Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb23 Yuli p. 11
  • Za Ku Iya Sa Iyalinku Su Daɗa Farin Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ku Iya Sa Iyalinku Su Daɗa Farin Ciki
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Makamantan Littattafai
  • Shawarar Hikima ta Uwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Yadda Iyalinka Za Ta Zauna Lafiya
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ƙauna Ce Take Sa Jehobah Ya Yi Mana Horo
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • “Ka Girmama Mahaifinka da Mahaifiyarka”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
mwb23 Yuli p. 11
Hotuna: Hotunan da ke cikin bidiyon nan “Ku Sa Iyalinku Farin Ciki.” 1. Wasu yara biyu suna kallon iyayensu da suke cin kek. 2. Yaran suna dariya a lokacin ibadarsu ta iyali. 3. Daya yarinyar tana kula da mahaifiyarsu mara lafiya da take kwance a kan kujera.

RAYUWAR KIRISTA

Za Ku Iya Sa Iyalinku Su Daɗa Farin Ciki

Jehobah yana so iyalai su riƙa farin ciki. (Za 127:​3-5; M. Wa 9:9; 11:9) Amma za mu iya daina farin ciki don matsalolin duniyar nan da kuma kurakuran waɗanda suke iyalanmu. Mene ne kowa a iyalin zai iya yi don ya daɗa sa iyalin farin ciki?

Ya kamata miji ya riƙa girmama matarsa. (1Bi 3:7) Ya riƙa kasancewa tare da ita. Bai kamata miji ya so matarsa ta yi abin da ya fi ƙarfinta ba. Yakan nuna godiya don abubuwan da take yi masa da kuma iyalin. (Kol 3:15) Yakan nuna yana ƙaunarta kuma yana yaba mata.​—K. Ma 31:​28, 31.

Mace takan nemi hanyoyin taimaka wa mijinta. (K. Ma 31:12) Takan yi wa mijinta biyayya kuma ta bi shawarar da yake bayarwa. (Kol 3:18) Takan yi masa magana cikin ladabi kuma tana maganar kirki game da shi.​—K. Ma 31:26.

Ya kamata iyaye su riƙa kasancewa tare da yaransu. (M.Sh 6:​6, 7) Suna gaya musu cewa suna ƙaunarsu. (Mt 3:17) Sukan nuna musu ƙauna da kuma bi da su cikin basira saꞌad da suke yi musu horo.​—Afi 6:4.

Ya kamata yara su girmama iyayensu kuma su riƙa yi musu biyayya. (K. Ma 23:22) Su riƙa gaya wa iyayensu abubuwan da suke tunani da kuma yadda suke ji. Su riƙa bin shawarar iyayensu kuma su yi musu ladabi.​—K. Ma 19:20.

KU KALLI BIDIYON NAN KU SA IYALINKU FARIN CIKI, SAI KU AMSA TAMBAYA TA GABA:

Mene ne kowannensu ya yi don su riƙa farin ciki a iyalin?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba