RAYUWAR KIRISTA
Abubuwan da Za Su Taimaka Mana a Littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!
Babu shakka kuna jin daɗin yin amfani da bidiyoyi da tambayoyin da ke littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, ko ba haka ba? Sashen “Wasu Sun Ce” da “Maƙasudi” da “Ka Bincika” kuma fa? Waɗanne abubuwa ne kuma a littafin nan za su iya taimaka maka sa’ad da kake nazari da mutane?—Mt 28:19, 20.
Bidiyoyi da Sauti da Kuma Talifofi: Idan ka fi jin daɗin amfani da littattafan da aka buga don yin nazari, ta yaya za ka iya samun bidiyoyi da talifofin da ke ciki a wuri ɗaya? Ka buɗe littafin a wayarka, ka zaɓi ɗaya daga cikin sassa huɗu da ke wurin. A ƙarshen jerin darussan, za ka iya samun dukan bidiyoyi da sauti da kuma talifofin sashen da ka zaɓa. (Ka duba hoto na 1.)
Yadda za ka zaɓi “Printed Edition”: Idan kana amfani da wayarka don yin nazari da wani, za ka iya yin amfani da “Printed Edition” duk lokacin da kake so. Sa’ad da ka buɗe wani darasi, ka danna alamar da ke da ɗigo uku a saman shafin sai ka zaɓi “Printed Edition.” Hakan zai iya taimaka maka ka riƙa ganin yadda jigon darasin yake da alaƙa da sauran bayanan da ke ciki. Idan kana so ya koma yadda yake da farko, ka sake danna alama mai ɗigo uku sai ka zaɓi “Digital Edition.”
“Na Shirya?”: Akwatunan da ke cikin “Na Shirya” a ƙasan darussan da ke sashe na huɗu na littafin sun bayyana abin da mutum zai yi kafin ya soma yin wa’azi da ’yan’uwa a ikilisiya ko kuma ya yi baftisma. (Ka duba hoto na 2.)
Ƙarin Bayanai: A sashen nan ne ake samun ƙarin bayani game da wasu muhimman batutuwa. Idan kana amfani da “Digital Edition” na littafin, a kowane ƙarshen ƙarin bayani, akwai mahaɗi wato link da zai mai da kai inda kuka tsaya a darasin. (Ka duba hoto na 2.)
Ku tabbata cewa kun kammala littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! da ɗalibanku ko da sun yi baftisma kafin ku kai ƙarshen littafin. Za ka iya ci gaba da ƙirga lokaci da komawa ziyara da kuma nazarin da ka yi da ɗalibin har bayan ya yi baftisma. Idan kai da wani mai shela ne kuka yi nazarin, shi ma zai iya ƙirga lokacin