba, ko kuma mun riga mun yi abin da Jehobah ba ya so, zai dace mu nemi taimakon dattawa.
6. Mene ne waɗanda suka yi zunubi mai tsanani suke bukatar su yi?
6 Gaskiyar ita ce, waɗanda suka yi zunubi mai tsanani, wanda zai iya sa a cire mutum daga cikin ikilisiya suna bukatar su sami dattawa. (1 Kor. 5:11-13) Duk wanda ya yi zunubi mai tsanani yana bukatar taimako don ya gyara dangantakarsa da Jehobah. Jehobah zai gafarta mana zunubanmu idan mun tuba da gaske. (A. M. 26:20) Hanya ɗaya da za mu nuna hakan ita ce gaya wa dattawa abin da muka yi.
7. Su waye ne kuma suke bukatar su nemi taimakon dattawa?
7 Ba kawai waɗanda suka yi zunubi mai tsanani ne dattawa suke taimaka wa ba. Suna kuma taimaka wa waɗanda bangaskiyarsu ta soma sanyi. (A. M. 20:35) Alal misali, za ka iya ga kamar ba za ka iya shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau ba. Musamman idan kafin ka soma bauta wa Jehobah kana shan kwayoyi, ko yin lalata ko kuma kallon batsa. Idan haka ne, kar ka ji tsoron neman taimako. Za ka iya tattaunawa da wani dattijo da ka san cewa zai saurare ka da kyau. Zai bayyana maka abubuwan da za ka yi don ka ci-gaba da shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau. Kuma zai tuna maka cewa Jehobah zai yi farin ciki idan ka ci-gaba da yi masa biyayya. (M. Wa. 4:12) Idan ka damu domin kana fama da shaꞌawoyi marasa kyau, dattawa za su tuna maka cewa Jehobah yana son yadda ka nemi taimako. Hakan ya nuna cewa kana da sauƙin kai, kuma kana so ka sa Jehobah farin ciki.—1 Kor. 10:12.
8. Shin, muna bukatar mu gaya wa dattawa kowane kuskuren da muka yi?
8 Ba kowane kuskuren da muka yi ba ne za mu gaya wa dattawa ba. Alal misali, a ce ka yi wa wani a ikilisiya bakar magana, ko ka yi magana cikin fushi. Maimakon ka je ka gaya wa dattawa, zai dace ka bi shawarar da Yesu ya bayar cewa ka je ka sami ɗanꞌuwan ko ꞌyarꞌuwar kuma ku sasanta. (Mat. 5:23, 24) Ƙari ga haka, za ka iya yin nazari a kan yadda za ka ƙara kasancewa da sauƙin kai, da haƙuri da kuma kame kanka a nan gaba. Amma idan ka yi iya ƙoƙarinka kuma kun gagara sasantawa, za ka iya nemi taimakon dattawa. Saꞌad da Yudiya da Sintiki suka sami matsala, kuma suka gagara warwarewa, manzo Bulus ya gaya wa wani ɗanꞌuwa ya taimaka musu. Mu ma a yau, za mu iya zuwa wurin wani dattijo ya taimaka mana.—Filib. 4:2, 3.
ME YA SA MUKE BUKATAR MU KIRA DATTAWA?
9. Idan muka yi zunubi mai tsanani, me ya sa bai kamata mu bar kunya ta hana mu gaya wa dattawa abin da muka yi ba? (Karin Magana 28:13)
9 Idan muka yi zunubi mai tsanani, ko idan muna ganin ba za mu iya shawo kan wata kasawa ba, muna bukatar bangaskiya da ƙarfin zuciya don mu nemi taimakon dattawa. Kada mu yarda kunya ta hana mu neman taimakonsu. Me ya sa? Domin Jehobah ya ba mu dattawa ne don su taimaka mana mu ci-gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da shi. Saboda haka, idan muka nemi taimakonsu, muna nuna cewa mun dogara ga Jehobah kuma muna so mu yi masa biyayya. Ƙari ga haka, muna nuna cewa muna bukatar taimakon Jehobah don yin abin da ya dace. (Zab. 94:18) Idan muka yi zunubi, muna da tabbaci cewa Jehobah zai gafarta mana in mun gaya wa dattawa abin da muka yi kuma muka daina.—Karanta Karin Magana 28:13.
