Za Mu Iya Kawo Ƙarshen Yaƙi da Tashin Hankali?
Mutane suna yaƙi domin dalilai da yawa. Wasu suna yaƙi domin siyasa, ko tattalin arziki, ko kuma don su ƙwato ꞌyancinsu. Wasu kuma suna yaƙi domin suna son abubuwa masu daraja da wasu ƙasashe suke da su, kamar maꞌadinai da itatuwa da kuma mai. A yawancin lokaci tashin hankali na faruwa ne saboda bambancin addini da kuma ƙabila. Mene ne mutane suke yi don a daina yaƙi kuma a sami zaman lafiya? Shin mutane za su iya sa a daina yin yaƙi?
Drazen_/E+ via Getty Images
GINA TATTALIN ARZIKI
Dalilinsu na yin hakan: Inganta rayuwar mutane. Hakan zai rage ko kuma ya kawo ƙarshen rashin daidaituwa a batun tattalin arziki wanda shi ne ɗaya daga cikin manyan abubuwa da ke jawo tashin hankali.
Abin da ya sa yin hakan na da wuya: Hakan zai bukaci gwamnatoci su canja yadda suke kashe kuɗi. A 2022, an kimanta cewa gwamnatoci a faɗin duniya sun kashe dala biliyan 34.1 a kan abubuwan da za su inganta rayuwar mutane. Amma hakan kashi 0.4 ne na yawan kuɗin da suka kashe a harkokin sojoji a shekarar.
Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya mai suna António Guterres ya ce: “Muna kashe kuɗi sosai wajen taimaka ma waɗanda yaƙi ya shafe su fiye da yadda muke kashe kuɗi don mu yi abubuwan da za su hana yaƙi, su kuma kawo zaman lafiya.”
Abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa: Gwamnatoci da ƙungiyoyin duniya za su iya taimaka wa talakawa, amma ba za su iya cire talauci gabaki-ɗaya ba.—Maimaitawar Shariꞌa 15:11; Matiyu 26:11.
DIFLOMASIYA
Dalilinsu na yin hakan: Hana ko kuma kawo ƙarshen jayayya cikin salama, ta wurin tattaunawa ko kuma yin yarjejeniya da zai amfani ɓangarori biyun.
Abin da ya sa yin hakan na da wuya: Ɓangarori biyun ko kuma ɗaya daga cikinsu zai iya ƙin tattaunawa ko kuma ya ƙi yin abin da ya kamata ya yi don su cim ma yarjejeniya. Kuma yana yi wa mutane sauƙi su karya yarjejeniyar zaman lafiya.
Wani mutum mai suna Raymond F. Smith ya faɗa a littafin nan American Diplomacy cewa: “Ba a kullum ne ake cim ma zaman lafiya ta wurin diflomasiya ba. Ɓangarori biyun za su iya yin yarjejeniya marar kyau da za ta iya jawo yaƙi mai tsanani a gaba.”
Abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa: Mutane su “nemi salama.” (Zabura 34:14) Amma mutane da yawa a yau “marasa aminci, . . . masu ƙin yarda da juna, . . . masu cin amana” ne. (2 Timoti 3:1-4, New World Translation) Irin halayen nan ne suke hana shugabannin siyasa kawo ƙarshen tashin hankali.
KAWAR DA MAKAMAI
Dalilinsu na yin hakan: Rage ko kuma hallaka musamman makaman nukiliya ko makamai masu guba ko kuma kwayoyin cuta da ake amfani da su a matsayin makamai.
Abin da ya sa yin hakan na da wuya: Ƙasashe ba sa yarda su kawar da makamansu domin suna tsoro cewa yin hakan zai sa su rasa ƙarfinsu da kuma abin da za su kāre kansu da shi. Ko da ƙasashe sun kawar da dukan makamansu, ba za su iya kawo ƙarshen dalilin da ya sa mutane suke yaƙi ba.
Littafin nan “Securing Our Common Future: An Agenda for Disarmament” ya ce: “Gwamnatoci da yawa da suka yi alkawarin kawar da makamansu bayan 1991, ba su cika alkawarinsu ba, har da alkawarin da suka yi na rage haɗari, da tashin hankali a duk duniya, don a sami zaman lafiya.”
Abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa: Mutane su zubar da makamansu kuma “su mai da takubansu garmar noma.” (Ishaya 2:4) Amma don a kawo ƙarshen yaƙi, mutane suna bukatar su yi fiye da hakan, domin daga zuciya ne mugunta take somawa.—Matiyu 15:19.
ƘUNGIYOYIN HAƊIN GWIWA
Dalilinsu na yin hakan: Ƙasashe sukan yarda su taimaka ma wasu ƙasashe su yaƙi abokan gābansu. A ganinsu, abokin gābansu ba zai so ya soma yaƙi da su ba domin idan ya yi hakan, zai yi yaƙi da sauran ƙasashen.
Abin da ya sa yin hakan na da wuya: Barazanar ramuwa ba ta tabbatar da zaman lafiya. Ba a kullum ne ƙasashe suke cika alkawarin da suka yi ba, kuma ba sa cim ma yarjejeniya a kan lokaci da kuma yadda za su mayar da martani ga abokan gābansu.
Littafin nan “Encyclopedia Britannica” ya ce: “Ko da yake Majalisar Ɗinkin Duniya ta dā da ta yanzu sun yi ƙoƙari sosai wajen taimaka wa gwamnatoci su kafa ƙungiyoyin haɗin gwiwa, amma hakan bai hana yaƙe-yaƙe ba.”
Abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa: Ya fi kyau idan mutane da yawa suka yi aiki tare don su taimaka wa juna. (Mai-Waꞌazi 4:12) Amma gwamnatoci da ƙungiyoyin ꞌyanꞌadam ba za su iya kawo zaman lafiya da salama na har abada ba. “Kada ka dogara ga shugabanni, ko ga ɗan Adam wanda ba ya ceto. Da numfashinsa ya bar shi sai ya koma ƙasa inda ya fito, a ranar nan dukan shirye-shiryensa su zama banza.”—Zabura 146:3, 4.
Duk da cewa ƙasashe da yawa suna yin iya ƙoƙarinsu don a sami zaman lafiya, ana ci-gaba da yin yaƙe-yaƙe.