26 ga Satumba–2 ga Oktoba
1 SARAKUNA 15-16
Waƙa ta 73 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Asa Ya Kasance da Ƙarfin Zuciya, Kai fa?”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
1Sar 16:34—Ta yaya ayar nan ta taimaka mana mu ƙara ba da gaskiya cewa annabcin da Jehobah ya yi zai cika? (w98-E 9/15 21-22)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) 1Sar 15:25–16:7 (th darasi na 5)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 3) Ka bi bayanin da ke yadda za mu soma nazari na musamman. Mutumin ya ba da wata hujja da aka saba bayarwa a yankin. (th darasi na 12)
Komawa Ziyara: (minti 4) Ka soma da bin bayanin da ke yadda za mu soma nazari na musamman. Ka gabatar (amma kar ka kunna) bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? (th darasi na 16)
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5) lff darasi na 07 batu na 6 (th darasi na 6)
RAYUWAR KIRISTA
Ku Zama Sojojin Kristi Masu Karfin Zuciya: (minti 5) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon. Sai ku amsa tambayar nan: Mene ne kuka koya daga labarin Benjamin da Sruthi?
Abubuwan da Ƙungiyarmu ta Cim Ma: (minti 10) Ku kalli bidiyon Abubuwan da Ƙungiyarmu ta Cim Ma na watan Satumba.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lff darasi na 20
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 103 da Addu’a