10. Me zai faru idan muka yi ƙoƙarin ɓoye zunubanmu?
10 Idan muka gaya wa dattawa zunubin da muka yi, Jehobah zai gafarta mana kuma za mu sake kusantar sa. Amma idan ba mu yi hakan ba, yanayinmu zai daɗa muni. Saꞌad da Sarki Dauda ya yi ƙoƙari ya ɓoye zunuban da ya yi, hakan ya jefa shi cikin damuwa sosai. (Zab. 32:3-5) Kamar yadda wanda ya ji rauni yake bukatar jinya don kada ciwon ya ƙara tsanani, haka ma wanda ya yi zunubi mai tsanani yake bukatar ya nemi taimakon dattawa da gaggawa don kada dangantakarsa da Jehobah ta lalace. Jehobah ba ya son hakan ya faru, shi ya sa ya ce mu nemi taimakon dattawa. Yana amfani da su wajen taimaka mana mu sake zama abokansa.—Isha. 1:5, 6, 18.
11. Mene ne kuma zai iya faruwa idan ba mu gaya wa dattawa game da zunubin da muka yi ba?
11 Wani abu kuma shi ne, idan muka ɓoye zunubin da muka yi, hakan zai iya shafan wasu mutane. Za mu iya hana ruhun Jehobah kasancewa a ikilisiya, kuma mu tayar wa ꞌyanꞌuwa hankali. (Afis. 4:30) Saboda haka, idan mun san cewa wani a ikilisiya ya yi zunubi mai tsanani, mu ƙarfafa shi ya je ya gaya wa dattawa. Idan ya ƙi, zai dace mu je mu gaya musu da kanmu. Domin idan ba mu yi hakan ba, mu ma muna da alhakin zunubin ke nan. (L. Fir. 5:1) Ƙaunarmu ga Jehobah ce take sa mu gaya wa dattawa game da zunubi mai tsanani da wani ya yi. Yin hakan zai kāre ꞌyanꞌuwa a ikilisiya, kuma zai taimaka wa wanda ya yi zunubin ya sake kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah.
TA YAYA DATTAWA SUKE TAIMAKA MANA?
12. Ta yaya dattawa suke taimaka wa waɗanda suka yi zunubi?
12 Littafi Mai Tsarki ya gaya wa dattawa su taimaka wa waɗanda suke bukatar su gyara dangantakarsu da Jehobah. (1 Tas. 5:14) Idan ka yi zunubi, dattawa za su yi maka tambayoyi don su fahimce ka da kyau. (K. Mag. 20:5) Mai yiwuwa, ba zai yi maka sauƙi ka tattauna da dattawa ba, ƙila kana jin kunyar gaya musu abin da ya faru. Amma za ka taimaka musu idan ka gaya musu matsalolin da kake fama da su. Kada ka damu cewa wataƙila za ka faɗi wani abin da ba daidai ba. (Ayu. 6:3) Dattawa ba za su yi saurin yanke hukunci don abin da ka faɗa ba. A maimakon hakan, za su saurare ka da kyau don su fahimci batun, kafin su ba ka shawara daga Littafi Mai Tsarki. (K. Mag. 18:13) Dattawa sun san cewa taimaka wa mutum yana ɗan ɗaukan lokaci. Saboda haka, a wasu lokuta suna bukatar su tattauna da mutumin fiye da sau ɗaya.
13. Idan dattawa suka yi adduꞌa a madadinmu kuma suka ba mu shawarwari daga Littafi Mai Tsarki, ta yaya hakan zai taimaka mana? (Ka kuma duba hotunan.)
13 Dattawa ba za su so ka ji kamar taka ta ƙare don zunubin da ka yi ba. A maimakon hakan, za su yi adduꞌa a madadinka. Adduꞌarsu tana da “ƙarfin aiki da iko sosai.” Za ka ji ka samu sauƙi da ƙarfafa fiye da yadda kake tsammani. Ban da haka ma, idan mutum ya gaya wa dattawa abin da ya yi, za su taimaka masa ta wajen “shafe shi da mai a cikin sunan Ubangiji.” (Yak. 5:14-16) Wannan “mai” ita ce gaskiyar da ke Kalmar Allah. Saboda haka, dattawa za su tattauna wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki da kai da za su ƙarfafa ka, kuma su taimaka maka ka sake kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah. (Isha. 57:18) Shawarwarin da za su ba ka za su taimaka maka ka ci-gaba da yin abin da Jehobah yake so. Ta wurin taimakonsu, za ka ji kamar Jehobah yana gaya maka cewa: “Ga hanyar, yi tafiya a cikinta.”—Isha. 30:21.
Dattawa suna amfani da Littafi Mai Tsarki wajen taimaka da kuma ƙarfafa mu (Ka duba sakin layi na 13-14)
14. Bisa ga Galatiyawa 6:1, ta yaya dattawa suke taimaka wa wanda ya yi laifi? (Ka kuma duba hotunan.)
14 Karanta Galatiyawa 6:1. Idan Kirista yana “cikin yin laifi,” yana yin abin da Jehobah ba ya so ke nan. Mai yiwuwa ya tsai da shawarar da ba ta dace ba ne, ko kuma ya yi zunubi mai tsanani ne. Idan hakan ya faru, ƙauna za ta sa dattawa su komo da shi kan hanya. Suna yin hakan cikin “tawaliꞌu, a hankali kuma.” Ana iya amfani da kalmar Girkanci da aka fassara zuwa “komo” a ayar nan wajen kwatanta yadda likita yake saita ƙashin da ya karye don ya warke da kyau. Likitan da ya ƙware zai yi ƙoƙari ya saita ƙashin a hanyar da ba zai yi wa mutumin zafi sosai ba. Haka ma, idan dattawa suna son su taimaka wa wanda ya yi laifi, za su yi ƙoƙari don kada su ƙara damuwan da yake ciki. Littafi Mai Tsarki ya kuma gaya musu cewa su mai da hankali ‘kada maimakon dawo da ɗanꞌuwansu, su ma su faɗi cikin jarraba.’ Yayin da suke taimaka wa wanda ya yi zunubin, ya kamata dattawa su riƙa tuna cewa su ma ajizai ne. Saboda haka, za su mai da hankali sosai don kada su ga kamar sun fi mutumin da suke taimaka wa. A maimakon hakan, su kasance da sauƙin kai da kuma tausayi.—1 Bit. 3:8.
15. Me ya sa yake da kyau mu nemi taimakon dattawa idan muna da wata matsala?
15 Jehobah ya koya wa dattawa yadda za su iya riƙe sirrinmu. Kuma sun koyi yadda za su riƙa ba da shawarwari daga Littafi Mai Tsarki maimakon gaya mana raꞌayinsu. Ƙari ga haka, sun koyi cewa suna bukatar su ci-gaba da taimaka mana mu shawo kan matsalolinmu. Saboda haka, muna bukatar mu yarda da dattawa kuma mu nemi taimakonsu. (K. Mag. 11:13; Gal. 6:2) Kowane dattijo yana da nashi baiwa, kuma wasu sun daɗe da zama dattawa kafin wasu. Amma, za mu iya zuwa wurin kowane dattijo idan muna da matsala. Yana da muhimmanci mu tuna cewa, ba zai dace mu riƙa zuwa wurin dattawa ɗaya bayan ɗaya muna yi kamar muna neman shawara, alhali, magoya baya muke nema. Idan muka yi hakan, za mu zama kamar mutanen da suke so a gaya musu abin da suke so su ji kawai, maimakon gaskiyar da Jehobah yake koyarwa daga cikin Kalmarsa. (2 Tim. 4:3) Idan mun sami wani dattijo kuma muka gaya masa game da wata matsala, zai iya tambayar mu ko mun tattauna da wasu dattawa, da shawarar da suka bayar. Amma, ko da mun tambayi wasu dattawa ko aꞌa, sanin kasawarsa zai sa dattijon ya nemi taimakon wasu dattawa kafin ya ba da shawara.—K. Mag. 13:10.
HAKKIN KOWANNENMU
16. Wane hakki ne kowannenmu yake da shi?
16 Ko da yake dattawa suna taimaka mana kuma suna ba mu shawarwari a lokacin da muke da wata matsala, ba za su gaya mana abin da za mu yi ba. Kowannenmu ne yake da hakkin nuna kowace rana cewa yana ƙaunar Jehobah, kuma yana so ya faranta masa rai ta wurin abubuwan da yake faɗa da kuma yi. Da taimakon Jehobah, za mu tsai da shawarwari masu kyau kuma mu riƙe amincinmu. (Rom. 14:12) Saboda haka, maimakon gaya mana abin da za mu yi, dattawa suna nuna mana raꞌayin Jehobah da ke Littafi Mai Tsarki. Idan muka bi shawarar da suka ba mu, za mu kasance da raꞌayin Jehobah kuma mu yanke shawarwari masu kyau.—Ibran. 5:14.
17. Mene ne Jehobah yake so mu yi?
17 Muna godiya sosai ga Jehobah don yadda yake kula da mu kamar yadda makiyayi yake yi! Jehobah ya turo Yesu Kristi wanda shi ne “makiyayi mai kyau,” ya ba da fansa don mu sami damar yin rayuwa har abada. (Yoh. 10:11) Ƙari ga haka, Jehobah ya ba mu dattawa da suke kula da mu a ikilisiya kamar yadda ya yi alkawari. Ya ce: “Zan ba ku makiyaya masu zuciya irin tawa, waɗanda za su bi da ku cikin hikima da fahimta.” (Irm. 3:15) Saboda haka, idan mun ga kamar bangaskiyarmu ta soma sanyi, ko kuma muna bukatar mu gyara dangantakarmu da Jehobah, kada mu yi jinkirin neman taimakon dattawa. Idan muka yi hakan, za mu ga yadda Jehobah yake amfani da su wajen taimaka mana.
WAƘA TA 31 Ka Bi Allah!