Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb22 Satumba p. 7
  • Ku Kasance da Ƙarfin Zuciya Sa’ad da Kuke Fama da Rashin Kuɗi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Kasance da Ƙarfin Zuciya Sa’ad da Kuke Fama da Rashin Kuɗi
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Makamantan Littattafai
  • Allahnka Jehobah Yana Daraja Ka!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ku Rika Jira da Hakuri
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Bangaskiyarka Tana da Karfi Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Habakkuk
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
mwb22 Satumba p. 7
Hotuna daga bidiyon “Ku Gina Gidan da Zai Dawwama​—‘Ku Hakura da Abin da Kuke da Shi.’” Hotuna: 1. Ángel tana karanta Littafi Mai Tsarki. 2. Lester da matarsa suna karanta Littafi Mai Tsarki tare.

RAYUWAR KIRISTA

Ku Kasance da Ƙarfin Zuciya Sa’ad da Kuke Fama da Rashin Kuɗi

Rayuwa a kwanakin ƙarshe na da wuya sosai. Yayin da muke gab da ƙarshen zamanin nan matsaloli za su yi ta ƙaruwa. Hakan zai iya sa mu kasa samun wasu abubuwan biyan bukata. (Hab 3:​16-18) Me zai taimaka mana mu zama da ƙarfin zuciya idan muna fama da rashin kuɗi? Wajibi ne mu dogara ga Jehobah, Allahnmu. Ya yi alkawari cewa zai kula da bayinsa kuma zai tanadar mana da abin da muke bukata.​—Za 37:​18, 19; Ibr 13:​5, 6.

Ga abin da za ku iya yi:

  • Ku roƙi Jehobah ya ja-gorance ku, ya ba ku hikima kuma ya taimaka muku.​—Za 62:8

  • Idan aka ba ku aikin da ba ku taɓa yi ba a dā, ku yi haƙuri ku amince da shi.​—g-E 1/10 8-9, akwatuna

  • Ku ci gaba da yin ayyukan ibada kamar su, karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai da halartar taro da kuma yin wa’azi

KU KALLI BIDIYON NAN KU GINA GIDAN DA ZAI DAWWAMA​—“KU HAƘURA DA ABIN DA KUKE DA SHI,” SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne matsaloli ne iyalan da ke bidiyon nan suka fuskanta?

  • Mene ne ya fi muhimmanci a rayuwa?

  • Ta yaya za mu iya taimaka wa waɗanda suke fama da rashin kuɗi?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba