2-8 GA MARIS
ISHAYA 41-42
Waƙa ta 8 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. ‘Kada Ku Ji Tsoro’
(minti 10)
Jehobah zai naɗa wani “daga gabas” da zai sa mutane su yi rawar jiki (Ish 41:2, 5; ip-2-E 20 sakin layi na 10)
Bayin Jehobah ba za su ji tsoro ba (Ish 41:10; ijwbv-E talifi na 5 sakin layi na 4-7)
Jehobah zai taimake su (Ish 41:13)
DON BIMBINI: Wane amfani ne Kiristoci a yau suke samuwa daga annabcin da ke Ishaya 41?—w16.07 shafi na 18 sakin layi na 4-5.
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
Ish 41:8—Ta yaya Jehobah ya nuna cewa Ibrahim amininsa ne? (w01-E 10/1 20 sakin layi na 3)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) Ish 42:1-13 (th darasi na 11)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 3) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Mutumin ya karɓi takardar gayyata zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, kuma ya ce zai halarci taron. (lmd darasi na 6 batu na 4)
5. Fara Magana da Mutane
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka gayyaci wani danginku zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, kuma ka yi amfani da dandalin jw.org don ka nuna masa wurin da za a yi taron a yankinsa. (lmd darasi na 3 batu na 5)
6. Ka Bayyana Imaninka
(minti 5) Jawabi. ijwbq talifi na 60—Jigo: Me Zai Taimaka Mini Na Daina Tsoron Mutuwa? (th darasi na 1)
Waƙa ta 19
7. Za A Soma Gayyatar Mutane Zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu Ranar Asabar, 7 ga Maris
(minti 5) Jawabi da mai kula da hidima zai yi. Ka gaya wa ꞌyanꞌuwa shirye-shiryen da aka yi don waꞌazi na musamman da jawabi na musamman da kuma Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Ka ƙarfafa ꞌyanꞌuwa su ƙara ƙwazo a waꞌazi a watan Maris da Afrilu. Masu shela za su iya yin hidimar majagaba na ɗan lokaci, kuma su ba da awa 15.
8. Abubuwan da Ƙungiyarmu Ta Cim Ma na watan Maris
(minti 10) Tattaunawa.
Ku kalli BIDIYON. Sai ka yi tambayoyin da aka yi a bidiyon.
9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) lfb darasi na 66-67