Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb22 Maris p. 13
  • Dukan Jarrabobi Suna da Ranar da Za Su Ƙare

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Dukan Jarrabobi Suna da Ranar da Za Su Ƙare
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Yana Taimaka Mana Saꞌad da Muke Cikin Matsala
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Ci Gaba da Zama Mai Hakuri
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ku Dogara ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Kana Shirye Ka Jira Jehobah da Hakuri?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
mwb22 Maris p. 13
Hotuna: Hoto daga bidiyon “Hadin Kai a Duniya Cike da Nuna Wariya.” 1. ’Yan’uwa masu bakin fata kawai a taron da’ira. 2. Dattawa masu bakin fata da masu farin fata da matansu suna daukan hoto. 3. ’Yan’uwa mata biyu masu launi fata da shekaru dabam-dabam suna wa’azi da amalanke.

RAYUWAR KIRISTA

Dukan Jarrabobi Suna da Ranar da Za Su Ƙare

Jarrabawa takan sa mu sanyin gwiwa, musamman idan sun ƙi ci sun ƙi cinyewa. Dauda ya san cewa wata rana Sarki Saul zai daina taƙura masa kuma zai zama sarki yadda Jehobah ya yi masa alkawari. (1Sam 16:13) Dauda ya kasance da bangaskiya, hakan ya taimaka masa ya dogara ga Jehobah cewa zai canja yanayinsa.

Sa’ad da muke fuskantar jarrabawa, basira da hikima da kuma yin tunanin kirki za su iya taimaka mana mu canja yanayinmu. (1Sam 21:12-14; K. Ma 1:4) Amma, za mu iya ci gaba da fuskantar wasu matsaloli ko da mun yi iya ƙoƙarinmu don mu bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. A irin wannan yanayin, wajibi ne mu kasance da haƙuri kuma mu dogara ga Jehobah. Nan ba da daɗewa ba, zai kawar da dukan matsalolinmu kuma ya “share . . . dukan hawaye” daga idanunmu. (R. Yar 21:4) Ko mun sami sauƙi domin Jehobah ya taimaka mana ko kuma don wasu dalilai, mun sani cewa: Kowace jarrabawa tana da ƙarshe. Kuma hakan yana ba mu ƙarfin gwiwa.

KU KALLI BIDIYON NAN NUNA HAƊIN KAI A DUNIYA CIKE DA NUNA WARIYA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne matsaloli ne wasu Kiristoci suka fuskanci a kudancin Amirka?

  • Ta yaya suka nuna haƙuri da ƙauna?

  • Ta yaya suka ci gaba da mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci?—Fib 1:10

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba