Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb22 Maris p. 9
  • Su Waye Ne Abokanka a Dandalin Sada Zumunta?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Su Waye Ne Abokanka a Dandalin Sada Zumunta?
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Guji Hadarin da Ke Dandalin Sada Zumunta Na Intane
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Dandalinmu na Intane—Ku Yi Amfani da Shi Wajen Yin Nazari da Iyalinku ko Kuma Ku Kaɗai
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Ka Zabi Abokan Kirki
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Yana da Muhimmanci Mutum Ya Sami Dimbin Abokai a Shafin Sada Zumunta?
    Tambayoyin Matasa
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
mwb22 Maris p. 9

LIVING AS CHRISTIANS

Su Waye Ne Abokanka a Dandalin Sada Zumunta?

Aboki mutum ne da ka shaƙu da shi kuma kuna ƙauna da daraja juna sosai. Alal misali, Jonathan da Dauda sun soma abokantaka na kud da kud bayan da Dauda ya kashe Goliyat. (1Sam 18:1) Dukansu suna da halaye masu kyau, kuma abin da ya sa suka zama abokai ke nan. Saboda haka, ƙulla abokantaka ya dangana ne da sanin mutumin sosai. Sanin mutum yakan ɗauki lokaci kuma muna bukatar mu ƙoƙarta sosai. Amma a dandalin sada zumunta, yana da sauƙi mutane su zama abokai nan da nan. A dandalin sada zumunta, mutane sukan shirya abin da za su faɗa yadda zai yi wuya mutum ya gane ko su waɗanne irin mutane ne, sai su ɓoye ainihin halinsu. Saboda haka, yana da kyau ka san irin mutane da za su zama abokanka. Idan wani da ba ka sani ba yana so ya zama abokinka a dandalin sada zumunta, kada ka ji kamar ka yi laifi idan ka ƙi zama abokinsa. Tun da yake akwai haɗarurruka tattare da dandalin sada zumunta, wasu sun yanke shawara cewa ba za su shiga dandalin ba. Amma mene ne ya kamata ka riƙa tunawa idan ka yanke shawarar shiga dandalin sada zumunta?

KU KALLI BIDIYON NAN KA ZAMA MAI HIKIMA A DANDALIN ZUMUNTA NA INTANET, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Hoto daga bidiyon “Ka Zama Mai Hikima a Dandalin Zumunta Na Intanet.” Wata yarinya tana mamakin ganin hotunanta a telibijin.

    Mene ne ya kamata ka yi la’akari da shi kafin ka rubuta saƙo ko saka hotuna a dandalin sada zumunta?

  • Hoto daga bidiyon “Ka Zama Mai Hikima a Dandalin Zumunta Na Intanet.” Ma’auni da ke dauke da hoton yarinya a gefe daya da tarin tsabar kudi a gefe daya. Hoton yarinyar ya fi tarin tsabar kudin nauyi.

    Me ya sa ya kamata ka zaɓi abokai da kyau a dandalin sada zumunta?

  • Hoto daga bidiyon “Ka Zama Mai Hikima a Dandalin Zumunta Na Intanet.” Maza biyu da ba su yi ado da kyau ba suna nuna wa wani yaro abin da aka saka a dandalin sada zumunta, yaron kuma ya rufe idonsa.

    Me ya sa ya kamata ka tsai da yawan lokacin da za ka riƙa yi a dandalin sada zumunta?—Afi 5:15, 16

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba